Category: WikiHausa

Yadda ake amfani da WikiHausa

  • Nazarin Rayuwar Adabin Kasuwar Kano

    Nazarin Rayuwar Adabin Kasuwar Kano

    Balaga: 1990 zuwa 1995

    Nazarin rayuwar Adabin Kasuwar Kano a zamanin da muka kira na balaga ya fito mana da siffofi mabambanta. Da farko dai lokaci ne da littattafan da suka samu wanzuwa daga shekarar 1984 suka samu karɓuwa tsakanin makaranta da masu buga littatafan da kuma masu sayar da su.

    A daidai wannan zamani ne na shekarar 1990 zuwa 1995 za a ce Adabin Kasuwar Kano ya shiga tashen balaga, marubutan da suka yi suna da karɓuwa a tsawon shekaru, suka bayyana. Cikin irin waɗannan marubuta akwai Ɗan Azumi Baba Cheɗiyar ‘Yan Gurasa, wanda ya wallafa littatafai guda 9 a cikin wannan tsakani da kuma Aminu Abdu Na’inna da ya fitar da littatafai guda 6.

    Akwai kuma irin su Ado Ahmad Gidan Dabino da Bala Anas Babinlata da Badamasi S. Burji da suka wallafa littattafai 4 kowanensu, haka kuma akwai marubuta irin su Balaraba Ramat da Yusuf Lawan Gwazaye da Alkhamees Bature da suka fitar da littattafai bibiyu kowane. Saura kuwa, irin su Ibrahim Mandawari da Ibrahim Sheme da Bashir Sanda, kowane ya fitar da littafi guda.

    A ɓangaren mata kuwa, a wannan lokaci ne aka sami fitowar manyan marubuta mata da suka yi tashe a cikin wannan harka da daɗewa, marubuta irin su Bilkisu A. Funtua da Hadiza S. Aliyu da Hawwa Aminu da Atika S. Sidi da suka antayo daga shekarar 1994.

    Abin la’akari dangane da wannan zamani na balaga shi ne, yawancin littattafan da aka samar daga cikin sama da 110 da aka wallafa a wannan tsakani sun fito ne daga taskar ƙungiyar Raina Kama da muka yi bayani a baya, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Ado Gidan Dabino.

    A daidai wannan lokaci za a fahimci cewa wanda ya fi tashe a cikin wannan ƙungiya shi ne Ɗan Azumi Baba, wanda ya fito da wani salo na labaran aljannu da dodanni da muridai, sai ko Ado Gidan Dabino da ya ɗauki fagen soyayy wanda kuma ya fi kowane daga cikin marubutan shahara saboda alaƙarsa da ‘yan jarida da suka yayata shi da kuma irin rawar da ya taka wajen tallata kansa da kuma ƙwazonsa wajen gina labari.

    Daga jadawalin marubutan da muka samu kai hannu kansu, mun fahimci nan ma maza suka fi shahara a fagen rubutun domin kuwa mata 12 ne suka tusgo, alhali maza 60 suka wallafa littattafai a wannan zango na Adabin Kasuwar Kanon (Dubi rataye na 8.0)

    Tsufa Da Hayayyafa: 1996 zuwa 2001

    Daga lokacin da kasuwar littatafan Adabin Kasuwar Kano ta yi tashin gwauron zabbi daga shekarar 1995  zuwa 1996 amon wannan sabon tsarin rubutu ba inda bai kai ba, wannan ne ya sa harkar ta koma irin ta wani babban kamfani. Ƙungiyoyin marubuta da suka ɓullo daga shekarar  1990  kamar su Kungiyar Matasa Marubuta da Kukan Kurciya da Raina Kama  da Jigon Hausa duk a cikin birnin Kano da Ruwan Dare a  Kaduna da kuma Kungiyar Matasa Marubuta ta Jihar Sakkwato a Sokoto (Adamu, 2006) su ma suka ƙara wa wannan harka martaba da ɗaukaka a idon mutane.

    Haka kuma ƙungiyoyin makaranta irin su Dakata Readers Association da Kabuga Readers Association da Tudun Wada Readers Association da Hotoro-South Readers Association duk a cikin Kano sun agaza wajen tabbatuwar wannan harka.

    Daga cikin kuma masu sayar da littattafan da suka agaza sosai a daidai wannan lokaci akwai irin su Alhaji Baba  na Jakara City Bookshop da Alhaji Musa Ɗanbala na Sauƙi Bookshop kuma Alhaji Garba Mohammed na Garba Mohammed Bookshop da ke Sabon Gari Kano.

    Wannan aure na marubuta da makaranta da masu sayar da littattafai da kuma ƙungiyoyi daban-daban, shi ne za a iya cewa ƙashin bayan wannan fasali na Adabin Kasuwar Kano, wanda ya sanya harkar ta hayayyafa, ta kuma bunƙasa fiye da yadda ake tsammani.

    Wannan ne ya sa aka sami yawancin tarin littattafan adabin Kasuwar Kanon masu yawan gaske da suka kai sama da 400, a tsakanin 1996 zuwa 2001. Daga wannan zango ne mata suka fara kunno kai sosai da sosai domin kuwa an sami marubuta mata sama da 50.

    ’Ya’ya Da Jikoki: 2002 zuwa 2008

    Littattafan da aka yi wa laƙabi da ‘ya’ya da jikoki su ne ƙagaggun labaran da aka samu daga shekarar 2002 zuwa shekarar 2008. Nazarin da aka yi wa waɗannan littatafai an fahimci cewa duk da sauye-sauyen da aka samu na litattafan Adabin Kasuwar Kano a wannan zango, ba a bar fasalin da aka saba ba, wato na yin rubutun bisa tsarin ni na rubuta, ni na gyara, ni na kai inda za a buga mini, ni kuma ke sayarwa da kaina.

    An dai samu wasu sababbin marubuta ne da irin nasu fasali, sun ɓullo domin taka rawa irin tasu. Sai dai kamar yadda muka fahimta, wannan ba ya rasa nasaba da ganin cewa tsofaffin marubutan da suka yi tashe a baya, wasu sun watsar da rubutun, ko dai saboda sun yi aure ko kuma yayinsu ya wuce, wasu kuma sun koma wata sana’ar, musamman shirya finafinai, ga shi kuma buƙatar litattafan ba ta kau baki ɗaya ba, wannan ya jaza fitowar sababbin marubuta domin nuna irin tasu fasahar. An dai ga cewa an samar da littattafai na wannan zangon kimanin 248.

    A wannan zangon kamar yadda muka nazarta, marubuta mata sun sami filin baje kolinsu. Daga cikin littattafan da muka samu kai hannu kansu marubuta mata sama da 76 ne suka yi tashe. Wannan shi ne karon da mata suka yi ambaliya sosai. Haka kuma daga hirar da na yi da makaranta littattafai a wannan zango sun nuna sha’awarsu kan rubuce-rubucen matan, ƙila wannan shi ya ƙara sa yawan marubuta matan.

    A cikin waɗannan jerin littattafan na wannan zango, wadda ta fi yawan littattafai ita ce marubuciya Sa’adatu Saminu Kankiya tana da 14 da suka yi fice sosai, wannan kuma alama ce da ke nuna littattafanta sun fi samun karɓuwa ga makaranta. Mai yiwuwa saboda suna ɗauke da labaran da suka shafi soyayya da aure waɗanda bisa ga nazarin da aka gudanar su ne suka fi tashe a wannan zango.

    Akwai kuma wasu marubutan mata da suka fi shahara a wannan zango da suka haɗa da Saliha Abubakar Zariya da Hadiza Salisu Sharif da Amina Abdullahi Sharaɗa da Zainab Birged da su Sa’adiya Kankiya da Rahmatu Hassan Sanda.

    Duk da cewa yawancin waɗannan sababbin marubuta ne, duk da haka akwai fitattu da suka yi tashe, wasu tun daga haihuwa da ƙuruciya, ba su kuma daina ba har zuwan ‘ya’yan da jikoki. Cikin irin wannan fasali akwai irin su Rahma A. Majid da kuma su Hafsat A. Sodangi da Zuwaira Isa da Bilkisu Ahmed Funtua, da dai sauransu da dama.

    Daga cikin maza kuwa, littattafan Nazir Adam Salihi su ne suka fi karɓuwa da tashe kuma ya rubuta littattafai guda 13. Shi kuma yanayin gabatar da jigon littattafansa ya sha bamban da na sauran marubutan wannan zamani, domin wani lokaci za ka ga labaran nasa na soyayya ne, amma cikin ban takaici, wata sa’a ma da ban tsoro. Sai dai irin yadda yake wasa da harshe a cikin littattafan nasa ya sa yawancin masu karatu ke biye da shi a kullum.

    Maje El-Hejeej Hotoro shi ma wani marubucin ne da litattafansa da kuma tauraruwarsa, musamman a wannan zango suka yi tashe. Shi ma ɗin yakan yi amfani da jigon soyayya ko kuma jigon ban tsoron da jan hankali.

    A daidai kuma cikin wannan zango ne aka soma ganin ɓullar sabon tsarin rubutun Adabin Kasuwar Kanon. Da farko dai an sami marubutan da suka canza akalar rubutun nasu domin ya dace da zamani musamman ganin cewa an sha suka da taƙaddama kan yawaitar rubuce-rubuce kan soyayya da aure. Ire-iren waɗannan marubuta sun haɗa da Bala Anas Babinlata da Ibrahim Sheme da Sakina A. Aminu da Rahma A. Majid da Saliha Abubakar Abdullahi da sauransu da dama.

    Daga nazarin da aka yi, an fahimci cewa yawancin waɗannan marubuta ko dai ilminsu na zamani ne da suka yi nisa a ciki ya sa littattafan nasu suka yi armashi; wato kamar Ibrahim Sheme da Rahma Majid da suka nazarci adabin duniya daban-daban, da yake sun yi digiri, Ibrahim Sheme har digiri na biyu ya yi, ko kuma sun dai tsara littattafan ne domin su ɗan sha bamban da waɗanda aka saba ji da gani a wannan zango bisa sani, domin sun ga yadda aka daɗe ana ta kai-kawo game da neman sauyi, wato kamar su Babinlata da Rahma da Saliha da Abdullahi da Mukhtar Yaron Malam.

    Duka dai alamu ne da ke nuni da cewa sabon yanka rake na Adabin Kasuwar Kano ya shigo kasuwa. Baya ga wannan kuma ga gasar ƙaga littattafai da ta kunno kai, musamman ta Bashir ƙaraye da aka fara a shekarar 2007, wadda ta ba da dama aka sake ɗaga martabar rubutun da kuma marubutan wannan zango. A nan ana maganar irin su Ibrahim Sheme da Lawan Barista da Maje El-Hajeej da suka cinye gasar rubutun a cikin wannan zango. 

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Karanta Adabin Kasuwa A Ƙasar Hausa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Karin Lafazi (ACCENT)

    Karin Lafazi (ACCENT)

    Gabatarwa
    Baiwar da Allah ya yi wa ɗan Adam ta amfani da harshe yana daga cikin abubuwan da suka bambanta shi (ɗan Adam ɗin) da sauran halittu, har ya fifita shi bisa kansu. Ko da yake dabbobi ma suna da tunani irin nasu, wanda kuma suke bayyanawa cikin hanyar sadarwa iri daban-daban, amma babu wata dabba da take da hanyar sadarwa irin wadda ɗan Adam yake amfani da ita, wato harshe.

    Sannan kuma, kowace al’umma tana da harshenta da ya keɓanta da ita domin sadarwa, wannan dalili ya sanya da zarar an samu hulɗa tsakanin al’umma ɗaya masu rayuwa a yankuna mabambanta to a kan samu karin lafazi. Har ila yau kuma, ana samun karin lafazi a lokacin da aka yi hulɗa tsakanin al’umma mabambanta, kamar yadda bayani zai gabata a cikin wannan aiki.

    Ma’anar Harshe
    Masana da dama sun sha tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar Harshe. Daga cikinsu akwai:

    Fagge, (2002) ya ce: “harshe wata hanyar sadarwa ce da ɗan Adam yake amfani da sauti mai ma’ana wanda kuma yake bin wasu dokoki. Ya ce ta hakan ne kowacce al’umma da ke zaune a doron ƙasa take sadarwa kuma ta fahimci abubuwan da ke ƙunshe a zukatan jama’a kamar tunani da ra’ayi da hikima da sha’awa da dai sauransu”.

    Yakasai, (2012:47) kuwa ya ce: “harshe shi ne hanyar furta ma’anoni da tunane-tunanen da suke ran ɗan Adam, wato dai ita ce hanyar sadarwa tsakanin mutane. Ita wannan hanya kuma ba ganinta ake yi ba, jin ta ake yi kawai, wato hanyar sadarwa ta ɗan Adam (harshe) saututtuka ne masu ma’ana da ake furta su, kunnen mai sauraro ya ji, kana basirarsa ta kama, ta fahimta domin amfaninsa”.

    A taƙaice harshe, yana nufin wani furuci mai ma’ana da mutane ke yi ta hanyar magana domin su isar da saƙon da zukatansu suka ƙudurta ga irin mutanen da ke iya fahimtar wannan nau’i na sarrafa harshe ba tare da ishara da hannu ba.

    Ma’anar Ilimin Harshe (Linguistics)

    Ilimin kimiyyar harshe wani fage ne na ilimi da ake nazartar harsuna a kimiyyance. Dangane da ma’anarta, ga ta bakin masana:

    Lyons (1981:1) ya ce: “Linguistics is the scientific study of language”
    Fassara: “Ilimin harshe tsararriyar hanya ce ta kimiya da ake bi domin nazarin harshe”.
    Yusuf (2007:1) yana cewa: “Linguistics is the study of language”.
    Fassara: “Ilimin harshe fage ne da ake nazarin harshe”

    Masana sun karkasa ilimin harshe zuwa manyan rassa guda biyu:
    1. Manyan rassan ilimin harsuna (macro linguitics)
    2. Ƙananan rassan ilimin harsuna (micro linguistics).

    Kowanne daga cikinsu yana da rassa kamar haka:
    1. Manyan rassa (macro) su ne:
    Phonetics-Ilimin tsarin furuci
    Phonology-Ilimin tsarin sauti
    Morphology- ilimin ginin kalma
    Syntax- ƙirar jimla
    Semantics- Ilimin Ma’ana.

    2. Ƙananan rassa (micro) su ne kamar haka:

    • Socio linguistics
    • Historical linguistics
    • Geographical linguistics
    • Comparative linguistics
    • Psycho linguistics
    • Descriptive linguistics
    • Computational linguistics
    • Applied linguistics
    • Quantitative Linguistics. Da sauransu.

    To mu a nan aikinmu ya shafi ilimin walwalar harshe ne wato (sociolinguistics), don haka za mu fara da bayyana ma’anar ilimin walwalar harshe daga bakin masana.

    Ma’anar Ilimin Walwalar Harshe (Sociolinguistics)

    Dangane da ma’anar wannan fage ga ta bakin masana:
    Trudgill (1974:32-33) ya bayyana cewa: “Sociolinguistics is a part of linguistics concerned with language as a social and cultural phenomenon. Sociolinguistics is concerned with investigating the relationship between language and society with the structure of a language and of how such a linguistic code functions in communication”.

    Fassara: Ilimin walwalar harshe wani ɓangare ne na ilimin harshe da ya danganci cuɗanya da yadda al’adun al’umma ke gudana. Ilimin walwalar harshe ya ƙunshi binciko dangantakar da ke tsakanin harshe da al’umma ta la’akari da irin tsare-tsaren harshen da kuma yadda wannan canji kan yi tasiri a wurin sadarwa.

    Shi kuwa Yakasai (2012:24) cewa ya yi : “Ilimin walwalar harshe, wanda da Ingilishi ake kira “SOCIOLINGUISTICS” wani ɓangare ne daga fannin nazarin harshe da kuma yadda ake sarrafa shi. A haƙiƙanin gaskiya, wannan fanni na walwalar harshe yana da faɗi ƙwarai da gaske, musamman ma da yake ya tatttare irin rawar da harshe yake takawa cikin dangataka da muhimman al’umuran rayuwa; da al’ada da al’umma da jinsi da rukunin jama’a da harshen ƙasa da nazarin karin harshe da jin harsuna biyu ko da yawa da kuma muhallin magana”.

    Ma’anar Karin Lafazi (Accent)

    Muhammad (1990) ya fassara “Language Accent” da “Karin Lafazi”.
    Dangane da ma’anar karin lafazi kuwa masana da dama sun tofa albarkacin bakin su. Daga cikinsu akwai: Crystal (2008:3) ya ce “karin lafazi ya ƙunshi wasu matakai na furuci waɗanda suke taimakawa wajen karin harshe, mutum ya yi magana kuma aka fahimci yankın da ya fito wato Bazazzage, ko Bakano, ko Basakkwace, ko Badaure ne, to wannan shi ne karin lafazi. Haka kuma, karin lafazi kan taimaka wajen bayyana rukunin al’ummar da mutum ya fito”.

    Misali,
    Duk mai nazarin harshen Hausa in yana magana da wani mutum sai ya ji ya furta:

    • Ɗamra
    • Amre
    • Ɗwaci
    • Hwaɗa

    Nan take zai fahimci cewa wannan mutumin daga yankin Yammaci ƙasar Hausa ya fito, wannan ganewar da ya yi shi ne karin lafazi. Haka ma tasirin ilimi addinin da na boko kan haifar da samun karin lafazi. Misali:

    Idan mutum ya yi zurfi a ilimin boko ko na addini, yana magana za a ji yana amfani da tsarin furucin wasu sautuka na Ingilishi ko na Larabci wajen furta sautukan Hausa. Wannan tsarin furucin sautin wani harshe da ake ji a kan tsarin furucin wani sautin na wani harshen daban shi ne ma ya zama karin lafazi.

    Ire-Iren Karin Lafazi

    Karin lafazi ya kasu zuwa kashi biyu, kamar haka:

    • Karin lafazi ‘yan asali (Native Accent)
    • Karin lafazin baƙi (Non-Native Accent)

    1. Karin lafazin ‘yan asali (Native Accent): Nau’in karin lafazi ne wanda ake samu a tsakanin al’umma masu amfani da harshe ɗaya a matsayin harshen uwa waɗanda suke zaune yankuna ko wurare mabambanta. Misali: Ana samun wannan nau’i na karin lafazi a harshen Hausa. A ƙasar Hausa akwai karuruwan harshe da dama. Misali:

    • Bakatsine
    • Bazazzagi
    • Basakkwace
    • Hiɗi
    • Uni
    • Hwaɗa
    • Halshe
    • Ƙarke
    • Amre

    A nan da zarar yanayin yadda mutum ya faɗa waɗannan kalmomi za a fahimci daga yankin da ya fito. Wannan yanayi da ya sa ake gane cewa mai magana ɗan yankin, Bakatsine da Bazazzagi da Basakkwace. Shi ma ya zama karin harshen lafazi.

    Bayan haka a cikin al’ummar Hausawa akan samu rukunin al’umma kamar sarakuna da malamai da “yan boko da ‘yan daudu da mawaƙa da sauransu. Duk ya yin da ɗaya daga cikin wannan rukunin ya yi magana har ta kai daga furucinsa aka gano rukunin al’ummar da yake to an samu karin lafazi.

    2. Karin lafazin baƙi (Non-Native Accent): Wannan shi wani yanayi ne da ake samu, idan mutum yana magana da wani harshe sai ya riƙa amfani da karin harshen uwa (L1) maimakon karin harshen da yake magana da shi. Misali akasarin harsunan da suke Kudancin Kaduna ba su da sautukan /ɓ/ da /d/ da /ƙ/ da sauransu. Misali:

    • Barawo maimakon Varawo
    • Kato maimakon Ƙato
    • Daki maimakon Ɗaki
    • Izo maimakon ya zo
    • Baro maimakon Biro
    • Haro maimakon yaro

    Wannan zai sanya da sun yi magana za a fahimci cewa ga daga inda suka fito. To wannan abin da suka yi har aka gane ga inda mutum ya fito, su ba ainihin masu magana da wannan harshe ba ne to shi ne karin lafazi na baƙi.

    Dalilan Da Suke Haifar Da Karin Lafazi

    Daga cikin dalilan da suke haifar da Karin lafazi akwai;
    1. Tsarmi (Language Interference)
    2. Karin harshe (Dialect) da sauransu.

    Hanyoyin Wanzuwar Karin Lafazi

    • Karin lafazi na wanzuwa ne ta hanyoyi uku:
    • Karin lafazin tsarın sauti (phonological Accent)
    • Karin lafazin ginin kalmomi (morphological Accent)
    • Karin lafazin ginın jimla (syntactic Accent).

    Karin lafazi na tsarin sauti: shi ne wanda ake samun mai magana da wani harshe a matsayin harshe na biyu ya rinƙa amfani da wasu sautuka na harshe na ɗaya a lokacin magana ba tare da ya sani ba, wanda mai saurare zai fahimci cewa shi ba ainihin mai harshen ba ne. Misali:

    • Yuƙa
    • Tabshi
    • Barawo
    • Halshe

    Waɗannan su ne misalan karin lafazi na sauti saboda duk ana fahimtar su ne ta tsarin sautukan da aka sauya saɓanin na daidaitaccen furucin harshe.

    Karin lafazi na kalmomi: Shi kuwa wannan ana samun shi ne a yayin ginin kalma da ake samu ga masu magana da harshe. Misali;

    • Cin maimakon ci
    • Birori maimakon birai
    • Barewoyi maimakon berayi

    Karin lafazi na jimloli: Shi ne wanda ake samu mai wannan karin harshen, ko harshe na ɗaya ya riƙa amfani da tsarin harshensa wajen gina jimlolin da yake magana da su. Misali;
    Kai da ni maimakon ni da kai.
    Yat tashi maimakon yan tashi
    Nac ce maimakon na ce

    To duk ya yin da ɗaya daga cikin wannan ya faru kuma har aka gane cewa shi wannan mai magana yana amfani da harshe ne a matsayin harshe na biyu, shi ga inda ya fito to shi ne karin lafazi.

    A takaice karin lafazi nau’i ne na harshe wanda ke nuna, ko jaddada asalin mutum, da kuma inda ya fito ta yanayi furuncin sa ta hanyar sautinka. Misali, idan aka duba British English da American English sun bambanta ta yanayin karin sautin/lafazinsu, sannan ta haka ne za ka fahimci inda mutum ya fito. To wannan abin da ya sa in mutum ya yi magana a fahimci cewa shi ba dan asalin harshen ba ne ko kuma ga yankin da ya fito, wannan abin shi ne karin lafazi.

    Kammalawa

    Daga bayanan da suka gabata za a fahimci cewa, ilimin walwalar harshe ɗaya ne daga cikin manyan rassan ilimin kimiyyar harshe, kuma fage ne da ya ƙunshi abubuwa da dama ciki har da karin lafazi. A cikin wannan aiki an yi ƙoƙarin bayyana ma’ana, ire-ire, yadda karin lafazi ke wanzuwa da dalilan da suke haifar da shi tare da kawo misalai daban-daban game da abin da ake kira da karin lafazi da karin a fagen ilimin walwalar harshe.

    Manazarta

    Fagge U.U (2002). “Zaurance Zawarawa a Birnin Kano da Kewaye”. In Algaita Journal of Current Research in Hausa. Vol. 2 No. 1.
    Lyons, L. (1981). Language and Linguistics: An Introduction. Cambridge: Cambridge University Press.
    Muhammad, D (1990), Hausa Metalanguage, (edt). Ibadan Univesity Press Ltd.
    Trudgill, P. (1974). The Social Differentiation of English in Norwich. Cambridge: University Press.
    Yakasai M.G (2012). Jagorar Ilimin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Services LTD.
    Yusuf, O. (ed) (2007). Basic Linguistics for Nigerian Languages Teachers. Port Harcout:Lingistics Association Of Nigeria&M J Grand Orbit.

    Na Muhammad Abubakar

    Mai Maɗi Ke Talla (Mai Zuma Gida Ake Tad Da Shi) danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Adabin Kasuwa A Ƙasar Hausa

    Adabin Kasuwa A Ƙasar Hausa

    A wannan babin an yi ƙoƙarin bin yadda aka samar da adabin kasuwa a ƙasar Hausa. Abin nufi, bayan ganin yadda fasalin adabin kasuwa ya kasance a sassan duniya daban-daban, da kuma ganin irin yadda ya samu ga maƙwabtanmu, Inyamurai, sai kuma mu gangaro domin ganin yadda ya samu a ƙasar Hausa.

    Don haka, a wannan babin an dubi irin zangunan da Adabin Kasuwar Kano ya shiga a ƙasar Hausa, da kuma irin rawar da ya taka wajen ginuwar wani ɓangare na ƙagaggun labaran Hausa.

    Samuwar Adabin Kasuwar Kano

    Daga abubuwan da aka gani a babin da ya gabata ke nan ba abin mamaki ba ne idan aka ci karo da Adabin Kasuwa a Amurka ko Turai ko Rasha ko cikin ƙasashen Asiya ko Larabawa, kai ko ma ina ne a cikin duniya.

    Hakan na faruwa ne ganin cewa ai ba ƙasashen Turawa ko waɗanda suka ci gaba ne ke da damar su samar da adabin kasuwa su kaɗai ba, haka kuma ba dole sai harshen Ingilishi ko wani harshen da ya sami ci gaba kaɗai ne zai iya samar da shi ba; kowace ƙasa, kuma kowane irin harshe zai iya samun adabin kasuwa a cikin wani zangon rayuwar adabin. Domin inganta bincike, ya dace mu bi salsala, mu ga yadda aka samar da abin da yawanci ake kira Adabin Kasuwar Kano tsakanin Hausawa.

    Rayuwar Farko : 1984-1989

    Abin da aka daɗe ana kira Adabin Kasuwar Kano ya samo asali ne a farkon shekarun 1980, kuma wannan shekaru a ƙasar Hausa ko Arewacin Nijeriya baki ɗaya, shekaru ne masu tarihi a ɓangaren samuwar ilmin boko da rubutu.

    A daidai wannan zangon rayuwa ne ɗaliban UPE, shirin gwamnatin tarayya da aka soma daga 1976 domin ba kowane yaro damar samun ilimin furamare kyauta, suka fara shiga kasuwar rubutu da karatu da rububin abubuwan karantawa, domin ɗaliban farko na wannan shiri sun baro firamare a shekarar 1982, daga wannan lokaci har zuwa 1984, an yaye ɗalibai har kashi huɗu. Saboda haka an samar da sababbin makaranta da suke buƙatar abin karantawa.

    Haka wannan zango ya zo daidai da lokacin da babban kamfanin wallafa da ɗab’i a ƙasar Hausa wato NNPC ya soma shiga tasku, ya soma sukurkucewa da neman durƙushewa. A daidai wannan lokaci kamfanin NNPC ya daina buga littattafan hira da nishaɗi, bayan kuma ga dubban matasa da aka yaye daga shirin na UPE sun antayo cike da  shauƙin irin waɗannan littattafai da babu su.

    Wannan shiri na UPE, duk da cewa bai zaunu da gindinsa ba, amma ya samar da sababbin makaranta a farkon shekarun 1980. Kuma a daidai wannan lokaci sai ga shi tattalin arziƙin Nijeriya ya ƙara inganta, saboda gano man fetur da aka yi, ya ƙara wa ƙasar hanyar samun kuɗaɗen shiga masu yawa.

    Bincike kuma ya nuna cewa duk lokacin da irin wannan harka ta kasance haka, wato ga masu ilmi gwargwado, sa’annan ga ‘yan kuɗi a hannun jama’a, kamar yadda muka gani a fasalin Adabin Kasuwar Kitsch na Jamus, sai ka ga hanyoyin samar da adabi, mai kyau ko maras kyau, suna wadatuwa.

    Da yake tun can azal akwai kayayyakin rubutu da ɗab’i gwargwado a ƙasar Hausa, sai ya ba matasa damar da suka tsunduma cikin wannan harka ta wallafa littattafai ba ji ba gani, kamar yadda Furniss (2001) ya yi nuni. Sai dai ko kafin shekarar 1984 da littafin Rabin Raina na Talatu Wada Ahmed ya fito kasuwa akwai ɓirɓishin rubuce-rubuce na soyayya a ƙasar Hausa.

    Idan ba a manta ba a shekarar 1978 kamfanin NNPC ya shirya gasa da ta samar da littattafai a shekarar 1980, kamar su Mallakin Zuciyata na Sulaiman Ibrahim Katsina da So Aljannar Duniya na Hafsat Abdulwaheed da kuma Amadi na Malam Amah na Magaji Ɗambatta, (Haruna, 2009).

    Sai dai abin lura shi ne waɗannan littatafai daga gasa suka fito, wato sai da aka yi shiri da tsari, haka kuma na hukuma ko kamfani ne, don haka sun biyo tsari da ingancin da ya bambanta su da adabin kasuwa. Ke nan za a iya cewa waɗannan littatafai na gasar 1978 sun dai nuna hanya ne na irin adabin da zai iya biyo bayansu, ba su ne farkon adabin na kasuwa a ƙasar Hausa ba.

    A ɗaya ɓangaren kuma an danganta littafin Rabin Raina na Talatu Wada Ahmed da tushe ko tubalin samuwar adabin kasuwa a ƙasar Hausa saboda yanayin da ya samu da kuma yadda ya shiga kasuwa. Shi ma ba wai zama aka yi domin assasa wannan fage na adabin kasuwa ba tattare da shi ba.

    Kamar yadda a karo na farko wadda aka danganta aikinta da Adabin Kasuwar Kano, Talatu ta bayyana wa Mujallar Garkuwa (2000) yadda ta samar da littafin, ta ce ita ba ta san da wani abu wai shi adabin kasuwa ba lokacin da take rubuta littafinta. Ta ƙara da cewa ta dai rubuta shi ne a lokacin tana makarantar WTC Katsina, tana aji uku, wato wajajen shekarar 1980.

    Ta kuma rubuta shi ne daga gyauron labaran da take ba ‘yan uwanta ɗalibai lokacin suna makaranta can da dare kafin su yi barci. Bayan ta gama sakandire ne ta fitar da shi ta hanyar aika shi gidan rediyon tarayya Kaduna domin a karanta a shirin Shafa Labari Shuni, amma aka daɗe ba a karanta shi ba, daga baya ta miƙa wa wani kamfanin bakin hanya da ake kira Ogwu a Kaduna domin ya buga mata shi.

    Kamfanin Ogwu ya buga, ya kuma shiga sayar da littafin da ya ga mutane sun dami suna son su karanta. A lokacin da Kamfanin Ogwu ya shiga sayar da littafin, ita Talatu tana Kwalejin Ilmi ta Kafanchan wajen ƙaro ilmi, a can ne wata ƙawarta ta zo da littafin, tana yi mata bayanin yadda littafin ya yi kasuwa, ita ba ta ma sani ba. Wannan daɗin abin da ya faru ya sa ta koma gida ta ji abin da ya auku.

    Mahaifiyar Talatu ta ba ta kuɗin da aka samu, ta yi murna ƙwarai da ganin arzikin da wannan littafi ya jawo mata. Daga wannan lokaci ne ta shiga sake buga littafin, ana watsawa a cikin ƙasar Hausa, ta yadda abin ya dinga ba ta mamaki na ganin cewa mutane, musamman masu sayar da littatafai daga ko ina a faɗin ƙasar Hausa ke kira ko yo saƙon don Allah ta aika masu da kwafe 500 ko dubu ko dubu biyu ko ma fiye.

    Fitar wannan littafi da yanayin da ya samu kan sa lokacin bugu da sayarwa da kuma hanyoyin da aka bi aka samar da shi ya nuna wa sauran marubuta cewa ashe akwai wata hanyar rubutu da wallafa littattafai ba dole sai ta bin kamfanonin bugu da wallafa na gwamnati ba.

    Saboda haka daga samuwar wannan littafi na Rabin Raina a shekarar 1984 za mu iya cewa akalar adabin hira ko ƙagaggen labari ta soma sauyawa, kuma a iya cewa daga wannan lokacin ne Adabin Kasuwar Kano ya fara ginuwa. Sai dai abin da ke da muhimmanci a nan shi ne ba wai zama aka yi ba domin a tsara da gina wannan fasali na Adabin Kasuwar ta Kano ba, abu ne da ya kasance caccakuɗe, kuma tattare da abubuwa mabambanta da suka haɗa da :

    • Tun da farko dai akwai matsalar abubuwan karantawa a makarantu da kuma tsakanin sababbin makaranta kamar yadda muka yi bayani.
    • Ga halin da kamfanin NNPC ya shiga daga farkon shekarun 1980 da rashin buga littatafan hira.
    • Ga kuma ɗaruruwan ‘yan makaranta da waɗanda suka kammala makarantun, sun kuma rubuta littattafai masu yawa, ba wurin buga su, balle a san da su.
    • Shirin gidan Rediyon Tarayya Kaduna na Shafa Labari Shuni da wasu da dama a gidajen rediyon jihar Kano da Katsina da Sokoto da wasu wurare da dama ya taimaka wajen fito da waɗansu daga cikin marubutan da ke ɓoye.
    • Bugun littafin Talatu na bakin kasuwa da yadda ya sami karɓuwa ya sanya wasu, ƙila suka ce su ma bari su gwada bugawa da sayarwa.

    Saboda haka littattafan da ake ta yayatawa a halin yanzu a matsayin waɗanda suka biyo bayan littafin Talatu daga 1984, ba wai shawara suka yi da juna ba, kuma ba su san wani na yin irin wannan aiki ba, kamar yadda bincike ya nuna a halin yanzu. Ke nan jawabin da Malumfashi, (1994) ko wanda Adamu, (1996) da Adamu (2000) suka yi na lissafa littatafan da suka biyo na Talatu kamar haka ba daidai ba ne, sai dai daga littafin Talatu na Rabin Raina sai:

    • Ibrahim Hamza Abdullahi da Soyayya Gamon Jini a 1986.
    • Idris S. Imam da In Da Rai a 1987.
    • Balaraba Ramat da Budurwar Zuciya a 1987.
    • A.M Zaharadden da Kogin Soyayya a 1988.
    • Idan so cuta ne, na Yusuf M. Adamu a 1989.

    An yi wannan hasashe bisa hujjar da ta nuna cewa babu wani bincike da ya tabbatar da jeruwa da daidaituwar wannan tsari ko kuma wani bayani da ya ce an tattauna tsakanin waɗannan mutane na biyo sahun Talatu Wada.

    Bari mu yi nazarin batun da kyau, tun da farko dai garuruwan marubutan daban-daban suke, Talatu na Kaduna, Ibrahim Hamza na Kano, Idris S. Imam kuwa tun 1984 aka buga littafin nasa ba wai a 1987, Balaraba kuwa ko kafin ta shigar da littafinta na Budurwar Zuciya a layin adabin kasuwa ta fuskar shiga ƙungiyar Raina Kama, an riga an buga littafin a Zaria,(Gaskiya Corporation a 1984).

    Haka shi ma Zaharradeen a Kano yake, shi kuwa Yusuf Adamu yana ɗalibta a Sakkwato ne ya shigo da nasa littafin. Haka kuma daga binciken da aka gudanar an fahimci cewa ko kafin Ibrahim Hamza Abdullahi da littafinsa na Soyayya Gamon Jini a 1986, an samar da Hannunka Mai Sanda I na Ƙamarradeeen Imam a 1985, me ya sa ba a shigar da shi cikin layin na farko ba? Haka kuma a tsakanin 1984 da aka samar da littafin Talatu, ba wai littattafai huɗu ne kurum suka yi tashe ba, guda 13 ne.

    Ke nan ba wata ƙungiya ba ce ko kuma wani taro aka yi ba aka ce a samar da wannan abu da aka kira Adabin Kasuwar Kano daga baya. Shi kuma Malumfashi (1994) da ya kira shi da wannan suna, ya yi haka ne daga abin da ya gani masu kama da juna tsakanin littattafan da irin waɗanda aka samar a Onisha kamar yadda ya bayyana daga baya, (Malumfashi, 2004).

    Kamar yadda muka gani can baya, rayuwar adabi takan shiga cikin wani sauyi ne na wani lokaci, daga baya kuma ta kasance cikin wani tsari na daban, irin wannan shi ne ya faru da abin da aka kira Adabin Kasuwar Kano yanzu. Sai dai wani abu da za a yi la’akari da shi, shi ne, yawancin matasan da suka yi tashe a wancan lokaci a wannan fage ba su yi amfani da kamfanonin ɗab`i da ake da su don bayyanar da ayyukansu na adabi ga jama’a ba, ba don komi ba kuwa sai don ba wani kamfani da ya damu ya buga ire-iren waɗannan littattafai.

    Ba kuma wai don ba su da kasuwa ko kuma ba su sami karɓuwa ba a tsakanin al`umma ba, a a, a tsakanin shekarun 1978-1982 ba abin da ya fi tashe da karɓuwa irin labaran da wasu suke rubutawa, suna aika wa gidajen rediyoyi daban-daban ana karantawa. Ba wani abu ya jawo hakan ba sai ganin litattafan da aka samar daga gasar da aka shirya a 1978 da suka samar da litattafan soyayya na farko da za a iya kira `yan zamani, sun yi tasiri ga rayuwar irin waɗannan matasa.

    Sai dai da alama amfani da aka yi da kafar rediyo, wadda ta sanya ƙagaggun labarai irin waɗannan suka sami martaba, ba wai kawai tsakanin waɗanda suka yi boko ba kurum, har ga waɗanda aikinsu shi ne sauraron rediyo, ba su iya karatun ba.

    Bisa wannan tafarkin aka shiga samar da sababbin marubuta, wasu ta hanyar kwaikwayon abin da aka rubuta, suka aika gidajen rediyoyin, wasu kuma ta sake wa tatsunniyoyi da labaran Hausa fasali, wasu ko ta kwaikwayo ko ɗaukar fasalin wasu labaran Ingilishi ko fassara kai-tsaye ko kuma naɗe fina-finan Indiya da na Turawa zuwa takarda.

    Cikin ɗan lokaci ƙanƙani sai ga kabod-kabod na gidajen rediyoyin nan sun cika maƙil, wasu ma suka shiga ƙonawa, wanda ya sa masu rubutun suka shiga guna-guni idan ba a karanta nasu labaran ba. Sai dai kuma waɗanda Allah ya tarfa wa garinsu nono daga cikin waɗanda aka karanta nasu a gidajen rediyoyin, sai ga shi sun fara samun suna da ɗaukaka.

    Wannan ya jawo wasiƙu suka shiga gilmawa zuwa gare su, ana yaba masu, ta haka kuma aka ga cewa ga wata kafa ta samu ta kashe waccan ƙishirwa ta rashin labaran Hausa da ta addabi matasa, ta yadda a tsakanin shekarar 1984 zuwa 1998 marubuta da sababbin littatafai suka baje kasuwarsu a ƙasar Hausa.

    Idan aka yi nazari sosai za a ga ko da Talatu ta bayyana a 1984 a Kaduna, ba a Kadunar ta tsaya ba, domin littattafan sun baje duk faɗin ƙasar Hausa, musamman a Kano da suka dasa rayuwarsu. A Kanon akwai irin littafin Talatu Wada da ya riga ya shiga kasuwa shi ma kafin ma bayyanar na Talatu, wato Wasiyar Baba Kere na Ibrahim Sale Gumel, a kuma wannan shekara ta 1984, an sami ɗan uwan na Talatu, wato In Da Rai Da Rabo na Idris S. Imam.

    Saboda haka ko da Ƙamarradeen ya shigo da nasa littafin a 1985, ba dole ba ne ya san da abin da Talatu ta yi ko kuma sauran da suka riga nata shiga kasuwa; musamman ganin cewa ɗa ne ga marigayi Abubakar Imam, kuma yana aiki da kamfanin Huda-Huda da ke Zaria, waɗanda su ne mawallafansa.

    Yadda Kano ta shigo cikin harkar da litatattafan da ‘yan Kanon suka samar bai rasa nasaba da suna da tashe da littafin Talatu da na Idris da Ibrahim suka yi a kasuwar Kanon. Littattafai goma sha uku ne suka wanzu a wannan lokaci a tsakanin 1986 zuwa 1989. Ga alama kuma su ne suka sanya Kano ta sami karɓuwa da tagomashi a wannan harka ta yadda daga baya Gusau ta shigo sahu, Kanon ta sake bayyana daga can kuma sai Sakkwato tare da Yusuf Adamu.

    Ga jerin waɗannan littattafai da suka kasance na farko ko suka kasance jijiyar da ta gina wannan sabon yanayin rubutu na Adabin Kasuwar Kano. Daga marubuta waɗannan littattafai an fahimci marubuta mata guda biyu suka wanzu, sauran kuma duk maza ne.

    LAMBA LITTAFI MAWALLAFI SHEKARA
    1 Wasiyyar Baba Kere Ibrahim Saleh Gumel 1983
    2 In Da Rai da Rabo Idris S. Imam 1984
    3 Rabin Raina Talatu Wada Ahmed 1984
    4 Hannunka Mai Sanda 1 Ƙamaruddeen Imam 1985
    5 Soyayya Gamon jini Ibrahim Hamza Bici 1986
    6 Daji Bakwai Abba Ado Ɗandago 1987
    7 In Da Rai… Idris S. Imam 1987
    8 Kogin Soyayya Ahmed Mahmoud Zaharaddeen 1988
    9 Turmi Sha Daka Kabiru Ibrahim Yakasai 1988
    10 Budurwar Zuciya Balaraba Ramat Yakubu 1989
    11 Soyayya Danƙon Zumunci Bashir Sanda Gusau 1989
    12 Tsalle Ɗaya… Idris S. Imam 1989
    13 Idan So Cuta Ne Yusuf M. Adamu 1989

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Danna nan don karanta Jigogin Adabin Kasuwannin Ƙasashe

    Edita@rumasau-kallamu

  • Jigogin Adabin Kasuwannin Ƙasashe

    Jigogin Adabin Kasuwannin Ƙasashe

    Saƙonni ko kuma jigogin da waɗannan ayyuka na adabi suke isar wa sun bambanta ne daga wannan gari zuwa wancan ko kuma daga wannan ƙasa zuwa waccan, amma dai abu muhimmi shi ne kowane da abin da yake son ya isar ga al’ummar.

    Alal misali daga nazarin da aka yi wa Adabin Elizabeth da ya wanzu a zamanin sarauniya Elizabeth ta Ingila a tsakanin ƙarni na 16 da na 17, ya shahara ne ta fuskar wasan kwaikwayo da kuma waƙoƙi, sannan kuma kusan yawancin marubutan suna yin rubutunsu ne domin kare martabar masu mulki da kuma tajirai.

    Wannan ne ma ya sanya tun daga farkon mulkinta, Sarauniya Elizabeth ta kasance tamkar uwar ƙungiyar, kuma mai ba da taimako ga marubutan, ta yadda kamar yadda muka nuna a wasu lokuta har aiwatar da wasan kwaikwayon ake yi a gabanta.

    A adabin Larabawa ma musamman kuwa waƙoƙin lokacin jahiliyya, jigonsu  bai wuce faɗakarwa ta zamantakewa ba, ko kuma rayuwa irin ta yau da kullum ba, sai kuma jigon waƙoƙin yawace-yawace da kuma waƙoƙi na ƙabilanci da kusan kowace ƙabila ke da shi. Amma bayan bayyanar Musulunci da wayewar kai sai abin ya canza, domin kuwa  litattafan adabin Larabci a lokacin sun fi bayyana rayuwar iyali, misali ayyukan Naguib Mahfuz na Cairo Trilogy,

    Shi kuwa adabin Onitsha na Nijeriya jigoginsu sai suka sha bamban da na sauran sassan duniya, domin kuwa a lokacin da aka fara samar da shi a 1947, sai ya kasance ya ta’allaƙa ne wajen ba da labaran soyayya da suka shafi aure da kuma kasuwanci, a sassan wannan yanki na Nijeriya.

    Ke nan a iya cewa yawancin labaran na Adabin Onisha ba su maganar komai sai labaran soyayya da tatsuniyoyi. Daga baya kuma sun tattauna abubuwa da suka shafi yadda ake rubuta wasiƙa da yadda ake koyon Ingilishi da kuma tallata haja da makamantansu.

    Daga binciken da aka gudanar an dai fahimci cewa yawancin jigogi na yawancin Adubban Kasuwa a kowace ƙasa, suna kasancewa abin da al’ummar wannan wuri ne suka fi so da ko sha’awar gani ko karantawa a daidai lokacin da ake aiwatar shi, ko dai na soyayyar ne ko kuma na kasuwanci, ko rayuwar iyalin ko kuma na masu mulkin, kusan a ce wannan shi ya fi rinjayar masu karanta ko sauraron wannan adabi na wannan yanki.

    Marubuta

    Marubuta waɗannan litattafan dai kamar yadda muka nazarci wasu daga cikinsu, shahararru ne a fagen da suke, wasu kuma fitattun malamai ne a makarantun zamanin. Misali, marubuta adabin Elizabeth, wasunsu sun yi fice matuƙa, marubuta kamar  Roger Ascham, wanda yake fitacce kuma shahararren malami ne, domin har sarauniyar Ingilar ma sai da ya koyar da ita a makaranta, an haife shi a shekarar 1515.

    Sannan ga masana irin su Edmund Spenser da William Shakespeare da Christopher Marlowe da Ben Johnson da Edmund Spencer da John Fletcher da Thomas Kyd da Thomas Middleton da Thomas Nashe da John Webster da John Donne da Philip Sidney, dukkansu fitattun marubuta ne waɗanda suka yi tashe a wannan zamani na Elizabeth da kuma bayan wannan zamani.

    Idan muka dubi marubutan Adabin Kitsch na Jamus, shi ma ya samu fitattun masu zane da rubutu a lokacin, fitattun daga cikinsu kuwa su ne; Gabriel Thuller da Matk A. Cheetham da kuma George Wilhelm Friedrich Hegel.

    A adabin kasuwa na Larabawa da muka gani, shi ma ya zo da nasa fitattun marubutan da suka shahara kuma suka samar da litattafai a lokacin, fitattu daga cikinsu akwai Muhammad Husayn Haykal da Muhammad Tahir Haqqi da Naguib Mahfuz da kuma Al-Hamadhani da fitaccen aikinsa na Maqamatil-Hariri da dai sauransu.

    Haka ma a kasuwar Onisha wanda za a fara cewa ya fara samar da waɗannan litattafan na kasuwar Onitsha ba wai kawai ya yi fice ba ne, mutum ne wanda ya shahara ta fuskar ilimin boko daga baya, wato Cyprian Ekwensi wanda daga baya ya tashi daga wallafa ƙananan litattafai zuwa manya.

    Makaranta

    Makaranta Ayyukan adabin kasuwa su ma sun bambanta, wasu talakawa ne kaɗai ke sauraro ko kallo, yayin da wasu  kuwa kamar na Elizabeth ya kasance masu sarautar Ingila ɗin suna daga cikin masu yi da sauraron wannan adabi. Sai da ta kai ma wasu ayyukan idan aka yi su, sai a ware wanda za a kai wa sarauniyar, da kuma wanda za a gabatar a bainar jama’a.

    Saboda haka sai ya kasance daga cikin masu sha’awar wannan aikin; wato ko dai wasan kwaikwkon ko kuma waƙoƙi sun fito daga masarautar Ingilar. Wannan ne ma ya sa marubuta da dama na wannan lokacin sun ji daɗin yadda ‘yan majalisar Sarauniya ke tarairayar su.

    Shi kuwa adabin Kitsch ba wai na talakawa ba ne kaɗai, na sababbin matsakaitan tajirai ne da suke da kuɗin sayen irin waɗannan ayyuka, amma ƙarfinsu bai kai na sayen adabin masu gari ba, sun yi haka ne domin a tunaninsu sayen wannan aikin adabin zai sa su tafi kafaɗa-kafaɗa da sarakuna da tajiran Jamus, masu sayen ayyukan adabi na ƙwarai.

    Shi dai adabin kitsch an samar da shi ne domin matsakaitan masu kuɗi ko masu mulkin da ba su kai su yi gogayya da waɗanda suka yi fice ba, duk da haka su ma waɗanda suka yi ficen, ganin ƙarƙo ko kuma yanayin wannan na Kitsch ɗin ya sanya suka fara sayen shi.

    Shi kuwa Adabin Kasuwa na Onitsha ya fi shahara ne a wurin matasa `yan makaranta maza da mata, da kuma  masu ƙaramin ƙarfi don su samu abin karantawa wanda baya da tsada, ta yadda kowa za iya sa kuɗi ya saya ba tare da wani tarnaƙi ba.

    Tsarin Littattafai

    Ko a tsarin waɗannan litattafan, mafi yawancinsu ba su da shafuka da yawa, ana yin su ne ta yadda kowa zai iya karance ce su ba tare da ɗaukar wani dogon lokaci ba. Sannan kamar yadda muka ce kuma harshen da ake rubuta su shi ma mai sauƙi ne, wanda bai yi karatu ba da wanda ya fara bai tasa ba da kuma wanda ya yi karatu mai zurfi da sauransu duk za su iya karantasu, domin ba a  nannaga harshe ko nuna ƙwarewar harshen da zai zama matsala wajen karantawa.

    Saye da Sayarwa

    Duk aikin Adabin da ya kasance ana samun shi a wasu wurare da ba na saida litattafan ko aikin adabi ba ne to wannan adabi zai kasance na kasuwa ne ko yayi ko kuma mai tashe ne. Duk adabin da ake bi kasuwa-kasuwa, da shaguna, da wajen `yan tireda, da masu tura kaya a baro, ko wurin `yan kura, kai ko kawai a hanya, ana nemansa don a saya, adabin kasuwa ne, (Malumfashi, 2002).

    Wannan ya zama gaskiya idan aka yi la’akari da irin wuraren da ake sayar da littattafan zamanin Sarauniyar Ingila Elizabeth Ta ɗaya, yawancin littattafan ana sayar da samunsu a bakin shagunan da marubutan suka buɗe don tallata hajarsu, ko dai a cikin birnin London ko kuma ƙauyukan da ke maƙwabtaka da shi. An fi ganin su a bakin titi, ‘yan ƙalilan ne suka samu shiga shagunan sayar da littatafai na zamani.

    Wasu kuma kamar yadda muka bankaɗo, ana saye da rarraba su ne ta hannu, tsakanin wannan marubuci ko marubuciya zuwa wancan marubuci ko marubuciya. Sai dai za a iya cewa wasu kuma ba ma sayar da su ake yi ba ana aiwatar ko gabatar da su ne a gaban jama’a a lokuttan bukukuwa ko tarurrukan marubuta.

    Kusan irin wannan fasali ne aka gani a adabin Kistch na Jamus, yawancin zane-zanen da ayyukan adabin da suka yi tashe a wannan karon an samar da su ne a kasuwar birnin Munich, inda yawancin masu adabin suka rayu. Saboda haka za a iya cewa adabin da zane-zanen duk ‘yan kasuwa ne, don haka a bisa titi ake samu da sayar da su a tsakanin al’ummar wancan zamani.

    Idan kuma aka lura da tsarin saye da sayarwar littatafan Adabin Kasuwar Onitsha za a fahimci shi ma ya bi irin wannan fasali na baya. Tun da farko dai an yanke wa adabin cibi ne a kasuwar Onitsha, nan yawancin marubutan suka wanzu, sai kuwa wasu sassa na garuruwan Aba da maƙwabta.

    Saboda haka yawancin littattafan ana saye da sayar da su ne a waɗannan kasuwanni. Ba kuma wani wuri na musamman aka tanadar musu ba, inda ‘yan kasuwar ke saye da sayarwar nan ne littattafan suka samu matsuguni.

    Naɗewa

    A wannan babin an kalli samuwar Adabin kasuwa da kuma bambancin da ke tsakanin Adabi da Adabin kasuwa ɗin ko na yayi ko kuma na talakawa. Bayan ganin irin wannan adabi a sassan duniya kamar na sarauniya Elizabeth a Ingila da na Kitsch a Jamus da na Adbul-Mu’athir a ƙasashen Larabawa sannan sai nan gida a garin Inyamurai wato Onitsha, an kuma kalli matakan gane wannan adabi  da sauransu.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Danna nan don karanta Adabin Kasuwa Na Onitsha A Nijeriya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Adabin Kasuwa Na Onitsha A Nijeriya

    Adabin Kasuwa Na Onitsha A Nijeriya

    Kamar yadda wannan fasali na adabin kasuwa ya samu karɓuwa da watsuwa a sassan Turai da Amurka da ƙasashen Larabawa, haka ma inda Turawan suka yi mulkin mallaka fasalin ya samu zaunuwa, ko dai a cikin harshen ‘yan gida ko kuma cikin harshen baƙin da suka zo cikin Afirkawa.

    Misalin da za a iya kawowa a nan shi ne na Adabin Kasuwar Onitsha da ya wanzu cikin harshen Ingilishi, masana da dama sun bayyana yadda wannan fasali ya samu ya kuma wanzu. Haka kuma kamar yadda Okoro (2002) ya bayyana, adabin Kasuwar Onisha an yi shi ne a wani zamani a farkon ƙarni na 20 a ƙasar Inyamurai a Nijeriya da ya kasance, wanda a lokacin an sami al’ummar Igbo da ba su da isasshen ilmin boko.

    Wasu sun kammala Elementare, suka sami aikin malanta ko suka zama masinjoji ko sakatarori a ofisoshin gwamnati a Onitsha, sai dai da yawa daga cikinsu sun fahimci cewa ba za su iya rayuwa da irin wannan aiki ba, domin ba albashin ƙwarai, wasu kuma da ba su sami aikin ba, bayan sun kammala karatu, sai abubuwa suka cunkushe musu, domin waɗanda suka yi karatun ma ya suka ƙare, su kuma masu aikin suna aiki, ga shi ƙaro karatun na da matsala a wannan lokaci.

    Wannan ya sa wasu da dama suka fantsama cikin kasuwar Onisha ko dai a matsayin ‘yan tireda ko masu koyon sana’ar hannu ta kafinta ko teloli ko magina ko maƙera. Da yake yawancinsu, sun yi boko to ba su son su zauna haka nan ba abin karatu, ga shi kuma ayyukan adabin Ingilishi da ke makarantu ya fi ƙarfin aljihunsu, sai suka shiga rubuta abin da ya zo ga ransu domin su karanta tsakaninsu; ire-iren waɗannan rubuce-rubuce ne aka kira da Adabin Kasuwar Onitsha.

    Ke nan, kamar yadda Obiechina (1973) da Okoro (2002) da Malumfashi (2005) suka yi bayani daga nasu binciken ba wani abu ba ne Adabin Kasuwar Onitsha sai ƙananan littatafan nan da aka samu da yawan gaske a kasuwar ta Onitsha da wasu sassa na Kudancin Nijeriya a tsakiyar shekarun ƙarni na 20, suka ce, an tsara da shirya da kuma sayar da su domin talakawan Onisha da ba su yi zurfin karatu ba.

    Wannan adabin na Kasuwar Onitsha, wanda shi ne za a iya kira da wanda ya fara samar da wurin buga litattafai, garin Onitsha dai yana kudancin Nijeriya, mutanen wurin waɗanda Igbo ne sun shahara wurin kasuwanci, a wani lokaci ma ana iya cewa kasuwar ta Onitsha ita ce mafi shahara a Afirka.

    An fara samar da littafin adabi a wannan wuri cikin shekarar 1947, babu wani tsari ko fasali da aka bi domin samar da waɗannan litattafan, hasali ma dai an fara samar da su ne domin cike wani giɓi da aka samu na karatu da ko rubutu, saboda a lokacin samuwar addinin kirista da `yan mulkin mallaka sun taimaka wurin samar da makaranta a garin Onitsha domin su yi aiki, ko kasuwanci ko kuma su samu wata damar ta ci gaba.

    Wannan shi ya haifar da masu buga litattafai na bakin hanya ko na kasuwa da suka fara samar da wannan adabi. Wanda za a fara cewa ya fara samar da waɗannan litattafan na kasuwar Onitsha ba wai kawai ya yi fice ba ne, a lokacin, mutum ne kuma wanda daga baya ya shahara ta fuskar ilimin boko, wanda kuma yana ma daga cikin waɗanda suka wakilci jama`arsu, kuma ƙwararre wurin haɗa magunguna (Pharmacist), wato Cyprian Ekwensi, wanda ya tashi daga wallafa littattafan adabin kasuwa ko yayi zuwa wallafa gangariyar adabi.

    Littafin da aka fara samarwa a lokacin shi ne; Ikolo Wrestler na Cyprian Ekwensi, an samar da shi ne daga tatsuniyoyin Igbo, wanda aka buga a wurin sai da litattafai na Tabansi  Bookshop da kuma ɗayan, When Love Whispers na soyayya. An sake samar da wasu bayan shekara biyu wato; Tragic Niger Tales, mawallafin litattafan wani malamin makaranta ne, yana ba da labarin aure ne ko ma’aurata.

    Su dai irin waɗannan litattafai da aka samar sun yi tashe da suna a duk faɗin garin Onitsha da kewaye, musamman a wurin matasa ‘yan makaranta, maza da mata. Wannan ya sanya wasu marubutan suka biyo baya, don ganin irin amsuwar da waɗannan litattafai suka yi.

    Wannan kuma shi ya sanya aka shiga samar da sababbin masu buga litattafan na bakin hanya, da kuma na cikin kasuwa, shi ya sanya har zuwa shekarar 1960 abin ya haɓaka, wanda ya sanya masu buga litattafan suka watsu har zuwa garuruwan Aba da Fatakwal da Inugu da sauran manyan garuruwan gabashin Nijeriya.

    Akwai dalilai da dama da suka sanya aka samu wannan bunƙasuwar a garin Onitsha kamar yadda Obiechina (1973) ya bayyana. Wasu daga cikin dalilan kuwa har da kasancewar kasuwar garin Onitsha ta yi fice ba a gabashin Nijeriya ko Najeriyar ba, kai har faɗin Yammacin Afirka.

    Saboda haka idan aka lura za a ga cewa Adabin Kasuwar Onitsha ya kasance da siffofi da alamu da dama, waɗanda suka yi kama da waɗanda aka gani a ƙasar Ingila, ko a Jamus ko na ƙasar Larabawa, domin dai an yi shi ne saboda masu ƙaramin ƙarfi su samu abin karantawa, ke nan ba ya da tsada, sannan yana da saurin fahimta, ma`ana harshen da aka yi amfani da shi mai sauƙin fahimta ne, kuma an yi shi ne musamman saboda talakawa ko waɗanda ba su tare da gangariyar adabi.

    Haka kuma ba su maganar komai sai labaran soyayya da tatsunniyoyi da rayuwar aure da kuma bunƙasuwar kasuwanci. Sai dai wannan bai zama abin mamaki ba, domin suna yin la’akari ne da buƙatun masu karatun su.

    Matakan Gane Adabin Kasuwa

    Abin lura a nan shi ne, irin wannan fasali da Adabin Kasuwar Onitsha ya ɗauka shi ne Adabin Elizabeth a Ingila ko kuma na Kitsch a Jamus, da na Larabawa ya ɗauka. Ke nan babban matsugunin kowane aikin adabi da aka yi wa laƙabi da na kasuwa ko na yayi bai wuce irin fasalin da ya tashi da shi ba, ko dai mai arha ne ko kayan da aka yi amfani da su wajen samar da shi ba su da inganci ko kuma masu yin sa da karanta shi wasu gungun jama’a ne, ba na kowa da kowa ba ne.

    Gungun mutanen na iya kasancewa masu kuɗi ko talakawa ko iyayen gari, sannan uwa uba kuma wannan adabi na da lokacin da yake rayuwa, ya kuma mutu (Malumfashi,2005:8).

    Domin gane wannan fasali na adabin kasuwa bari mu dubi adabin Elizabeth na Ingila da kyau, ya dai yi tashensa ne cikin shekara 45, wato daga 1558 zuwa 1603, shi kuma na Kitsch da ke a Jamus, ya rayu ne daga 1860 zuwa 1870, wato shekara 10 ya yi a duniya ko kuma na Onisha daga 1947 zuwa 1975, ya shekara 28 ke nan a raye.

    Saboda haka, fasalin adabin kasuwa yana zuwa da siffofi da kamannu masu yawa. Sai dai domin taƙaitawa muna iya cewa shi ne adabin da ake samu a cikin kasuwa, ba wai ana nufin kasuwar dole ta kasance irin wadda muke tunani ba, duk inda jama’a suke hada-hadar saye da sayarwa, shi ake nufi da kasuwa a nan.

    Idan ana son a gane shi da kyau sai a dube shi da waɗannan fasalce-fasalcen :

    • Adabin kasuwa zai iya kasancewa mai sauƙin karantawa, wato mai jimloli marasa sarƙaƙiya.
    • Haka kuma nahawunsa zai kasance sassauƙa, ba mai nauyi ba.
    • Haka yawancin wannan adabin yakan kasance bai da yawan shafuka, ma`ana, bai ɗaukar lokaci za a iya karance shi.
    • Ga shi kuma yana da arha, kusan kowa zai iya sanya kuɗi ya saya ba tare da wani tarnaƙi ba (Obiechina, 1973:12).

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Danna nan dan karanta Adabin Kasuwar Kitsch A Jamus 

    Edita@rumasau-kallamu

  • Adabin Kasuwar Kitsch A Jamus

    Adabin Kasuwar Kitsch A Jamus

    Duk da an ce samuwa da ginuwa na adabin jama’a ko yayi ya tusgo ne daga ƙasar Ingila, amma ba a ƙasar Ingila irin wannan rayuwar adabin kasuwa ko yayi ya samu gindin zama ba kawai, a can Jamus a cikin ƙarni na 18 da na 19, an sami irin wannan adabi da ake wa laƙabi da Kitsch.

    A cikin harshen Jamusanci ko Yiddish, kalmar Kitsch na nufin duk wani aikin adabi ko zane da bai da tagomashi ga masu mulki ko tajirai ko ya kasance lami ko kwashe-kwashen ayyukan wasu da aka yi a baya, (Wikipidia.org).

    Adabin Kitsch ya soma watayawa sosai da sosai a ƙasar Jamus a ƙarni na 19, musamman a kasuwannin birnin Munich a tsakanin 1860 zuwa 1870, inda ake kiran duk wani aikin adabi da ke da arha ko na yayi ko mai karɓuwa a tsakanin al’ummar da aka yi domin su ko yake ja a cikin kasuwar sayar da ayyukan adabi da sunan na Kitsch.

    Shi wannan adabin na Kitsch ba wai na talakawa ba ne kaɗai, na sababbin matsakaitan tajirai ne da suke da kuɗin sayen irin waɗannan ayyuka, amma ƙarfinsu bai kai na sayen adabin masu gari ba, sun yi haka ne domin a tunaninsu sayen wannan aikin adabin zai sa su tafi kafaɗa-kafaɗa da sarakuna da tajiran Jamus, masu sayen ayyukan adabi na ƙwarai.

    Duk da cewa Kitsch ya samu karɓuwa a tsakanin jama’a, duk da haka bai wuce adabin kasuwa ko yayi ba ga sauran jama’a, musamman masu sarauta da tajirai, domin kuwa ba a yi aikin da kyau ba ko kuma takardun da aka zayyana hoton ko buga aikin adabin sun kasance na banza, ba su da aminci.

    Ke nan adabin Kitsch bai wuce adabin Jamus da bai da mazaunin ƙwarai ba a tsakanin masu mulki da tajirai ko kuma yana magana kan abubuwan da ba su ne aka sa gaba ba a tsakanin al’ummar, ko kuma dai gwanjon adabi ne ko adabi ne da ke kwaikwayon wani adabi, ba tunani ko ƙirƙirar wanda ya samar da shi ba ne ko da kuwa ya samu karɓuwa tsakanin wasu gungun mutane, (Cuddon, 1999).

    Saboda haka kamar yadda muka gani a baya, Kitsch wani nau`in adabi ne da ya wanzu a ƙasar Jamus wanda yake nufin duk wani aiki na zane ko aikin adabi wanda masu mulki ko masu kuɗi ba su yi na`am da shi ba. An samar da wannan adabi ne mai suna Kitsch domin a mai da martani ko ya yi jayayya da ayyukan adabi da aka samar a ƙarni na 18 da na 19 wanda yake ana masa kallo na masu mulkin ƙasaita da fitattun masu kuɗi ne.

    Shi dai wannan salon adabin yana da matuƙar alaƙa da adabin da ke tashe ko kuma na yayi, ba wani abu ya sa aka kira shi da haka ba kuwa sai ganin cewa aikin da aka yi na zanen ko aikin adabin ba a yi shi yadda za a iya cewa ya ginu ko tsaru ba.

    Ke nan adabin Kitsch an samar da shi ne domin matsakaitan masu kuɗi ko masu mulkin da ba su kai su yi gogayya da waɗanda suka yi fice ba, duk da haka su ma waɗanda suka yi ficen, ganin ƙarko ko kuma yanayin da wannan adabi ya fita da yadda mutane ke rububinsa ya sanya suka fara saye da karanta shi.

    Za mu iya cewa adabin Kitsch ya kasance na talaka ne kawai domin ganin fasalin yadda aka samar da shi ba mai aminci ba ne, ma’ana kayan da aka yi aiki da su wurin samar da waɗannan zane ko ayyukan adabin ba su da inganci, kuma an samar da su ne ganin cewa waɗanda suke sayen shi ba su iya sayen manyan ayyukan adabi, wato wannan yana da sauƙin kuɗi ga masu sayen shi, kusan kowa zai iya sa kuɗi ya saye shi.

    Wannan ya sa ake danganta adabin Kitsch (Wikipedia.org) da duk wani aikin adabi ko zane da aka samar maras kyau, wanda zai iya biya wa mai saye da buƙatarsa, ma’ana zai kashe masa ƙishirwa daga abin da yake so ya gani ko ya karanta, musamman cikin wata sabuwar kama ko siffa, a ayyukan adabin wanda aka kwaikwaya daga wanda ya gabace shi ko suke rayuwa tare.

    Wannan ne ya sa irin wannan tsari ko fasali ya sha suka daga masana, fitattun daga cikin su kuwa su ne; Gabriel Thuller wanda ya goyi bayan wannan adabi na Kitsch bai dace da zamanin ba, domin ba gwanaye ke yin sa ba. Haka kuma wani fitaccen masani a fannin zane Georg Wilhelm Friedrich Hegel ya jaddada cewa zane-zanen wannan zamani yana da alaƙa da wani yanayi na lokacin da aka samar da shi, ba abin damuwa ba ne, in dai ya samu karɓuwa daga masu karatu.

    Adabin Kasuwa Na Larabawa

    Shi ma adabin Larabci kamar sauran ya sha kwaramniya har zuwa lokacin da aka samar da na zamani wanda yake da alaƙa da na Yammacin Dauri (Neo-Classical) wanda ya nemi ya canza fasalin adabin Larabci gaba ɗaya, wato wanda za a ce ya samo kayan aikinsa daga wanda ya gabata, kamar su Maqamatul Hariri da Alfu Laylah.

    Saboda haka su waɗannan na zamanin sai ya kasance sun koma ko dai suna samo kayan gininsu daga waɗannan ko kuma suna juyar aikin marubuta adabin Yammacin Dauri ne kai tsaye, suna mai da su na Larabci.

    Marubuta da dama a ƙasashen Siriya da Lebanon da Egypt sun samar da ayyukansu na adabi daga Maqama, fitattun daga cikinsu akwai Al-Muwayhili da littafinsa na The Hadith of Issa ibn Hisham a zamanin mulkin Ismail a Egypt, wanda wannan littafin shi ne za a iya cewa ya haifar da wani sabon zango a adabin Larabci.

    Wannan yanayi shi ya ba marubucin nan ɗan ƙasar Lebanon,Goergy Zeidan, wanda kirista ne da ya yi hijira zuwa ƙasar Misira, bayan zanga-zangar da aka yi a Damaskus a 1860 damar fitar da basirarsa a fili sosai.

    An dai fara buga labarin Ziedan a farkon ƙarni na 18 a cikin jaridar ƙasar Misira, wato Al-Hilal. Ba wani abu ya sa aka kira ayyukan waɗannan mutane na yayi ko na kasuwa ba sai ganin cewa su ne ayyukan da mutane suka fi sha`awa, saboda irin yadda aka samar da su da harshen da kalmomin da aka yi amfani da su da kuma yadda aka tsara su, sai kuma ficen da marubutan suka yi. Sauran waɗanda suka kasance a cikin wannan tsarin sun haɗa da Khalil Gibran da Mikha`il Na`ima.

    Amma dai masana da dama na adabin Larabci sun bayyana cewa an fi ganin Littafin Zaynab na Muhammad Husayn Haykal da Adraa Denshawi na Muhammad Tahir Haqqi da kasancewa ayyukan adabi na farko a wannan ƙarni masu kama da ayyukan adabin jama’a ko kasuwa, fiye da waɗancan da muka ambata a baya. (dubi ƙarin bayani a Arabic Literature daga Wikipidia: The free encyclopedia).

    Daga nazarin da aka gudanar an fahimci litattafan adabin yayi ko na jama’a na Larabci sun fi bayyana rayuwar iyali, misali ayyukan Naguib Mahfuz na Cairo Trilogy inda ya siffanta rayuwar iyali.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Don karanta Adabin Kasuwar Sarauniya Elizabeth A Ingila danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Adabin Kasuwar Sarauniya Elizabeth A Ingila

    Adabin Kasuwar Sarauniya Elizabeth A Ingila

    Da yake mun ga yadda wannan adabi ya kasance da kuma tasirin da ya yi tsakanin al’umma a Ingila, zai dace a nan mu faɗaɗa kan wannan batu domin mu ga yadda fasalin adabin kasuwar ya kansance ta hanyar bayar da misalai.

    Da yake tun da farko mun yi nuni da cewa harkar ta adabin kasuwa ta samo tushe ne daga Ingila, ya dace mu fahimci yadda al’amarin ya kasance, kafin mu shiga wasu sassan na duniya mu ga su kuma irin nasu fasalin.

    Daga nazarin da aka yi an fahimci akwai bambance-bambancen da aka samu a tsawon zamanin aikin adabin Ingilishi, tunanin farko dai ya fara ne daga `yan Sukotlan ba daga Ingila ba, shi wannan adabin ne ya ci gaba da watayawa a tsakanin ƙarni na goma sha biyar zuwa farko, da tsakiyar ƙarni na goma sha shida.

    Wannan ne ya samar da  gagarumin aikin Tottel a shekarar 1557. Shi dai wannan littafin ya shahara ne saboda dalilai da dama; Na farko dai abin da ya fi jan hankalin sababbin makaranta a wannan lokacin shi ne mafi yawan abin da littafin ya ƙunsa abu ne wanda ba a san da shi ba da, haka kuma akwai hasashe ba yaƙini ba a cikin labarin, wanda kuma wannan shi ya fi burge masu karatun ayyukan adabin wannan lokacin, ba kamar ayyukan wasu da suka wallafa ba waɗanda ko dai sun mutu ko kuma sun daɗe ƙwarai da yin rubutun, (Saintsbury,1920).

    Wannan zamani na Sarauniya Elizabeth kamar yadda muka yi bayani akwai aikin manyan masana a ƙasar Ingila, kamar fitaccen marubucin nan na wasan kwaikwayo, Christopher Marlowe da marubuta waƙoƙi irin su Edmund Spenser da kuma shahararrun masana kimiyya irin Francis Bacon.

    Marubuta da dama na wannan lokacin sun ji daɗin yadda ‘yan majalisar Sarauniya ke amsar su in sun kai ziyara, duk da cewa suna daga cikin talakawa (Saintsbury, 1920). Wannan kuwa ya faru ne domin tun farkon mulkin Sarauniya Elizabeth, ita ta kasance tamkar Uwar ƙungiyar, kuma mai ba da taimako ga marubuta labaran wasan kwaikwayo, kai har aiwatar da wasan kwaikwayon ake yi a gabanta.

    A shekarun 1560 aka fitar da wasan Kwaikwayo na Blank Verse Tragedies wanda za a iya cewa shi ne ya buɗe ƙofa wurin samuwar kimiyyar wasan kwaikwayon da ake nazari har zuwa yau. A shekarar 1568 ne aka aiwatar da wasan kwaikwayon a gaban sarauniya a bisa dandamali.

    Irin yadda aka samar da litattafai da ayyukan adabin Elizabeth ya taimaka ƙwarai wurin ceton adabin Ingilishi daga shiga cikin haɗari na kwasar ayyukan da ‘yan kasuwa suke yi, waɗanda kuma ake samarwa da tsada. Misali, a lokacin da Tottel ya fiddo littafin shi na Miscellany ba dukkan mawallafa na lokacin suka san da wannan hanyar ta fiddo da littafin kai tsaye ba, wato ba tare da an miƙa shi ga masu wallafar zamani ba (Saintsbury,1920).

    Ta ɓangaren rubutun zube ma, lokacin mulkin sarauniya Elizabeth ya samu tagomashi sosai, saboda a lokacin ne aka samu ayyukan adabi waɗanda suka yi tashe ko kuma suka zama na yayi, domin a lokacin malaman da ke koyarwa a Jami`ar Kambirij (Cambridge) sun taimaka ƙwarai da gaske wurin samar da ayyukan masana irin su Ascham da Wilson, da sauransu ta fuskar zube.

    Duk da cewar akwai ayyukan magabata irin su Thomas Hoby, amma dai za a iya cewa Roger Ascham shi ne ya fara buɗe fagen da littafinsa Toxophilus da ya rubuta aka kuma wallafa shi a shekarar 1545, amma dai littafinsa da ya fi tashe, wato Schoolmaster bai fito ba sai bayan da ya mutu, (Saintsbury,1920). Shi dai Ascham fitacce, kuma shahararren malami ne domin har sarauniyar Ingilar ma sai da ya koyar da ita a makaranta.

    Kamar yadda muka gani a sama, Adabin Elizabeth na Ingila ya ratsa zangunan mabambanta. Misali, mun dai ga akwai ayyukan adabi da aka yi kafin lokacin Elizabeth ɗin kamar na su Thomas More wanda ya yi rubuce-rubuce, musamman na waƙoƙi da kuma Wyatt da sauransu.

    Ko a lokacin mulkin Sarauniya Elizabeth ɗin ma, ayyukan adabi da suka fi tashe su ne waƙoƙi da wasan kwaikwayo da kuma ƙagaggun labaran, amma dai masu sarrafa waƙoƙin da wasan kwaikwayo sun fi yawa da tashe, wato kamar masana irin su Edmund Spenser da sauransu (Saintsbury,1920).

    A ɓangaren wasan kwaikwayo da ƙagaggun labarai kuwa dole ne masana irin su Shakespeare su shige gaba, sannan ga Marlowe wanda zaƙaƙuri ne, wanda ayyukansa suka yi tashe, ga kuma Ben Jonson wanda ya kwaikwayi ayyukan magabatansa, ya samar da nasa. Ta ɓangaren ƙagaggun labarai kuwa akwai marubuta irin su Philip Sidney da Richard Hakluyt da Francis Bacon da sauransu da dama.

    Daga wannan taƙaitaccen bayani mun fahimci a ƙasar Ingila ne aka samar da wannan fasali na adabin jama’a ko na kasuwa, mun dai fahimci  irin wannan adabi na yayi ko kasuwa ya wanzu tsakanin ƙarni na 16 da na 17 lokacin da adabin sarauniya Elizabeth ya yi tashe tsakanin shekarar 1558 zuwa 1603.

    Shi dai adabin Elizabeth ba yana nufin ita Sarauniyar ce ta wallafa ko buga shi ba (kodayake ita ma ta jefo waƙoƙinta da aka karanta, musamman On Monsiuer’s Departure), sai dai ana iya cewa a lokacin mulkinta ne aka samar da yawancin ayyukan adabin da ake wa laƙabi da na yayi ko kasuwa, duk kuwa da cewa ayyuka ne na ƙwarai.

    Abin da ya sa wannan gangariyar adabi ya kasance adabin kasuwa shi ne ya samu karɓuwa a hannun yawancin jama’ar Ingila a cikin ƙanƙanen lokaci (Wikipidia.org). Duk da cewa akwai ƙagaggun labarai cikinsa, abin da ya fi yin tashe shi ne wasan kwaikwayo da waƙoƙi. Adabin Elizabeth ya somo ne daga zamanin su Tottel da suka wanzu da waƙoƙinsu zuwa masu tsara labarai na zamanin Caroline, (Saintsbury,1920).

    Ba wani abu ya sanya wannan zamani ya kasance na ayyukan adabin al’umma ba sai ganin manyan mashahuran marubutan da suka yi tashe a wancan zamani sun wanzu ne a lokacin, kuma har yau suna tashe a fagen nazari da sharhi. Akwai marubuta ayyukan adabi da suka haɗa da William Shakespeare da Christopher Marlowe da Ben Johnson da Edmund Spencer da John Fletcher da Thomas Kyd da Thomas Middleton da Thomas Nashe da John Webster da John Donne da Philip Sidney da sauransu, duk a wannan zamani suka wanzu.

    An kira waɗannan mutane da ayyukan adabinsu a matsayin na yayi a wancan lokaci, saboda sun kasance mutane ne ko kuma ayyukansu da jama’a ke rububi. Sa’annan kuma yawancin ayyukan nasu kwafe-kwafe ne ko dai daga wasu can da aka yi a baya da suka shahara ko kuma tsakanin marubutan wannan zamani.

    Misali, Thomas Kyd da aikinsa na The Spanish Tragedy, shi ya ba Shakespeare hasken rubuta Hamlet, ba kuma nan kaɗai Shakespeare ya tsaya ba, ya shiga cikin taskar tarihin zamanin da, da kuma zamanin da ya rayu ya kwafo abubuwan da suka taimaka ya gina nasa adabin.

    Bincike ya nuna cewa waƙokin Sonnet da Thomas Wyatt ya ƙaddamar su ne kuma Shakespeare da wasu na zamaninsa suka ci gaba da tallatawa, kuma sun ja ra’ayin Thomas Campion wanda ya rubuce su a takarda, aka shiga rububinsu a gidajen al’ummar wancan zamani, (Wikipidia.org).

    Ke nan ba kamar yadda ake tunani ba, yawancin ayyukan adabin zamanin Sarauniya Elizabeth ta 1, ba wai rashin kyau ko ma’ana ko kuma rashin goyon bayan hukuma ba ne matsalar da ta sa aka kira su na yayi, ba kuma domin ana rubutun domin talakawa ba ne kaɗai ba, sai dai domin yanayin samuwarsu, wato yadda jama’a ke ta wawason su da kuma shiga cikin harkar saye da karantawa da rubutawa, ciki har da masu gari, Sarauniya.

    Babban abin da ya fi fitowa fili game da wannan zamani shi ne yadda gamaɗe da kwashe-kwashen ayyukan wasu ke taimakawa wajen gina sabon adabin da ya burge al’ummar wancan zamani. Saboda haka daga abin da aka tattaro dangane da adabin Sarauniya Elizabeth na Ingila mu iya cewa mafi yawan ayyukan adabi na ƙwarai, an samar da su ne a wannan lokaci, cikin waɗannan shekarun ne aka samar da rubuce-rubucen adabi, musamman abin da ya shafi zane da waƙoƙi, wasan kwaikwayo da sauransu.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Don karanta Fasalin Adabin Kasuwa A Duniya danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Fasalin Adabin Kasuwa A Duniya

    Fasalin Adabin Kasuwa A Duniya

    Daga nazarin da aka gudanar an fahimci cewa adabin kasuwa ko na yayi yana tafiya ne kafaɗa da kafaɗa da gangariyar adabin al’umma. Shi gangariyar adabin yana kasancewa ne tsakanin masu ilmi ko hannu da shuni ko kuma iyayen ƙasa. Duk wani abu da ba na wannan gungun mutane ba ne, yawanci shi ake wa laƙabi da adabin kasuwa ko yayi.

    Alal misali kusan duk yawancin ayyukan adabi da suke da wannan siffa a Turai ko Amurka ko sauran sassan duniya an samar da su ne tsakanin ƙarni na 16 da 17 da na 18, daidai lokacin da fasahar ɗab’i ko buga littattafai ta yi tashe a duniya.

    Kamar yadda bayanai suka yi nuni, yawancin jama’a da masana idan ana maganar adabin ƙarni na 16 da 17 da na 18, ana maganar gangariyar adabi ne ko na masu ilmi ko mulki ko dukiya, amma ba su kaɗai ne suka kwashi nasu kason ba daga rayuwar adabi, akwai adabin talakawa ko na kasuwa, wato na kowa da kowa, adabin da aljihun talaka zai iya biya, ya saya don karantawa.

    Wannan dama ta samu ne domin an samar da injinun buga littattafai na bakin hanya da suka ba talaka damar ya sami gurbin da zai buga nasa adabin. Ire-iren waɗannan ayyukan adabin su ne ake ba sunaye daban-daban da suka haɗa da Grub Street Literature ko Chapbooks. Waɗannan laƙabobi sun wanzu ne saboda la’akari da irin yadda aka samar da adabin ko wuraren da ake samar da littattafan ko kuma yanayin bugawa da sayar da su.

    Su dai Grub Street Literature su ne ayyukan adabin da aka samar daga wuraren buga littattafai da ke kan Titin Grub a Landon. Da yake a tsakanin ƙarni na 16 da 17 da na 18 an samar da marubuta na ƙwarai, sai dai rubutun nasu ya fi mayar da hankali ne ga masu-faɗa-a-ji, bai ta’allaƙa ga sauran jama’a ba, ga shi kuma sun fi sauran jama’ar yawa, wannan ya sa aka shiga neman wasu da za su agaza da nasu rubutun.

    Sai dai yawancin irin waɗannan marubuta ba su da sanayya ta zamani game da fasahar rubutu da ƙaga labarai, shi ya sa idan sun yi rubutu ake biyan su kuɗaɗe kaɗan, wannan ya sa suke rayuwa a cikin talauci da ƙunci.

    Shi kansa inda suke zama a bakin titin domin yin aikin nasu na adabi, wuri ne na ƙazanta da yawan lalata da tashin hankali; nan ake samun ɓarayi da mabarata da dai ire-irensu; nan ne marubutan da injinan buga ayyukansu suka ɗaura aure.

    Su kuwa Chapbooks littattafai ne da ake wa laƙabin littattafai masu arha, su ne ayyukan adabin da suka kasance na yayi ko na jama’a a karo na farko a wancan zamani na ƙarni na 17 da 18.

    Ba ruwansu da kamfanonin hukuma ko na gwamnati, ba kuma ruwansu da manyan kamfanonin ɗab’i da ke neman ƙazamar riba. Ana kuma shirya da buga irin waɗannan littattafai domin isar da saƙo ga talakawa ko masu sha’awar adabi, amma ba su da kuɗin sayen gangariyar adabin da ke wanzuwa a lokacin.

    Wannan damar ce marubutan da masu karatu ke amfani da ita domin su isar da saƙo ga sauran jama’a ba tare da kamfanin ɗab’i ya sa baki ba, yawancin abubuwan da ake samarwa sun haɗa da waƙe-waƙe da labarai da ayyukan addini da saƙonnin siyasa da makamantansu.

    Tarihi ya nuna cewa ko da hada-hadar ɗab’i da rubuce-rubuce ta kankama daga ƙarni na 15 da na 16 akwai ire-iren waɗannan ayyuka masu arha, yawancinsu sun fita kasuwa ne daga ƙarni na 17 da na 18 a Ingila, an nuna sun kai ƙoƙoluwa ne a shekarar 1775 ta yadda ake samar da littattafai sama da 200,000 a kowace shekara.

    Waɗannan littattafai sun taimaka wajen raya ayyukan adabin Ingila a wancan lokaci, sun sanya son karatu ga waɗanda ba su yi nisa a karatun ba, ko suka yi karatun suka watsar daga baya.

    Yawancin waɗannan littattafai ba su da yawan shafi, ba a yi musu bugun ƙwarai, sa’annan ana sayar da su da arha, daga wannan titi zuwa wancan, a maimamkon wuraren da aka tanada domin sayar da gangariyar adabi. Domin ganin yadda wannan fasali ya kasance, bari mu dubi yadda na zamanin Elizabeth ya kasance a Ingila.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Don karanta Fasalce-Fasalcen Adabin Kasuwa danna nan 

    Edita@rumasau-kallamu

  • Fasalce-Fasalcen Adabin Kasuwa

    Fasalce-Fasalcen Adabin Kasuwa

    Kamar yadda muka gani a babi na biyu, rayuwar adabin Hausa ta biyo zanguna mabambanta, wannan ba sai an yi dogon sharhi ba, domin kuwa daga tashin Hausawa na zaman gargajiya har zuwa lokacin da suka cuɗanya da baƙi an sami sauye-sauye da adabin Hausawa ya yi ko dai ta fuskar sauyawar riga daga ta gargajiya zuwa ta zamani (Larabci ko Ingilishi ko Faranshi) ko kuma ta sauyawar kayan cikin adabin saboda haɗuwa da sababbin ladubban rayuwa.

    Irin sauye-sauyen da aka samu daga gargajiya zuwa zamani abu ne da masana sun sha ambaton sa, ƙila abin da ba a fi mayar da hankali kai sosai ba shi ne yadda gwamutsuwa da baƙin al’amurra ke haifar da sababbin batutuwa da ke buƙatar ƙara bincike da nazari.

    Batutuwan da suka yi tashe a cikin ‘yan shekarun nan, musamman abin da ya shafi ƙagaggun labaran Hausa, bai wuce batun nan na Adabin Kasuwar Kano ba, wato littattafan da yawancinmu ke kira Labaran Soyayya da suka tuzgo daga sassa daban-daban na ƙasar Hausa da hedikwata a birnin Kano.

    Samuwa da watsuwa ko kuma karɓuwa da kuma ce-ce-ku-ce da wannan sabon salon adabi ya samu kansa a ciki, tsakanin marubuta da manazarta da masana a  ƙasar Hausa da ma sassan duniya daban-daban ya jawo ayyukan nazari da musayar miyau mai tarin yawa.

    Abin da aka yi ƙoƙarin yi a wannan babi shi ne shimfiɗa tabarmar nazari game da wannan fage ta hanyar neman sanin yadda adabin kasuwa yake ta hanyar tambayar ko akwai wani abu wai shi adabin kasuwa? Idan akwai shi to a yaya yake? Shin ana iya samun sa a ƙasashe masu tasowa kamar Nijeriya? Ko kuwa dai wanda ake da shi da ake kira Adabin Kasuwar Kano, an sa masa sunan ne domin cin mutunci da ɓatunci ko son rai?

    Abin da wannan babi ya sa gaba bai wuce amsa waɗannan da ma wasu tambayoyi da ka iya biyo baya ba, ta haka ƙila haske ya ƙaru game da wannan fage na tarihin adabi da zai bayyana mana bambancin da ke tsakanin adabi na zahiri da wanda ake kira na kasuwa da kuma yadda irin fasali ya samu ginuwa a ƙasar Hausa.

    Yanayin Adabi da Adabin Kasuwa

    A duk lokacin da aka soma batun da ya shafi Adabin Kasuwa abubuwa da dama ke zuwa zuciyar mai nazari ciki kuwa har da tunanin nan da ke nuni da cewa idan har akwai adabin kasuwa to ke nan ashe akwai wani adabin da ba na kasuwa ba.

    Idan kuma ka ɗauki ma’anar Adabin Kasuwa a luggance da ke nufin adabi na kowa da kowa ko na yayi ko abin da ke jan hankalin jama’a a kodayaushe, ke nan ana iya cewa akwai adabin da ke da akasin haka, wato adabin da ba na kowa da kowa ba, adabin manya, masu ilmi ko sarauta ko daraja a tsakanin al’umma, a taƙaice dai adabin da ke shimfiɗe a wani wuri domin manazarta da masana ko kuma wanda fagensa ba na kowane ɗan tagaja-tagaja ba ne wajen saye da karantawa da nazari, wato abin da ake wa laƙabi da gangariyar adabi.

    Saboda haka ƙoƙarin wannan babi shi ne ya bambanta tsakanin gangariyar adabin da wanda ake wa laƙabi da na kasuwa, domin ta haka ne za a gane yadda tunanin samuwar Adabin Kasuwar Kano ya tusgo, yake kuma gudana.

    Adabi dai kamar yadda masana suka yi nuni, kundi ko hoto ko madubi ne (dubi Ɗangambo, 1984:1 da Gusau, 1995:58 da Malumfashi, 2002) da ke ɗauke ko nuna hanyar gudanar da rayuwar al`umma. Za a iya fahimtar irin wannan adabi ta yin la`akari da abubuwa guda biyu; Na farko shi ne harshen da ake amfani da shi, wanda yake maƙunshin tarihi, kuma linzamin bayyana tunani ko kuma wata manufa. Na biyu kuma ita ce fasaha wadda ita ke bayyana tunanin da ke cikin zuciya a aikace (Muhammad, 2001:3).

    Shi kuma Cuddon (1999) da yake ƙoƙarin fitar da ma’anar adabi a luggance, cewa ya yi adabi na iya kasancewa abubuwa da dama da suka haɗa da wasan kwaikwayo da waƙa da ƙananan labarai da rubutattun litattafai da dai sauransu. Ya ci gaba da cewa idan har aka ce wannan aikin adabi ne, to maƙunshiyar aikin ta bambanta da sauran kwashe-kwashe na yau da kullum, musamman idan abin ya shafi gaskiyar lamari ko kuma faɗar tarihi, ke nan adabi yana da wasu siffofi da suka bambanta shi da wasu ayyuka da ba su da tasiri irin nasa.

    Duk da haka akwai ayyuka ko rubuce-rubuce da dama waɗanda ba a yi su don su kasance na adabi ba ne, amma kuma za a iya sanya su cikin aikin adabi; saboda ingancin aikin da asalinsa ko kuma irin kyawu da kuma fasahar da aka nuna wurin rubuta shi, kamar yadda (Cuddon, 1999) ya nuna.

    Daga wannan hasashe za a iya cewa adabin da ke da waɗannan siffofi da aka ambata a sama, shi ne ke kasancewa gangariyar adabi, akasin haka kuma sai ya zama wani abin, ƙila ma na kasuwa ko kuma gwanjo ko makamancin haka.

    Kamar yadda kowane sashe na duniya yake da gangariyar adabi, to haka a wasu sassan duniya ake da adabin kasuwa, (Market Literature) ko kuma adabin yayi. To amma idan muka ce adabin kasuwa, nan zai iya kasancewa na yayi, domin kuwa duk abu ɗaya suke tattaunawa. Duk abin da ya kasance na kasuwa to yana da alaƙa da yayi.

    Kasuwa dai wuri ne da ake saye da sayarwa na dukkan abubuwan rayuwa, duk wanda ke cikin wannan al`umma yana iya zuwa cikinta domin yin kasuwancinsa. Saboda haka adabin kasuwa wani ɓangare ne na adabin al’umma da kowa zai iya shiga cikin kogin ya yi iyo ko kurme; masani ko malami ko manazarci ko akasin haka. Ke nan irin wannan adabi wani abu ne ko dai waƙa ko wasan kwaikwayo ko ƙananan labarai, ko rubutattun litattafai da aka tsara a wani zangon rayuwar jama’a, ake kuma tsintar su a tsakanin jama’ar ba tare da wani kandagarƙi ba.

    Ta fuskar sayar da su ba a yi wani tanadi na wurin da ya dace ba, ko dai a same su a kasuwa ko wurin hirar matasa ko tsakanin matan aure ko makarantu ko kuma ma duk inda jama’a ke tururuwa domin karatu da rubutu. Haka kuma idan aka ce adabi na yayi ne ana nufin cewa zai rayu daga wani lokaci zuwa wani, wato akwai lokacin da yake tashe, akwai kuma lokacin da yake sallacewa, sai a bar masana da yin rubdugu kansa, (Malumfashi, 2002).

    Sai dai ya kamata a lura cewa akwai lokutta kuma da ake kallon irin wannan adabin na kasuwa ko yayi a matsayin adabin talakawa ko marasa shi, wato ya keɓanta ne ga wasu gungun jama’a a cikin wani zamani da ba su damu da adabin da ke gudana ba, ƙila ko don ba su da kuɗin sayen sa ko kuma ya kasance na masu gari. Idan aka faɗaɗa tunani a nan za a ga cewa shi wannan adabi na kasuwar ko yayin, saboda canzawar zamani ta sa ake masa wani sabon kallo, musamman da yake  ba a damu sosai da yi masa gangariyar nazari ba.

    Kai ba wannan ba ai masana da dama ba su ɗauki aikin adabi irin wannan abin tinƙaho ba, shi ya sa ba a damu da sanin inda ya sa gaba ba. Sai dai ko da aka soma nazarin nasa daga baya, an kuma shigo da ayyukan adabi da mutum na iya cewa ba irin na adabin kasuwa ko yayin da aka saba ji da gani ba ne.

    A halin yanzu daga cikin ayyukan adabin kasuwa ko na yayi da ake da su an sanya irin ƙagaggun labaran da a da ba su cikin irin wannan rukuni, wato irin waɗanda suka haɗa da labaran bincike ko tsafi ko na ban tsoro ko soyayya ko na Amurkawan dauri ko na ban dariya ko kimiyya, wato dai ƙagaggun labarai da miliyoyin jama’a ke saye da karantawa a sassan duniya daban-daban ko da kuwa ba a nazarin su a ajin adabi ko jami’o’i, musamman daga shekarun 1930.

    Har yau taƙaddama ba ta ƙare ba dangane da ko waɗannan irin ayyukan adabi na gangariyar adabi ne ko kuma kwamacala. Ga masana kamar yadda aka bayyana a (eNotes.com), irin wannan aikin adabi na kasuwa bai da nasaba da aikin ƙwarai, ana nuni da cewa dabara ce kurum ta samun kuɗi da suna, amma ba adabin da za a ta da jijiya wajen karatu ko nazari ba ne.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Don karanta Fasalin Ƙagaggun Labaran Hausa A Zamanin Zuwan Turawa danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Mai Maɗi Ke Talla (Mai Zuma Gida Ake Tad Da Shi)

    Mai Maɗi Ke Talla (Mai Zuma Gida Ake Tad Da Shi)

    JAN KUNNE GA MATASA KAN SU KYAUTATA RAYUWARSU A YAU BA SAI GOBE BA

    DAGA
    DR. MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD
    SASHIN HARSUNAN NAJERIYA
    JAMI’AR SULE LAMIƊO
    KAFIN HAUSA
    JIHAR JIGAWA
    07030803404
    Email:muazusaadukudan299@gmail.com

    TAKARDAR AKA GABATAR A TARON FAƊAKAR DA MATASA WANDA ƘUNGIYAR ƊALIBAN GARIN KAFIN HAUSA SUKA SHIRYA A MAKARANTAR FIRAMARE TA SPECIAL A GARIN KAFIN HAUSA RANAR LAHADI GA ARI 2023, 19 GA SHAWWAL 1444 DA ƘARFE 10:00 NA HANTSI DAIDAI BAN RUWAN DAWAKI.

    1.GABATARWA

    Da sunan Allah Mai rahama, Mai jinƙai, Mai kowa, Mai komai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban Ma’aika, Annabi Muhammadu (S.A.W). Wannan muƙala, na da ƙudurin jan kunne ga matasa a kan su san mahimmancin Matasa a rayuwar al’umma. Akwai fagagen da ake buƙatar matasa su wakilci al’ummarsu, matasa kan yi tasiri a tsakanin al’umma ta fuskoki da dama.

    Wannan kuwa a bayyane yake a inda sukan yi sanadin hulɗa ta kyautatu da kuma sauran al’amura gaba ɗaya. Akan samu matasan da kan taka rawa a fagage kamar haka: Ilmi, da Siyasa, da Tattalin Arziki, da Kiwon Lafiya, da Harkar Tsaro, da Sauran al’amuran zamantakewarsu, da sauransu. Haƙiƙa wannan ba zai samu ba sai ana da matasa masu nagarta waɗanda suka san ciwon kansu da kishin zuci.

    Matasan da ba su da kwaɗayi, babu lalaci, da munafunci, da jahilci, tabbas wannan shi ne zai fitar da wannan yanki namu daga halin da muke ciki a yanzu. Haka kuma tare da fito da fa’idojin samu matasa na gari nagartattu masu tarbiyya, da kuma illolin gurɓatattun matasa marasa tarbiyya.

    Bayan wannan kuma an ɗan tsakuro wasu daga cikin haƙƙoƙin yin tarbiyya tare da nuna irin nauyin da rataya a wuyan mahaifa, da Hukuma,da al’umma. Bisa wannan dalili ne yasa na yi wa wannan maƙalar take da “Mai Maɗi Ke Talla (Mai Zuma Gida Ake Tad Da Shi)”. Na kawo taken a matsayin matashiya ne, don ya ba mu damar lalubo mafita.

    Manufata ita ce, Matashi mai halin kirki jama’a ke nemansa, shi kuwa lalatacce shi ne ke neman jama’a, amma kuma ana gudunsa. Tare da fatan mai karatu ko saurare zai gano saƙon da ake son isarwa a ƙarshen maƙalar, don samun mafita ko a fid da jaki a duma.

    2. FASHIN BAƘI

    Ma’anar Maɗi
    Ma’anar Talla
    Ma’anar Zuma

    JAN KUNNE: shi kunne kashi uku ne, akwai fatar kunne shi ne mai faɗi, sannan akwai lilin kunne shi ne wanda mata ke hudawa su sanya ɗan kunne, sai gintsi wani sashi mai tudu mai ƙarfi wanda ya kare ramin kunne.

    1.3.0 SAMARTAKA (Saurayi)

    Samartaka ita ce rayuwar da yaro namiji ko saurayi kan yi tsakanin shekara 15-27 ko kuma zuwa lokacin da ya yi aure, kodayake wasu sukan wuce wannan matsayi ko shekarun amma ba su yi auren ba.

    Duk inda ka ji an cewa mutum saurayi, to lallai ne yana tsakanin waɗannan shekarun, to da zarar yaro ya ga ya kai matsayin saurayi, dukkan ɗabi’un sa sai su canza kamar canzawar murya, fitar gashi a gemun sa (haɓa) ko a hammatar sa, kuma saurayi tun daga nan tunanin sa zai kama, sannan kuma natsuwa ta zo masa amma fa idan akwai tarbiyya daga yarinta, amma wasu za ka gansu akasin abin da aka lissafa a baya, to a na babu tarbiyya ke nan, yarinta ba ta samu kyakkyawar tushe ba ke nan ba.

    1.4.0 BUDURCI(Budurwa)

    Budurci ita ce rayuwar da yarinya take yi tsakanin shekara 13/14 -20, ita budurwa ƙarƙari shekara ashirin (20), a nan idan yarinya ta wuce haka, to abu dai ba haka aka so shi ba, don rayuwar Bahaushe ta haƙiƙa, budurwar Bahaushe ba ta wuce 18-20 in ta yi tsauri, watau ta ƙi yin girma da wuri, ƙarshen budurci shi ne yin aure.

    Duk inda ka samu budurwa, to lallai ne ta kasance mai hankali, tunani, natsuwa da kunya in har akwai tarbiya daga iyaye, abin da yasa ka ji na ambaci kunya a wajen bayanin budurwa shi ne duk inda za ka samu budurwa bata rasa jin nauyin wani ko wasu in da ba an ɓata ta ba, babu wata jayayya a kan haka.

    Babban al’amarin da yake nuna cewar yarinya ta zama budurwa shi ne nono ko kuma buɗewar ƙugu ko kuma fara (haila) ɓatan wata kenan, amma ba dukkan budurwa kan fara haila a gidan iyaye ba.

    2.0.0 SU WANENE MATASA?

    Matasa na nufin kalmar jam’i ce ta kalmar matashi, Matashi shi ne yaro mai shekara 9-13, saurayi kuma daga 14-17.

    2.1.0 FAƊAƊA MA’ANAR MATASA

    Ko da yake yanzu an faɗaɗa ma’anar Kalmar daga ma’anarta ta asali, an yi masu kuɗin goro samari da ‘yanmata sai a kirasu da matasa. Yanzu haka a wannan zamanin sai ka ji cikakken mutum magidanci ko kuma a kira shi dattijo kusan ɗan shekara 30-45 wai sai a ce masa matashi. Ko da yake ba mamaki ai daman shi mutum yana gudun abubuwa huɗu, kamar haka:1.Laifi, 2. Ƙauyanci, 3.Tsufa, 4.Hauka.

    FAGAGEN DA MATASA ZA SU TSAREWA AL’UMMA

    Babu shakka, akwai fagagen da ake buƙatar matasa su wakilci al’ummarsu, matasa kan yi tasiri a tsakanin al’umma ta fuskoki da dama. Wannan kuwa a bayyane yake a inda sukan yi sanadin hulɗa ta kyautatu da kuma sauran al’amura gaba ɗaya. Akan samu matasan da kan taka rawa a fagage kamar haka:

    • Ilmi,
    • Siyasa,
    • Tattalin Arziki,
    • Kiwon Lafiya,
    • Harkar Tsaro
    • Da Sauran al’amuran zamantakewarsu.

    Haƙiƙa wannan ba zai samu ba sai ana da matasa masu nagarta waɗanda suka san ciwon kansu da kishin zuci. Matasan da ba su da kwaɗayi, babu lalaci, da munafunci, da jahilci,tabbas wannan shi ne zai fitar da wannan yanki namu daga halin da muke ciki a yanzu.
    Gaskiya da amana, kamewa da rashin kwaɗayi, sanin ciwon kai daraja Karen farauta
    Ma’anar Rago: na nufi mutum, malalaci, mara ƙwazo, ko juriya, shi kuma kishiyar jarumi ne, domin rashin jarumta ke haifar da ragwanci.

    4.0 Jarumta A Mahangar Al’ada:

    A tunanin wasu masana ana iya cewa jarumta wata ɗabi’a ce muhimmiya. Wannan yasa gaba ɗaya al’adar Bahaushe take ƙaunarta da kuma mai ita. Tabbas mutum mai kyauta na da farin jini da kwarjini da mutunci a cikin al’ummar Hausawa. Matuƙar aka san mutum jarumi ne, a wani lokaci har ƙoƙarin auren ‘ya’yansa ake yi, ko kuma idan shi ya nema a ba shi.

    A mafi yawan lokutta, kowa kan so yin ma’ammala da shi. Al’adar Bahaushe ta camfa auren jarumi, shi yasa ake kwaɗayin aurensa ko kuma a auri ‘yarsa, don fatan a haifi ɗa ya gado shi wajen jarumta. Bisa dalilin cewa jarumta na cikin ɗabi’u da akan gada daga uwa.

    Haka nan kuma akan iya koyon ɗabi’ar jarumta daga abokin zama ko maƙwabci. Bahaushe ya ce: “zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai”. Bisa wannan dalilai ne yasa Bahaushe ya ɗauki jarumta a matsayin ɗabi’a.

    4.1 Jarumta A Matsayin Ɗabi’a

    Akwai mutanen da suke kallon jarumta a matsayin ɗabi’a ce wadda akan haifi mutum da ita, kamar ta gado, da kuma ta baiwa daga Allah. Haka kuma akwai masu ganin cewa koyonta ake yi, ko nemanta da ƙarfi ko da magani.

    4.4 Rashin Tsoro:Tsoro na nufin firgita, watau dukkan wani abin da ya ɗaga hankalin mutum, wannan abu na iya kasancewa ko dai mutum, ko dabba, kai ko ma mene ne. Sannan wannan na faruwa ne a dalilin baƙunta, watau kamar rashin sabo, ko rashin amincewa, ko yarda. Alhaji Mamman Shata Katsina a waƙar Bakandamiya yake cewa:

    Mai tsoro ba shi gwaninta
    Mai tsoro ba shi zama gwani
    ko wane ne kuma ko ɗan wa
    Ka zama kamar ni fili waƙa,
    Sararin waƙa bai san tsoro ba,
    In na fito Shata ne.

    6.0 Mai Sana’a Ya Wuce Tagumi” ma’ana duk wanda yake da sana’a komai ƙanƙantarta ya fi ƙarfin ya yi tagumi wato ya shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi (damuwa). Bahaushe na cewa; ba a dariyar mai noma ko bai sayar ba ya ci abinshi, Allah fid da A’i ga rogo ko ba ta sayar ba ta ci abinta, sana’a goma maganin magasa.

    10.1 MATSALOLIN ZAMANTAKEWA A YAU

    Al’amarin zamantakewa na fuskantar matsaloli da dama, a sakamakon sauye-sauyen da zamani ya kawo, a rayuwar Bahaushe ta yau da kullum. Misali, kamar cuɗanya da wasu ƙabilu a inda aka samu shigowar baƙin al’adu, sannan kuma suka yi tasiri. Haka kuma zuwan ilmin boko shi ma ya yi tasiri ƙwarai a kan rayuwar Bahaushe.

    Don kuwa ya zo da wasu ɗabi’u, sannan ya kuma kawar da wasu ɗabi’u da a ka gada kaka da kakanni. Misali zaman gidan haya da wasu ƙabilu, sannan kuma ɗaki ɗaya ko ciki da falo. Kamar rowar zamani, da ƙyamar haihuwa, da gudun dangi, da son abin duniya, da rashin wadatar zuci. Haka kuma ana iya cewa ya kori wasu abubuwa waɗanda da yake an san Bahaushe da su.

    Taimakon mabuƙata, da suka haɗa da ‘yan ‘uwa ne, ko bare, da aka san Bahaushe da shi. Domin haka sai aka samu giɓi a tsakanin ‘yan uwa, ko maƙwabta. Musamman masu hannu da shuni, wannan kuwa ya ƙara nesanta jama’a da dama da sauran ‘yan uwa da abokan arziki. Wanda babu shakka ya kawo lalacewar zumuncin mu’amalla a wurare da yawa. Domin sau da yawa kyauta na ƙara qulla zumunci, rowa kuma na tsinka shi.

    Son ‘ya’ya: A halin da ake ciki a wannan zamani ba maƙwabci ba, kai ko da ɗan uwa ne, ko kuma malami ne yanzu in ya hori yaro, sai ka ga an nuna ɓacin rai. Wai cewar ya tsargi yaron ko ya sa masa ido ne , ba domin gyara halin yaron ne ya hore shi ba.

    Rashin Girmama Na Gaba: Wanda shi ma ya ƙara durƙusar da zamantakewa ƙwarai da gaske. Domin idan aka dubi baya a zamanin da, zamu ga cewar an san Bahaushe da girmama na gaba da shi. Don ba a gida ɗaya ba, ko a unguwa ɗaya ake, da zarar a ka ce ga wani babban wanda ake girmama shi. Haka kuma da zarar babba ya yi magana a kan wani abu zai yi a saɓa. Duk kuma abin da ya hukunta, ko mene ne ya zauna, babu mai tayarwa, saboda irin matsayinsa.

    Bayan haka kuma, a da akan samu biyayya a tsakanin ‘yan uwa kamar wa (yaya) yana da iko a kan ƙaninsa. Ma’ana in ya yi hukunci ta zauna. Haka shi kuma ƙanin ba shi da ikon ya yi jayayya, don biyayya tare da girmamawa. Haka kuma yake har a kan ‘ya’yansu. Shi kuma wannan na da ikon yin hukunci da na ‘yan uwa, babu wata fargaba, don ya san ya fi ƙarfin abin.

    Kai ko babu jinin dangantaka a tsakani, ko ta abota ta haɗa mutum da iyaye wani. To sai ka samu ana girmama wannan mutum a matsayin uba. A wannan zamani abin ya zamanton saɓanin haka. Gurɓacewar halayen mutane, wanda ya sa suka yi watsi da waɗannan lamuran yasa zumunci da aka sani a tsakanin Hausawa ya yi rauni. Kowa kansa ya sani, to amma sai wasu na ganin cewa ci gaba ne.

    12.0 TO JAMA’A INA MAFITA?

    Dole ne mu gyara yanayin mu’amalla a tsakaninmu, saboda shi zai kyautata zamantakewarmu ta hanyar mu faɗawa juna gaskiya. Mu kiyayi duk wani aiki ko wani abu wanda zai kawo saɓani a tsakaninmu. Mu tsaya mu natsu mu san kan mu da darajar da Allah ya ba mu.

    Zuciya: In gyara zuciyata, kai ma ka gyara zuciyarka, ke ma ki gyara zuciyarki.
    Harshe: In riƙe harshena, kai ma ka riƙe harshenka, ke ma ki riƙe harshenki.
    Hannu: In riƙe hannuna, kai ma ka riƙe hannunka, ke ma ki riƙe hannunki.
    Ido: In kiyaye idona, kai ma kiyaye idonka, ke ma ki kiyaye idonki.
    Amana: Tsare amana ta kaya, ko dukiya, ko ta Magana.

    Gaskiya: Mu rungumi gaskiya, mu faɗi gaskiya, mu yi aiki da gaskiya.
    Tausayi: Mu tausayawa junanmu a ma’amalla ta kowace fuska.
    Biyayya: Mu girmama na gaba da mu a mu’amallarmu.
    Kunya: Mu yi amfani kunya a rayuwarmu domin reshe ne na imani.
    Ƙarya: Mu kiyayi ƙarya a maganganunmu da ayyukanmu.

    Kwaɗayi: Mu kaucewa kwaɗayi ta kowace fuska.
    Son abin Duniya: Mu rage dogon buri.
    Girmama kuɗi: Mu rage bai wa kuɗi muhimmanci fiye da mutunci.
    Tsageranci:Mu guje shi domin shi ne, tushen fitna.
    Ha’inci: Mu guji yinsa, domin yana ɓata dangantaka.
    Wayar hannu: Mu yi hattara da wayar hannu, tsegumi da gutsuri-tsoma.

    KAMMALAWA;

    A ƙarshe wannan takarda, ta tsakuro wasu abubuwa a kan rayuwar matasa da matsayinta a wannan zamani tare da tsokaci a kan mahimmancin Matasa a rayuwar al’umma. Haka kuma tare da fito da ma’anar matasa da alaƙarsu da tasirinsu ga rayuwar Bahaushe jiya da yau, sauye-sauye da rayuwar Bahaushe ta gamu da su, tare da gano hanyoyi, ko dalilan da suka jawo waɗannan sauye-sauye.

    Ban da wannan kuma, za a dubi irin yadda hakan ya shafi al’adu, da ɗabi’un Bahaushe, har da rayuwarsa gaba ɗaya. Daga nan sai a hararo fa’idojin samu matasa na gari masu tarbiyya, da kuma illolin gurɓatattun matasa marasa tarbiyya. Bayan wannan kuma an ɗan tsakuro wasu daga cikin haƙkoƙin yin tarbiyya tare da nuna irin nauyin da rataya a wuyan mahaifa, da Hukuma,da al’umma. Allah Ya tsare mu Ya bamu ikon gyarawa amin. Assalamu alaikum

    MANAZARTA.

    Alhassan H. D (1982) Zaman Hausawa. Islamic Publication Bureau,
    Lagos.
    Bunza A.M.(2006) Gadon feɗe al’ada. Tiwel Nigeria Limited Surulere,
    Lagos.
    Banbale M.B.(1994) Kukan Kurciya. Ibramud Nigeria Limited, Zaria.
    Ɗangambo A. (1984) Rabe-Raben adabin Hausa da Muhimmancinsa ga rayuwar Hausawa.Triunph Publication Kano.
    Ɗangambo A.(1983) Kitsen Rogo. Triunph Publication Kano..
    Ɗahiru B (2007) Tafsirin Watan Ramadan. Rediyo Najeriya Kaduna.
    Imam A.(1937) Magana Jar ice na 1, da 2, da 3.Northern Nigerian Publication Company, Zaria.
    Madauci I.(1963)Al’adun Hausawa. Northern Nigerian Publication Company,
    Zaria.
    Sadiya G.Y. (2005) Talauci Hauka ne? Super Prints Press, Kano.
    Williams B.(1979) Human Design.Harvard University Printed USA.
    Yaro Y.I. (1971)Tatsunniyoyi da Wasanni. Oxford University Press,
    Ibadan.
    Zindani A.A.(2000) Human Development. Muslim World League Printing Press.
    Saudi Arabia.
    Sarki H.A (2000) Zuwan Musulunci a Afirka da shigowarsu Ƙasar Hausa.
    G.A. Computer Centre. Ikere – Ekiti, Ekiti State.
    Ɗanfodiyo S.U. (2002)Faɗakar da ‘Yan’uwa a kan halayyar Ƙasar Sudan.
    (Fassara) Muhammad Mode Shuni. C.I.S Usman Ɗanfodiyo University,
    Sokoto.

    Don karanta Buki A Bahaushen Tunani

    Edita@rumasau-kallamu