Category: Waƙa

  • Waƙar Bikin Ƙaddamar Da Manhajar WikiHausa

    Waƙar Bikin Ƙaddamar Da Manhajar WikiHausa

    TAKARDA WADDA AKA GABATAR A WAJEN BIKIN ƘADDAMAR DA MANHAJAR WIKIHAUSA, RANAR ASABAR 19 GA OKTOBA, 2024, A ƊAKIN TARO NA GIDAN TARIHI NA MALLAM AMINU KANO (MAMBAYYA HOUSE) DA KE GWAMMAJA, KANO

    Assalamu alai gare ku,
    Amsuwar ku da bakunanku,
    Don ku samu abin riƙewa.

    Ya Ilahu ka ƙara tsira,
    Gun Rasulu da bai da kyara,
    Har da alu jini na baiwa.

    Sa sahabbai ‘yan aminci,
    Bin su ne fa cika ta ‘yanci,
    Har mazowa ran tuƙewa.

    ‘Yan’uwa na tsara waƙa,
    Don maraba a wanga harka,
    Gun bikin haɓakar ga nawa.

    WikiHausa ta kikkira mu,
    Yau da safe ta ce mu zo mu,
    Ga mu mun zo ba musawa.

    Manhaja kundin bayani,
    Ko ka ce rumbun tunani,
    Don a yaɗa ilim ga kowa.

    Har na Hausa da Dini namu,
    Ko kwa al’adar gidanmu,
    Wadda ba ta faɗa da kowa.

    In kana son gane harshe,
    Tun a tsini har da tushe,
    Ga fa Wiki tai sanarwa.

    Har a Indiya an jiyo mu,
    Ko Amurka da Chana, Jamu,
    Har garin Manzo na kowa.

    Je ka Ingila ko kwa Chadi,
    Kun sani ba ma fasadi,
    Mu nufin mu a ceci kowa.

    Ga saraki gida na girma,
    Sun halarto babu ƙyama,
    Gaisuwar ku nake taɓawa.

    Ga furofesas da dama,
    Har da daktoci na girma,
    Sun halarci bikin yabawa.

    Ga fa Imam har da ɗalib,
    Har da yaran ‘J’ fa ɗalib,
    Ga marubbuta na kowa.

    Yau fa murna ce a raina,
    Ga mutan Zazzau gaba na,
    Har na Barno suna jiyowa.

    Hausa ce kundi na hairi,
    Ce tsare tsara da tsari,
    Tsattsakin tsaka ba tsirarwa.

    In kana son gane harshe,
    Babu wasa zo ka lasa,
    Yau fa Hausa nake taɓawa.

    Godiya gun malamaina,
    Ambaton ku yana a raina,
    Ga tsironku ana jiyowa.

    In kuna neman bayani,
    Mai karatun nan ku ji ni,
    Ce Nayaya maso ga kowa.

    Can fa Yobe Jiha mahaifa,
    Nan Kano girma da tsufa,
    Ran kushewa ban sanarwa.

    Baituka ashirin na tsara,
    Layuka uku duk na jera,
    Wassalamu nake wa kowa.

    Ibrahim Baba Ibn Garba Nayaya
    Shugaban Sashen Hausa, WikiHausa
    Nguru Writers’ Association of Nigeria (NWAN)
    National Teachers Institute, Kaduna.
    +2347066366586, +2348125351695
    ibrahimba182@gmail.com

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Waƙar Ban Mutu Ba (Fati Nijar)

    Waƙar Ban Mutu Ba (Fati Nijar)

     Mawaƙiya : Fati Nijar 

    G/Waƙa: Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

     Ba ta mutu ba. 

    Jagora : Ya jama’a ga ni da rai, 

    Fati Nijar ban mutu ba, X2 

    ‘Y/Amshi: Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

     Ba ta mutu ba. X2 

    Jagora : Nai sallama gare ku dukkan al’umma,  

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba

    Jagora: Waƙa nake sai ku saurara kuma, 

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba, 

    Jagora: Na sanar da ku kan ƙorafin, 

    : Da ake ta yi na yi gaba, 

    ‘Y/Amshi: Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

    : Ba ta mutu ba. 

    Jagora : Rannan da safe na ji ana tai min waya,                                 

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba, 

    Jagora: Wajen sau biyar duk jama’a na tambaya, 

     ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba, 

    Jagora: Wai gaske ne Fati Nijar, 

    : Ta mutu ko ba ta mutu ba, 

    ‘Y/Amshi: Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

    : Ba ta mutu ba. 

    Jagora: Sai na ce musu Fati ne ke maggana,

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba, 

    Jagora: Ban san irin wannan kalamai ƙanƙana, 

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba, 

    Jagora: Kui haƙƙuri Allahu in dai yai niyya, 

    : Ba zai bar ni ba, 

    ‘Y/Amshi: Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

    : Ba ta mutu ba. 

    Jagora: Masu faɗin haka, 

    : Wai shin me ta tsare muku? 

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba. 

    Jagora: Ku faɗa mana ko kuma laifi tai muku, 

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba. 

    Jagora: Kui wa Allah zancenku ya zama alheri, : Ba sharri ba, 

    ‘Y/Amshi: Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

    : Ba ta mutu ba. 

    Jagora: Ya jama’a ga ni da rai, 

    : Fati Nijar ban mutu ba, 

    ‘Y/Amshi: Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

    : Ba ta mutu ba.

    Jagora : Wani maƙaryacin gari, 

    : Ya je yana ta faɗin haka, 

    ‘Y/Amshi : Ba ta mutu ba, 

    Jagora : Wai yana faɗin kabarina shi ma yai haƙa, 

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba, 

    Jagora: Ƙarya kake ga ni da rai, 

    : Fati Nijar ban mutu ba, 

    ‘Y/Amshi: Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

    : Ba ta mutu ba. 

    Jagora : Ya jama’a ku dinga zancen alheri, 

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba, 

    Jagora: Ko kui shiru, 

    : Don kar ma kui sharri, 

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba, 

    Jagora: Wannan magana Annabi ne ya faɗa, 

    : Jama’a ba Binta ba, 

    ‘Y/Amshi: Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

    : Ba ta mutu ba. 

    Jagora : Roƙo nake Allah don Almusɗafa, 

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba, 

    Jagora: Dukkan sharri, 

    : Kadda ka bar shi ya ƙarfafa, 

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba, 

    Jagora: Ka ije mini kai min abin da mutum, 

    : Ba zai cuce ni ba, 

    ‘Y/Amshi: Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

    : Ba ta mutu ba. 

    Jagora: Nai gaisuwa dukkan masoya bai ɗaya,

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba, 

    Jagora: An mun sharri har ƙasarmu gaba ɗaya, 

    ‘Y/Amshi: Ba ta mutu ba, 

    Jagora: Ku yi haƙuri ga ni da rai, 

    : Fati Nijar ban mutu ba, 

    ‘Y/Amshi: Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

    : Ba ta mutu ba. 

    Jagora: Ya jama’a ga ni da rai, 

    : Fati Nijar ban mutu ba, 

    ‘Y/Amshi: Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

    : Ba ta mutu ba, 

    : Ayyaraye ga ta da rai Fati Nijar, 

    : Ba ta mutu ba.

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Taƙaitaccen Tarihin Hajiya Fati Nijar 

    Taƙaitaccen Tarihin Hajiya Fati Nijar 

    Sunan Fati Nijar na yanka shi ne Fatima, Mahaifinta kuma Abdurrahman wanda ake yi wa sunan rana Labaran, mahaifiyarta kuma A’ishatu ‘yar Hassan Ɗan Tanko. 

    Fatima (Binta) ta sami sunan fati Nijar daga Sadi Sidi Sharifai a lokacin da take yi masa amshi na waƙoƙin finafinai. 

    Labaran bisa asali mutumin Madawa ne cikin Jihar Tawa, kuma ɗan kasuwa ne mai zagayen garuruwa da ƙauyuka a ranakun cin kasuwanni a Jamhuriyyar Nijar. 

     Haihuwar Fati Nijar 

    Haihuwar Fatima (Binta) ta auku ne a ranar Alhamis 26/10/1984 a birnin Maraɗi, Jamhuriyar Nijar. 

    Bishiyar Nasabar Binta Labaran (Fati Nijar): 

    Ibrahim Tanko 

    Hassan 

    Abdurrahman ==== A’ishatu

    Saudatu Usman Fatima Ibrahim Isa Musa (Fati NIjar) (Binta) 

     Yanayin Karatun Fati Nijar 

    Fatima (Binta) ta yi karatun Alqur’ani, mai tsarki. Haka kuma Fatima ta kori jahilci ta fuskar ilimin boko. 

    Fara Waƙar Fati Nijar 

     Binta Labaran mutum ce mai sha’awar waƙoƙin gaɗa na ‘yan mata, musamman waƙoƙin dandali masu tafiya da wasannin al’ada. Fati (Binta) ta zama zabiya, mai zaƙin murya, wadda ake son a ji amon muryarta a tsakanin ƙawayenta. 

    A wata ziyara da Binta ta kawo wa ‘yar’uwarta wadda take aure a Nijeriya cikin 2003, ta sami damar haɗuwa da wasu daga cikin makaɗa da mawaƙan sitidiyo, tun ma ba Ali Baba Yakasai da Sadi Sidi Sharifai ba. 

    Daga nan ne ta shiga hidima ta yin waƙoƙin fina-finai har ta kai lokacin da take shirya waƙoƙi nata na kanta daga 2006, kuma tana yaɗa su ta albam -albam. Fati Nijar tana da kyakkyawar dangantaka da makaɗan sitidiyo na lokacinta a Nijeriya da Jamhuriyyar Nijar. 

    Fati Nijar tana yin waƙoƙi na sitidiyo a ƙungiya da kuma a kaɗaita. vii) Wasu waƙoƙin Fati Nijar sun haɗa da: 

    – Waƙar ‘Ɗan Amina’ 

    – Waƙar ‘Girma-Girma’ 

    – Waƙar ‘Nijar-Nijeriya’ 

    – Waƙar ‘Ala Gidigo’ 

    – Wakar ‘Na yi Ritayar So’ 

    – Waƙar ‘Duniya’ 

    – Waƙar ‘Uwa mai Gyara ɗanta’ 

    – Waƙar ‘Dawo Aliyu Dawo’ 

    – Waƙar ‘Gamji Jijjige’ 

    – Waƙar ‘Manguno’ 

    – Waƙar ‘Gidan Sauro’ 

    – Waƙar ‘Musa Ango’ 

    – Waƙar ‘Al’amarin Hassan yana ban Mamaki’1 

    – Waƙar ‘G Cell’ 

    – Waƙar ‘Fati Nijar ba ta Mutu ba’ 

    – da sauransu 

    Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau 

    Alhamis 26/4/2018 

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Saƙo Cikin Waƙa (1991)

    Saƙo Cikin Waƙa (1991)

    1. Ƙaunar ku ce ta jiƙa7 ni 
    2. Sai ta mantar ni tunani 
    3. Kuskuren nan da nake yi Ku sani ku kuka sa ni
    1. Tun da in nai muku laifi Ba wanda za ya kwaɓe ni.
    1. Sai da Allah ya nufe ni Rannan na samu sukuni.
    1. Zuciyata ta matsa min Waƙe nake jin za ni.
    1. Musa da Gambo da Shehu Waɗanda Arrahamani.
    1. Ya ba su ni’imominSa Masu bamban a kamanni.
    1. Jami’a Gambo ya samu Shehu ko angon Ƙarni. 
    1. Musa ya yi amarya Tun a can wasu makonni.
    1. Zuciya ba ta da laifi Murna za ta taya ni.
    1. Baban Mujahidu Shehu Fitila haskaka birni.
    1. Dauriyarka ta Koyarwa Ita ke sa ni yaƙini.
    1. Bayanka za ta yi haske Ta sha gaban zamani.
    2. Baban mujahidu ɗana Tsaya na ba ka bayani.
    3. Ka kira ɗanka Mujahid  Wallahi ka birge ni.
    1. Tun da kai ma a jihadi Kake in an yi tunani.
    1. Koda yaushe burinka  Kowa ya san addini.
    1. Kullum ba ka da hutun Jigila ƙauye da birni.
    1. Malam Musa ango  To, sai ka gafarce ni.
    1. Don ba ka so a yabe ka Ni ko yabon yau za ni.
    1. Inda ina kannewa A yau biki ya zuga ni.
    1. Kowa yana shagalinsa Ni ko ina ta tunani.
    1. Da ma fatan Malam Ya auri mai addini.
    1. Wadda ta san Larabci Da ilmin zamani.
    1. Gwana idan ta kawaita Zaƙaƙura a bayani.
    1. Allah gwani mai kyauta Ya ba wa liman rawani.
    1. Ya tabbatar da mafarki  Ƙuruƙuru a yaƙini.
    1. Angwanci da amarci Sauƙi mai kashe rauni.
    1. Ya zumunci makusanci  Mai maganin saƙonni.
    1. Cikinka babu takaici  In dai da so a tsakani.
    1. Wani haske na filasha  Ya tsai da ni a tunani.
    1. Da na farka na ga ango Gami da shi da sa’anni.
    1. Kowa yana shagalinsa Ba wanda ke alhini.
    1. Farin ciki ya rufe ni  Sai na sabunta tunani.
    1. Ga su malam Musa nan Masu halin ladani.
    1. Kullum kiran da suke yi A zo gurin imani.
    1. Wadda ta auri irin su Ta ci ribar zamani.
    1. Za ta rayu cikin ni’ima A ƙarqashin Ƙur’ani.
    1. Ba ita babu fasadi Na Bature Majanuni. 
    1. Mai kilisai da katifa; Ai ya huce karauni.
    1. Malam ina daɗa murna Allah ya ba ku sukuni.
    1. Da so da ƙaunar juna Su ƙara inganta gini.
    1. Ya ba ku ‘ya’ya nagari Jigajigan addini.
    1. Malam Gambo Lawan, ko Sibawaihin Zamani.
    1. Dole ne in masa murna Ta masoyi da amini.
    1. Yau farin ran da nake ji Ya fi ƙarfin na yi muni.
    1. Tun da dai Gambo ya dace Ya adon ta da kyan launi.
    1. Ilmi ne kwaɗayinsa  Shugaban kowane ƙarni.
    1. Ai ko ya samu taraƙƙi”8 Ya haye ƙolin tsauni.
    1. Allah ya ba mu najahi  Mu ja gaban zamani.
    1. Ya azurta mu da ilmi  Gami da kyan imani.
    Domin karanta cikekken littafin Danna nan 

     

  • Waƙar Ya’yan Alhazai

    Waƙar Ya’yan Alhazai

    Ya’yan Alhazai laƙabi ne na Hausawa da Fulani da Bare-Bari (‘Yan Asalin Najeriya) waɗanda aka haife su a ƙasar Sudan, sakamakon tafiya aikin Hajji da iyayensu suka yi.

    1. Ganin ku ‘ya’yan Alhazai ya sa ina; 
    2. Ta tunatunin manya mazajen gaskiya. 
    3. Waɗanda ƙaunar Rabbana tsantsa ta sa; 

    Suka ƙaurace wa gida da daɗin duniya. 

    1. Ba kasuwanci koko noma za su je; 

    Ba bare a ce wannan bahaushe zai iya. 

    1. A a nufinsu kawai su keta duhun dare;  Su fice saharar nan kamar tatsuniya.
    1. Su je “Hijazu”4 Gabas su yo aiki Hajji;  Sannan su ga masu da sun ci burin duniya.
    1. Tun ma Bature bai yi ko da keke ba; 

    Balle su jirgi masu keta samaniya. 

    1. Sai dai su hau doki gami da su taguwa; 

    Koko su Alfadari da Jaki sha-wuya. 

    1. Ko Raƙumi ko ma su wanke ƙafafuwa; 

    Da ƙafarsu za su fito su doshi Sa’udiya! 

    1. Gaishe ku! Bayin Rabbana yaya kukai; 

    Da zama a zango inda babu gida ɗaya? 

    1. “Allahu Akbar” ya kuke a cikin Hama5

    Da lokacin rana kamar garwashiya. 

    1. Fatar jikunku kamar gasa ta ake ta yi; 

    Ina kukan samo ruwan sanyi niya. 

    1. Yaya kukai da harin ɓarayi masu son; 

    Su kashe mutum su fice da ɗimbin dukiya 

    1. Ko ko harin kura da kan yi cikin dare;

    4 Hijaz-Qasar Makkah da Kewaye. 

    5 Hamada – Sahara ke nan.

    Ku ko kuna tsaye tun daren har safiya. 

    1. Wata ma a sannan naƙuda kan zo mata: 

    Mata su je mata har ta haife lafiya. 

    1. Fallomi ga su Junaina har da Lubayya ma; 

    Dukkansu su shaida da kun yi gwagwarmaya. 

    1. Khartuumu Undurmana ga Madaninmu can; 

    Maƙil da ‘ya’yayen fataken gaskiya. 

    1. Maiwurno ga Sinari Sinja akwai su can; 

    A garin Damazin har zuwa ga “Isofiya” 

    1. A garin Gadarifu har zuwa Kasala da Bor

    Sudan Sawakin duk suna can bai ɗaya. 

    1. Haka nan kukai artabu ɗulin shekaru; 

    Kafin a ce kun je ku bakin Maliya. 

    1. Kogin da babu kamarsa ya haɗe duniya; 

    Zurfi da faɗi ga yawan ambaliya. 

    1. Sannan ku ajjari6 Murkaba wato kwami; 

    Don keta hamshaƙin ruwan nan Maliya. 

    1. Kukan yi kwanakki ɗari a cikin ruwa; 

    Wa ke batun girkin tuwo balle miya! 

    1. Amma a sannan kun yi fama, ba ta ma; 

    Kogi ake ba kawai, abokan taffiya. 

    1. Wani ba jimawa sai amai domin jiri; 

    Kullum yake yi har da tashin zuciya. 

    1. Wani ko gudawa in ta rafkake shi sai; 

    Dai ai ta biƙi nai da kiwon lafiya. 

    1. Shi ko matuƙin ba ruwansa gama mafi; 

    Yawan su ba su da tausayi ko da ɗaya. 

    1. Cewa yake yi ba ruwana ni idan; 

    Wani ya mace lallai a jefa Maliya. 

    1. Haka nan kukai har sai da kun ka haye ruwa; 

    Kuka je ku bautar Rabbana Sarki Ɗaya. 

    1. Haka nan kukai gumu a faɗin rayuwa;
    2. Gaishe ku jikoki da ‘ya’yan alhazai; 

    Ku kanku aya ce ta aikin gaskiya.

    Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
  • Waƙar yaƙin Korona

    Waƙar yaƙin Korona

    1. Bismillah za ni fara
    Waƙar yaƙar Korona

    2. Nai Salati nai Salama
    Ga manzo mai Madina

    3. Mu haɗo ƙarfi da ƙarfe
    Domin yaƙar Korona

    4. Duniya yau ta ɗumame
    Da annobar Korona

    5. Da ta ɓullo can ƙasar Sin
    Ta wuce har Basalona

    6. Ta mamayi duk Urubba
    Har Amurka akwai Korona

    7. Asiya, har nan Afirka
    Mun ga kutsowar Korona

    8. Larabawa ta shige su
    Ai waba’i ce Korona

    9. Garkuwa, mu biɗo ta ƙarfe
    Don tare kibiyar Korona

    10. Wanke hannaye da Soda
    Don cire ƙwayar Korona

    11. Ku rufe baki da hanci
    Don gudun shaƙar Korona

    12. Ku tsaya can nesa-nesa
    Haka nan in za ku zauna

    13. Tsafta ta jiki, muhalli
    Kuma cunkoso a daina

    14. Garzaya a gwado jikinka
    In alamu sun ka nuna

    15. Zazzabi mai sa kasala
    Tari da murar Korona

    16. In ko numfashi ya shaƙe
    Sai a killace mai Korona

    17. Har sai an maganin ta
    Can a killace za ya zauna

    18. In ka so ka fice ƙasarku
    To ka fara gwajin Korona

    19. Haka ma in can ka sauka
    Sai ka ƙara gwajin Korona

    20. Ga riga-kafi mai aminci
    Kariyar cutar Korona

    21. Biɗi inda ake a yi ma
    Ta ka allurar Korona

    22. Za ta ƙarfafa garkuwarka
    Domin yaƙar Korona

    23. ‘Yan uwa nan zan taƙaita
    In kuna son ambato na

    24. Faruuku Sarkinfada
    A Kanon Dabo gari na

    25. Ya Ilahi ka taimake mu
    Ka Ije cutar Korona

    26. Domin darajar Nabiyyu
    Ka kashe ƙwayar Korona

    Alhamdulillahi

    ©Faruk Sarkinfada
    Saturday 20/03/2021
    11:25 pm
    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Lokaci Da Yanayin Sadarwa A Waƙar Baka

    Lokaci Da Yanayin Sadarwa A Waƙar Baka

    Bisa yawancin lokuta na sadar da waƙoƙin baka na Hausa, kamar yadda aka yi bayani a baya; akan sadar da waƙar baka ne a lokaci na safiya ko na hantsi ko na rana ko na yammaci ko na daddare da dai sauran lokuta.

    Haka kuma Hausawa sukan sadar da waƙoƙin baka a kowane yanayi na damina ko na kaka; ko na rani ko na bazara ko na hunturu ko na ɗari. Alal misali waƙoƙin noma an fi yin su a yanayi na damina, wato lokacin da ruwan sama yake sauka.

    Haka kuma waƙoƙin ɓullowar kaka akan yi su ne da zarar damina ta shige ko tana gab da wucewa; wato an cimma amfanin gona ka’in da na’in, da dai sauransu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wuraren Sadawar Waƙar Baka danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Aiwatarwa Da Sadarwa A Waƙoƙin Baka Na Hausa. wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Sadarwa A Waƙar Baka

    Sadarwa A Waƙar Baka

    Bayan makaɗan baka sun gama tunanin waƙar da za su yi; sai kuma su zo, su sadar da ita ga al’umma.

    Ana sadar da waƙar baka ga Hausawa a ɗaiɗaikun gidajensu da wani wuri da suka shirya wanda ake kira dandali; wato wurin yin wasannin jama’a da a yayin farauta ko noma, musamman a lokacin gayyar noma a fadojin sarakuna, da lokacin bukukuwan al’umma da kuma taruka na makarantu da sauransu.

    A ma’ana ta lugga ko ta ƙamus, Ƙamusun Hausa (2006:380) ya bayyana kalmar sada tana nufin (i)gama (ii) isar da (iii)sulhunta. Shi kuma littafin Ƙamus na Keɓaɓɓun Kalmomi wato Hausa Metalanguage (Muhammad, 1990 UPL Ibadan:104) cewa ya yi, kalmar Sadarwa da Ingilishi tana nufin Communication.

    Shi ma Awde (1996:135) yana ganin kalmar Sadarwa tana nuni ne Communications da Ingilishi.

    Sadarwa a ilmin waƙar baka tana yin nuni ne game da wasu dabaru; waɗanda ake amfani da su wajen isar da waƙoƙin baka ga waɗanda ake yiwa su. Ana isar da waƙoƙin baka ta hanyar rera wa mutane a wasu wurare da lokuta da yanayi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Lokaci da Yanayin Sadarwa a Waƙar Baka danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabo A Waƙoƙin Baka danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Aiwatarwa Da Sadarwa A Waƙoƙin Baka Na Hausa wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yanayin Harshen Waƙar Baka

    Yanayin Harshen Waƙar Baka

    Mazubi na harshen waƙar baka yana ɗauke da ƙwayoyin sauti da gaɓoɓi da kalmomi da kuma jumloli; waɗanda suke ba makaɗa damar su iya aiwatarwa da sadarwa cikin rerawa a sauƙaƙe.

    A zubi na waƙoƙin baka, daɗa a wajen makaɗa masu shiri na baka ko masu shiri na ƙire ko haye ko masu shiri na rubuce; suna shirya kalmomi ne da kansu ko wasu su shirya musu, sannan su saka amo na murya da na kiɗa, su kuma rera.

    Waƙar Baka

    Shirya Kalmomi

    Shiri na Baka Shiri na Ƙire/Haye Shiri na Rubuce

    Kalmomi Kalmomi Kalmomi na kai
    na kai na kai
    Satar waƙar Kalmomi na wani
    Satar Waƙa

    Idan aka lura, dangane da harshe a zubin waƙar baka, makaɗa da mawaƙa suna tasirantuwa bisa wasu matakai na ginawa da shirya waƙa da suka haɗa da:

    3.1 Shirya Kalmomi

    Kamar yadda aka nuna a baya, waƙoƙin baka ana shirya su ta gaɓoɓin kalmomi bisa zaɓi na makaɗi. Kalmomi a harshe su suke yi wa makaɗi tsani ya saƙa saƙonni, manya da ƙanana, a waƙa.

    3.2 Daidaita Murya da Amon Kiɗa

    Makaɗi ko mawaƙi yana daidaitawa ne a tsakanin amon muryarsa, wadda take tafiya a saje da gaɓoɓi da kalmomi na zubinsa; da kuma amon kiɗa wanda yake wanzuwa daga kayan kiɗa waɗanda yake amfani da su. A lokacin da wannan yanayi ya daidaitu, sai rauji na waƙa ya wanzu; wanda yakan zama gajere ko dogo ko matsakaici, gwargwadon yanayin kalmoni da kuma amon kiɗan da aka ɗauka.

    3.3 Daidaita Tunani a Saɗaru

    A waƙar baka akan daidaita tunani da ma’ana, babba ko ƙarama ta waƙa ta gurabun kalmomin waƙa waɗanda ake rerawa ta hanyar tsayin rauji a saɗaru. Dole ne tunanin waƙa ya dinga tafiya tare da zubin kalmomi a saɗaru na waƙa.

    3.4 Kaucewa Dokokin Nahawu

    Harshen waƙa, musamman yadda wani bi yakan ƙunshi tarin kalmomi, sannan da yanayin rauji da rerawa; yakan wadatu da tsarinsa ne har ya dinga bauɗe wa wasu dokokin nahawu.

    Shi harshen waƙa yakan sanya masana nahawun harshe da jujjuyawar kalmomi da karin harshe da sauransu; su yi ta ƙoƙarin gwada ɗora kalmomi da jumloli na waƙa a kan daidaitaccen tsarin nahawu. A wajen waƙar baka ƙirƙirowa da baddala kalmomi ko tsarin jumla da sauransu wata hanya ce ta kamalar harshen waƙa.

    3.5 Jefa Dabarun jan Hankali

    Wasu daga cikin hikimomi na harshe wanda ake shirya waƙa da shi, sukan yi naso a waƙa. Makaɗi yakan yi amfani da dabaru na yi wa zubin waƙarsa kwalliya ya daɗa armasa waƙar; ya ƙara mata nagarta cikin dausayin harshe. Dabarun nan na jan hankali sukan iya sanya harshen waƙa ya ƙara tsada; ya zama mai nauyin fahimta, mai jefa sarƙadodo a wajen warware ma’ana.

    Akwai dabarun jan hankali da yawa waɗanda makaɗa da mawaƙa suke jejjefawa a waƙoƙinsu da suke bambanta a daraja da nauyi na kowace waƙa; ko kuwa a mabambantan waƙoƙi na makaɗi ko mawaƙi ɗaya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Makaɗi a Sarrafa Harshen Waƙa danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Waiwaye Kan Harshen Makaɗi A Zubin Waƙar Baka wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Dangantakar Harshe da Waƙa

    Dangantakar Harshe da Waƙa

    Harshe da Waƙa – Harshe wani muhimmin sinadari ne wanda al’umma take bayyana al’adunta da hali na zamantakewarta. Mutane a ɗaiɗaya ko a rukuni ko a ƙungiya na isar da muradansu a rayuwa ta hanyar harshe.

    Idan aka dubi kowace irin al’umma ko ƙabila za a ga tana da harshe nata; wanda take amfani da shi a matsayin harshen sadarwa.

    Harshen Hausa, harshe ne wanda yake sarrafa ƙwayoyin sauti cikin gaɓoɓi da kalmomi da jumloli; ya shirya magana wadda za ta ƙunshi wata ma’ana ko saƙo; wadda idan an sadar da ita, mai sauraro yake ji, ya fahimta.

    Ɗantumbushi (2012: 37); ya nuna harshen Hausa yana girma da ɗaukaka da faɗaɗuwa a cikin shuɗewar lokuta. Wannan harshe na Hausa yana kuma da karuruwa (Ɗantumbushi, 1998 & 2004; Amfani, 2011), musamman yana da karin gabas da karin yamma; waɗanda sukan sami bambanci ta hanyar sauti da kalmomi da siga ko tsari na gina jumloli da sauran wasu sassa na nahawu.

    Karuruwan Hausa

    Karin Gabaci Karin Yammaci

    Kananci – Sakkwatanci
    Dauranci – Garewanci
    Zazzaganci – Katsinanci
    Bausanci – Gobiranci
    Gudduranci Kurfayanci
    Zamfaranci
    Arewanci

    Makaɗin Hausa ya ɗauki harshen Hausa abokin hulɗa, ta haka harshen ya zama mai tagomashi a gare shi; wanda yake aiki da shi a kowane lokaci ba tare da wata tankiya ba. Makaɗi yakan iya fyauce hankali da tunanin mutum a yayin da ya sarrafa harshe bisa tsari da yanayi na waƙar baka. Harshe yakan haɗa hulɗa tsakanin makaɗa da jama’a ba dangi na iya ko na baba.

    Alan waƙa ya amince da harshen waƙa, harshe ne mai shigar kutse a cikin zukatan jama’a. Ga abin da ya ce:

    Jagora : Hikkima ba ruhi ko jiki ba hangena,
    : Ba aibn kallo ko ɗauki duba tuna,
    : Hikkima ba Rauhanai ka bai ba dangina,
    : Hikkima Ilhamiyya nake karatuna,
    : Jakadiyata waƙa mai tafi da saƙona,
    : Jakadiyata ba ƙwuya a aika saƙona.

    Makaɗan baka sukan yi amfani da harshe a bisa wasu mabambantan halaye. Harshe yakan zama zubi na mutum, makaɗi; tun ma ba idan aka yi la’akari da yadda tunani yake ginuwa a ɗayan-ɗayan mutane ba. Haka kuma nauyin ilimi da yin nutso a falsafa da fasaha; da wayewa kan sanya hanyoyin amfani da harshe a wajen makaɗa su bambanta (Alhassan, 2012: 128).

    A lokacin da makaɗi ko mawaƙi yake shiryawa da aiwatar da waƙa shi yake da mulki da harshe; baiwa da azanci da zalaƙa suna yi wa mai waƙa, makaɗi, jagora a zubi na waƙa (Yahaya, 2012: 233).

    Kila wannan harshe na waƙa mai kaifafa ma’ana ya sanya waƙa take saurin isar da saƙo; da fitar da ma’ana a cikin kalmomi ƙalilan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Gudumawar Waƙoƙin Baka na Situdiyo Wajen Haɓaka Tattalin Arziki danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka danna nan.

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Waiwaye Kan Harshen Makaɗi A Zubin Waƙar Baka; wanda Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.