Ma’anar Fiyano

0
611

Masana sun tofa albarkacin bakinsu wajen bayyana ma’anar fiyano (Piano). Misali: Gusau (2008:347) ya ayyana Fiyano wata alama ce ta yin kiɗa wadda Hausawa suka samu daga Turawa.

Sun sami wannan ala bayan yaƙin basasar Nijeriya wajejen shekarun 1970 lokacin da wasu ƙabilun Kudancin Nijeriya; suka fantsamo cikin Arewa. Fiyano (Piano) aba ce wadda ake kaɗawa ta bayar da amo nau’i-nau’i, mai diri ko mai zaƙi ko mai kauri gwargwadon yadda ake buƙata. Turawa sukan gwama masa jita da tasoshi da ganguna a lokacin kaɗa shi.

Fiyano abin kiɗa ne na Turawa wanda suke haɗa shi da jita da wasu tasoshi da nau’o’in amo na jita; da ganguna da kayan bushe-bushe da buge-buge da sauransu”.

Zainab (2009:83):

Ta bayyana fiyano da cewa, “Fiyano abin kiɗa ne da ake amfani da madannai fari da baƙi (keyboard) wadda ke girke a kan tebur don samar da sautin kiɗa.

Fiyano wata na’ura ce wadda ake amfani da madannai (keyboard) fari da baƙi. Kowane yana aiki kuma da irin sautin kiɗan da yake bayarwa ko kiɗan da ake buƙata.

Ita Fiyano tana amfani da wutar lantarki da kuma batir. Tana daga cikin sanannun kayan kiɗa na duniya”.

Binta (2011:76):

Ta bayyana cewa “Fiyano (Piano) wata na’ura ce mai amfani da wutar lantarki wadda take bayar da amo na kiɗa iri daban-daban.

Mutum ɗaya yana iya amfani da fiyano ya yi waƙa kuma ƙungiyar makaɗa ma suna yin amfani da fiyano domin rera waƙoƙinsu. Haka nan Kiristoci suna yin kiɗan fiyano a coci”.

Gusau (2016:27):

Ya sake bayar da ma’anar fiyano (Piano) da cewa, “Na’ura ce wadda ake iya samar da amo iri-iri na yawancin kayan kiɗa. Ana iya adana amo daban-daban da fiyano ta daddanna wasu mabuɗan amo da aka shirya masa; Fiyano yana da mazauni wanda ake ɗora shi a kansa. Mutum ɗaya yake sarrafa kiɗa da fiyano”.

Fiyano abin kiɗa ne mai girma wanda yake da madannai fari da baƙi a jere. Ana buga fiyano a zauna a gabanta, sannan a latsa madannan. Akwai kiɗa kala-kala a har dubu bakwai da ɗari biyar (7,500) a cikin fiyano.

Lokacin da Hausawa suka sami wannan abin kiɗa, sai suka cusa masa amon kiɗa na gargajiya kamar molo da ganga, da kotso, da shantu, da tafi, da busa, da kaca-kaura, da duma da sauransu. Fiyano yana da amon kiɗan zamani da na gargajiya. Ana ɗaukar fiyano a yi kiɗa da ita nan take (live performance). Fiyano koyon shi ake yi, sai a hankali ake fahimtarsa. An ci gaba da amfani da fiyano ana aiwatar da waƙoƙin Hausa.

Daga baya, an samu kiɗan komfuta wanda ita ma tana da nata kaɗe-kaɗen. Koda yake asalin kaɗe-kaɗen nata daga fiyano ne. Ma’ana daga fiyano ake turawa a cikin kwamfuta. Ana tattara kiɗan fiyano a mayar da shi a kwamfuta. Ana amfani da waya (midi cable) wajen haɗa fiyano da kwamfuta.

Kwamfuta tana da abin da ake kira (softwares) kamar Sonar. Daga cikinsa ne ake ƙirƙirar duk wani kiɗa. Akwai abin tace murya (cool edit) da (sound edit) a cikinsa.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Kiɗan Fiyano A Wajen Hausawa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Ire-iren Kiɗan Fiyano danna nan

labarin da ya wuceIre-iren Kiɗan Fiyano
Labarin na GabaYadda Ake Beef Burger