Category: Kiwon Lafiya

Mun samar da wannan ɓangaren ne domin koyar da ilimin yadda ake kula da lafiya a cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Za ku iya kai wa gare su ta hanyar amfani da kwamfutoci ko wayoyin hanu.

wikiHausa ta kowa ce. Kowa zai iya taimakawa da ilimi ko gyara. Bugu da ƙari, kowa na iya amfani da wannan kafa domin koya ko koyarwa.

  • Harara Garke (STRABISMUS)

    Harara Garke (STRABISMUS)

    A likitance ana kiran harara garke “strabismus”. A turance kuma yana da sunaye da yawa kamar “cross-eye” ko “boss-eye” ko “squint-eye” ko “cock-eye” ko “lazy-eye”. Harara garke yanayi ne da ke sanya idanun mutum su kasa daidaituwa (misalignment) idan yana kallon wani abu. WatO za a ga kamar ba abin yake kallo ba, alhali kuma shi yake kallo. Ana iya haihuwar mutum da harara garke, ko kuma ya same shi lokacin yarintarsa, ko bayan ya girma. Matsalar lalacewar tsokokin ido ita ce babbar abinda ke kawo shi.

    TSOKOKIN DA SUKE SARRAFA MOTSIN IDANU (MUSCLES THAT CONTROL EYES MOVEMENT)

    Akwai tsokokin da suke sarrafa motsin idanun mutum. Ana kiransu “ocular eye muscles”, kuma guda 6 ne kamar haka:

    1. Tsokar da take riƙe ƙwayar ido daga sama (superior rectus muscle): Babban aikinta shi ne juya ƙwayar ido sama idan buƙatar hakan ta taso. Sa’annan tana taimakawa ƙwayar ido juyawa gefen hanci. Idan tsokar tana da matsala, to, ƙwayar idon ba za ta iya juyawa ta kalli sama ba. Hakan zai sa idan mutum yana buƙatar juya idanunsa sama, sai ƙwayar idon mai lafiya ta juya sama, amma mai matsalar ta kasa juyawa.

    2. Tsokar da take riƙe ƙwayar ido daga ƙasa (imperior rectus muscle): Babban aikinta shi ne juya ƙwayar ido ƙasa idan buƙatar hakan ta taso. Sa’annan tana taimakawa ƙwayar ido juyawa gefen kumatu. Idan tsokar tana da matsala, to, ƙwayar idon ba za ta iya juyawa ta kalli ƙasa ba. Hakan zai sa idan mutum yana buƙatar juya idanunsa ƙasa, sai ƙwayar idon mai lafiya ta juya ƙasa, amma mai matsalar ta kasa juyawa.

    3. Tsokar da take riƙe ƙwayar ido daga gefen hanci (medial rectus muscle): Aikin wannan tsokar shi ne juya ƙwayar ido ta kalli gefen hanci idan buƙatar hakan ta taso. Idan tsokar tana da matsala, to, ƙwayar idon ba za ta iya juyawa ba. Hakan zai sa idan mutum yana buƙatar juya idanunsa gefen hanci, sai ƙwayar idon mai lafiya ta juya, amma mai matsalar ta kasa juyawa.

    4. Tsokar da take riƙe ƙwayar ido daga gefen kumatu (lateral rectus muscle): Aikin wannan tsokar shi ne juya ƙwayar ido gefen kumatu idan buƙatar hakan ta taso. Idan tsokar tana da matsala, to, ƙwayar idon ba za ta iya juyawa ba. Hakan zai sa idan mutum yana buƙatar juya idanunsa gefen kumatu, sai ƙwayar idon mai lafiya ta juya, amma mai matsalar ta kasa juyawa.

    5. Tsokar da take riƙe ƙwayar ido daga saman ƙwayar idon (superior oblique muscle): A saman ƙwayar ido take kuma ta gangara har can cikin ƙwayar idon. Babban aikinta shi ne juya ƙwayar ido ta kalli gefen hanci da kuma gefen kumatu. Idan tsokar tana da matsala, to, ƙwayar idon ba za ta iya juyawa gefen hancin ko gefen kumatun ba. Hakan zai sa idanunsa tsayawa kyam babu juyawa dama ko hagu.

    6. Tsokar da take riƙe ƙwayar ido daga ƙasan ƙwayar idon (imperior oblique muscle): A ƙasan ƙwayar ido take kuma ta yi sama har can cikin ƙwayar idon. Babban aikinta shi ne juya ƙwayar ido ta kalli gefen kunci. Idan tsokar tana da matsala, to, ƙwayar idon ba za ta iya juyawa ba.

    RABE-RABEN HARARA GARKE (TYPES OF STRABISMUS)

    Bisa la’akari da tsokokin da suke sarrafa motsin idanu, da kuma illar rashin yin aikinsu idan suna da matsala, harara garke ya rabu gida 4 kamar haka:

    1. Harara garke wanda idanu suke kallon gefen hanci (esotropia).

    2. Harara garke wanda idanu suke kallon gefen kunci (exotropia).

    3. Harara garke wanda idanu suke kallon sama (hypertropia).

    4. Harara garke wanda idanu suke kallon ƙasa (hypotropia).

    NAU’IN HARARA GARKE (TYPES OF STRABISMUS)

    Nau’in harara garke waɗanda suka fi shahara guda 2 ne:

    1. Harara garke mai faruwa a lokacin da mutum yake ƙoƙarin kallon abinda ke kusa da shi (accommodative strabismus): Irin wannan harara garken ba a ganin mutum da shi sai idan yana kallon abinda ke kusa. Ma’ana, idan yana kallon nesa, to, ba za a ga harara garken ba. Amma idan yana kallon kusa, sai idonsa ɗaya ko duka biyun su kalli gefen hancinsa. Hakan yana faruwa ne saboda baya iya ganin abinda ke kusa sosai, har sai idon ya karkata gefen hancinsa. Ƙoƙarin daidaita idon ya kalli abinda ke kusa, shi ne “accommodative” ɗin. Wannan ya fi kama mutum a lokacin yarinta, kuma akan yi maganinsa ne ta hanyar amfani da tabarau na likita.

    2. Harara garke mai faruwa lokaci-lokaci (intermittent strabismus): Wannan shi ne wanda ido guda ɗaya yake kallon abinda ake buƙata, amma ɗayan yana kallon gefen kunci. Mutum mai wannan nau’in harara garken yakan yi fama da gani biyu-biyu, wahalar ganin rubutu, da zazzare idanu wajen kallon nesa. Yana iya kama mutum a kowane lokaci na rayuwarsa, kuma akan magance shi ta hanyar amfani da tabarau na likita.

    ABUBUWAN DA SUKE HADDASA HARARA GARKE (CAUSES OF STRABISMUS)

    Babban abinda yake haddasa harara garke shi ne lalacewar tsokoki masu sarrafa motsin ƙwayar ido, kamar yadda bayani ya gabata. Bayan shi, akwai wasu dalilai kamar haka:

    1. Gado (inheritance) daga wani a cikin zuriyya.

    2. Rashin ƙarfin gani (poor eye vision) saboda cututtukan ido.

    3. Ciwon laka na sahuhanci (down syndrome).

    4. Ciwon laka na rashin ƙarfin jiki (cerebral palsy).

    5. Cututtukan ƙwaƙwalwa (brain diseases).

    6. Shanyewar tsagin jiki (stroke) saboda hawan jini.

    7. Cututtukan laka (neurological disorders).

    8. Rashin daidaiton sinadarin thyroid (grave disease).

    LOKACIN DA AKE GANE HARARA GARKE (STAGE OF STRABISMUS DETECTION)

    Idanun jariri sabuwar haihuwa za a gansu kamar harara garke. Hakan yana faruwa ne saboda jijiyoyi da tsokokin idonsa ba su girma ba. Idan ya kai wata 3 zuwa 4, to za su gyaru kuma zai iya kallo kai-tsaye. A cikin watanni 6 zuwa shekara 1 zai ƙware sosai wajen kallo. Idan iyaye suka ga idanunsa ba su tsaya sosai ba wajen kallo, to, sai su tafi da shi asibiti domin a duba shi. Na faɗa da farko cewa harara garke zai iya kama mutum a shekarun yarinta kamar daga shekara 3 zuwa goma. Wani kuma sai ya balaga.

    MAGANCE HARARA GARKE (TREATMENT OF STRABISMUS)

    Magance harara garke ya danganta da tsananinsa da kuma abinda ya haddasa shi. Don haka, hanyoyin magance shi sun haɗa da:

    1. Amfani da tabarau mai ƙara girman abubuwa wanda likita ya bayar.

    2. Allurai, ƙwayyoyi, da magungunan ɗigawa wanda likita ya bayar.

    3. Aikin tiyata na tsokar ido mai matsala.

    4. Atisayen daidaita ganin ido wanda likita ya koyar.

    Rashin magance harara garke zai haifar da rashin gani da kyau, ciwon kai, zazzare idanu, gani biyu-biyu, da rashin ƙwarin gwiwar hulɗa da mutane.Allah ka kare mu da lafiya, amin.

    Don karanta Ƙaiƙayi Mai Kamar Tafiyar Kiyashi A Jikin Mutum danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Warin Gaban Mace Da Yake Nuna Matsala

    Warin Gaban Mace Da Yake Nuna Matsala

    1. Idan mace ta rinƙa jin gaban ta yana ɗoyin warin kifi, to wannan yana nuni da ƙananun ƙwayoyin halittar bacteria masu haɗari sun rinjayi masu amfanin dake gaban mace. Ƙarin alamu sun haɗa da fitar farin ruwa, jin zafi wajen yin fitsari da kuma ƙaiƙayi saman gaban mace. Awani ɓangaren kuma idan mace tana jin warin kifi ga gaban ta haɗe da fitar tsanwa ko ɗorowan ruwa jin zafin fitsari da kuma ƙaiƙayi to wannan yana nuna alamaun trochomoniasis cutar da ake ɗauka ta hanyar saduwa.

    2. Idan kuma mace najin wari a gabanta kamar ana gasa bread wanda ya ƙone haɗe da fitar wani abu ta gaba kamar dussa-dussar cukui da matsanancin ƙaiƙayi a cikin matunci da wajen matunci to wannan alamu ne da ke nuna akwai (YEAST INFECTION)

    3. Idan mace tana jin mugun ɗoyi wanda ke haɗe da zazzaɓi ,matsanancin ciwon mara da kuma jin zafi yayin saduwa to wannan alamu ne da ke nuni da mace na da PID.

    4. In wari kamar warin cukui wanda ba kasafai ake samun shi ba. Shi wannan yana da nasaba da kamar macen da ke da yeast infection ta haɗu da irin sinadaran da ake shafawa ga gaba kafin saduwa ko macen da ke trichomoniasis a saka condom wajen saduwa da ita.

    WARIN GABAN MACE DA ZAI IYA ZAMA BA MATSALA BA

    1. Wari kamar na ruɓaɓɓen abinci ga gaban mace in dai ba wasu alamun ƙaiƙayin , wari ƙarni ko ƙuraje Gaba, ko kumburin gaba, to wani lokaci ba matsala ba ne. Wannan yana da nasaba da macen da take barin panties ga jikin su na tsawon wuni lokaci ba a canza ba. Hakan na da nasaba da haɗuwar kamar tsohon jini, ƙwayoyin bacteria da aka halitta ga gaban mace don wani amfani da kuma cakuɗuwar su da ruwan da ke fita ga gaban mace ga panties ɗin ta.

    2. Jin wari kamar na man bleaching lokacin saduwa na da nasaba da abinda aka yi amfani da shi don taushi ga gaban mace lokacin saduwa ko kuma hanyar kariya kamar amfani da condom.

    3. Jin wari kamar na muski yana da nasaba da idan mace ta yi wani aiki mai yawa sai gabanta ya fitar da zufa mai wari kamar na muski.

    4. Jin wari kamar na wani abu mai zaƙi yana da nasaba da abubuwan da mace ke ci ko sha. Idan abubuwan da mace ke ci sun shafi ababe masu zaƙi to za ta rinƙa jin shi ga gabanta sakamakon zufar jiki. Shi yasa wasu matan ke yawan shan abarba da sauran fruits.

    Don karanta Zinariyar Awa Ga Jariranmu danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Mutuwar Mata Masu Jego

    Mutuwar Mata Masu Jego

    Duk mai jegon da bayan haihuwa ko da da kwana 1 ne ballantana a ce an kwana uku da haihuwa ta ji alamun zazzaɓi, ko ciwon kai, ko ciwon ƙirji da sauransu. Toh lallai ta sanar a hanzarta kai ta asibiti kar a kuskura! ina maimaitawa kar a kuskura! a ce ai ba komi ta sha paracetamol ko a ce za a nemo Maganin ulcer kurum a ba ta babu komi. Hakan tamkar tallafawa me ƙoƙarin kashe kai ne.

    Sau tari a yanzu akan zo taron suna me jego ba lafiya sosai, amma tai ta juriyar banza saboda cutar da kai, alhalin ƙwayoyin cuta sun sami hanya ta dalilin jinin nifasi da ke fita sun shiga cikin jijiyoyin jininta suna haifar matan da puerperal fever da zai kai ta ga “Puerperal sepsis” yai ta cinta a jika tana zaton abu ne da zai zo ya shige ƙarshe sai gawa.

    Galibi wannan shi ke kashe masu jego in kika cire batun zubar jini bayan haihuwa, musamman bayan kwana 3 da haihuwa zazzaɓin ya fi somawa domin incubation period ɗin kenan na ƙwayoyin cutar, shi yasa wata sai bayan an yi taron suna ana murna kurum a ji an wayi gari wance ta mutu, mutuwa me duka.

    Kada a taɓa ɗaukar hakan da wasa, ko baka da kuɗi ranto ka kai ta asibiti, matuƙar me jego tace ba ta lafiya ƙasa da kwana 40 da haihuwa kar ai wasa.

    Ku kuma ƙananun jami’an lafiya da ke bibiyar rubutuna kodayaushe ku sa wannan cikin kanku, kar me jego tace:-

    – Tanajin kasala,
    – Kanta na ciwo
    – Zazzaɓi
    – Fitar farin ruwa ko jini me ɗoyi
    – Ciwon Mara
    – Zafin fitsari
    – Ko har yau girman cikinta yana nan da sauransa kamar ba ta haihu ba ko kamar da sauran jariri a ciki

    Ku ce za ku ba ta maganin rage zugi kurum ku sallame ta, ko kuwa ku ce za ku yi gwajin Malaria don haka in ya nuna Negative sai dai ku ba ta pain reliever, ko kuma in aka yi kiciɓis ga Malaria positive ku ce iya Malaria ke damunta.

    Kuke buɗe tunaninku sosai for differentials diagnosis, kada a ce komai in ya haɗu da ciwon kai kurum Malaria ko Bp, ko Typhoid ne, duk macen da kuka ji ta yi muku ƙorafin ɗaya ko biyu daga waɗancan alamun na sama kai tsaye ku yi treating ɗinta for puerperal infection muddin me jego ce, domin hakan na da alaƙa da haihuwarta. Mai jego ita ce wadda ba ta wuce kwana 42 da haihuwa ba. Don haka ko da ta yi wata da haihuwa duk da haka tana cikin hatsari har na zubar jini.

    Ya rage naku ku je ku yi biyayya ga manyanku da kuke aiki ƙarƙashinsu, su ilmantar da ku magungunan da alluran da ake amfani da su wajen addressing din matsalar, don ba kowanne antibiotics ake ba su ba, in su ma ba su sani ba toh ku je sahihan journals na obstetrics and gynecology ku yi binkice ku ilmantar da kanku ba wai google ba. Wannan lamari ne da kan zamo Medical Emergency.

    Wannan tasa ko ɓari mace ta yi sai an ba ta magungunan antibiotics, haka ma bayan haihuwa domin riga-kafi koda ƙwayoyin cutar sun maƙale to zai magance su kafin su yi ƙarfin da za su shiga jini tunda ido bai iya ganinsu. AMMA wasu marasa tunanin cikin mata ba sa sha, ko in sun fara sai su bar sha tun kafin ya ƙare, toh masu irin wannan ku kuka da kanku, Domin ba zubar jini ne kurum abin tsoro ba bayan haihuwa.

    In muka kiyaye wannan za mu taimaka wajen rage wasu mace-macen na masu haihuwa.

    Allah yasa mu dace.

    Danna nan don karanta Rashin Kogon Al’aura Ga Mata

    Edita@rumasau-kallamu

  • Hatsarin Yin Wasa-rere Da Hawan Jini

    Hatsarin Yin Wasa-rere Da Hawan Jini

    Kamar yadda kwanaki kuka ji na yi bayani kan ciwon sugar cewa shi ne kan gaba wajen haddasa chronic kidney failure toh Hawan jini shi ne a matsayi na biyu da ke take masa baya wajen lalata ƙoda.

    Nephr(o)tic syndrome shi ne abinda ciwon suga ke jawo wa wanda nace muku in an yi gwajin fitsari ga wanda ƙodar ta fara taɓuwa za a ga sinadrin Protein ko Albumin a ciki ba ya ga hauhawar serum Creatinine da kumburi a ƙafafu ko ciki a wasu lokutan in ya yi ƙamari.

    To a masu Hawan jini kuma Nephr(i)tic Syndrome shi ke faruwa. Su kuma a fitsarin abinda ake gani shi ne jini wato cast na Red blood cell. Wani ƙila zai ce ai fitsarina koyaushe yellow ne ko kuwa fari tas don haka babu alamar jini. Ina ba haka abin yake ba.

    Akwai jinin da in abin ya yi ƙamari kai da kanka za ka ke ganin fitsarinka ya canza wannan shi muke kira GROSS HEMATURIA toh amma akwai wanda ba za ka taɓa gani ba sai an yi urinalysis, gwajin fitsari an sa High field microscope shi ne muke kira MICROSCOPIC HEMATURIA. To wannan fa shi ke nuna cewa hawan jini ya fara cin ƙodar mutum dole ne ya yi wani abu, in kuwa sai bayan abu ya ɓaci aka farga toh gaskiya in dai ya fara shiga Chronic sai dai a yi management ai ta ƙoƙari. Amma in yana Acute Kidney disease akan yi nasarar ƙwato ƙodar ta hanyar control na hawan jinin da sauran maganin da zai aiki a ƙodar da kuma canza abincin mutum zuwa KETO DIET

    Hawan jini abu ne mai hatsari idan aka yi sake da shi to fa ba ƙoda ba a hankali zai lalata ƙwaƙwalwa, yana motse jijiyoyin jini ta kai ga haddasa shanyewar ɓarin jiki, cutar mantuwa, lalata ido yadda mutum zai sami Retinopathy ya makance, da uwa uba bugun zuciya ko heart attack ko heart failure ko Coronary artery disease wanda duk sanda aka kai haka musamman zuciya, to fa mutum ba shi ba kuma yin duk wani aiki da ya saba sai dai a ƙiyama domin ya nakasa abin da yake jira shi ne mutuwa.

    Yawanci ciwon zuciyar ya fi faruwa bayan an ba shekaru 50 baya. To amma fa yanzu ga shi hawan jini da sai an ba shekara 40 baya aka fi samu amma yanzu har yara ƙanana masu ƙananun shekaru fama suke.

    ‘Yan Shekara 20 da wani abu ko ‘yan goma sha sai ka gan su da hawan jini. Wasu kuma basu ma san suna da shi ba har yau. Babbar illar hawan jini shi ne ba za ka taɓa jin alamun rashin daɗi a jika ko kana da shi alhalin cikin jikinka yana ta maka illa, shi yasa ake kiransa da silent killer.

    A sabon jadawalin da AMERICAN HEART ASSOCIATION ta fitar yanzu kafin tabbatar da hawan jini sai an auna mutum a lokuta 2 zuwa 3 mabambanta na rana guda idan har an sami Bp ɗinsa sama da 140 to tabbata yana da hawan jini. Wajibi a ɗora shi kan magani.

    Amma yawanci akwai wani abu da nake musamman ƙananun ma’aikatan lafiya su sani duk inda kuka ga mutum ɗan ƙasa da shekaru 10, ko 20 ko ƙasa da 30 ɗauke da hawan jini kai ko da ya ba wa 30 baya da kaɗan toh ku yi hanzarin tura shi ya yi KIDNEY FUNCTION TEST musamman a yara ‘yan goma sha yawanci ciwon ƙoda ne ke haddasa hawan jininsu.

    Da an je an yi gwajin fitsari da Blood chemistry za ka samu CREATININE ɗinsu ya yi High ana fara ba su magani insha Allahu shike nan za su sami lafiya, ciwon ƙodar zai kau sannan hawan jinin ma zai tafi dama ciwon ƙodar ne ya kawo shi. Wanda in kuwa ka fara ɗora mutum a maganin hawan jini to fa kullum a magani zai tafi alhalin an bar tushen matsalar ƙarshen complications ɗin ya kashe shi.

    Na faɗa muku da yawa ciwon ƙoda sai ya yi muni ake jin alamu. Sai dai a yara masu High Bp idan ƙodar ta taɓu wasu ana ganin kumburin fuska da ƙafafu kai tsaye.

    Akwai wani bawan Allah da ya rasu a Kano satin da ya wuce sakamakon ciwon ƙoda na ga labarinsa inda aka riƙa neman milyan 15 don kai shi India a yi masa dashe. A bayanin da ya yi farkon matsalar hawan jini ne tun a 2001 yace bai sani ba sai da aka duba jininsa lokaci har 220 ya je. Tuni ya ɓata ƙodar amma saboda in pressure ta yi pressure ƙwaƙwalwa ma daina kai saƙo take shi yasa wani za ka ga jininsa a 160 ko 180 amma yace shi ai ƙalau yake jinsa ba abin da yake damunsa.

    Shi ma ɗin to zuwa 2006 shekara 5 kaɗai duk ƙodojinsa biyun suka kasa, a nan ne ya samu aka masa dashen ƙoda ɗaya, aka cire ɗayar Allah sarki zuwa 2010 shekara 4 kacal saboda na faɗa muku in aka sama Organ ɗin wani ba kurum sawar ba akwai Rikicin Rejection da garkuwar jikinka za take yaƙar organ ɗin toh shi ma ya sami CHRONIC REJECTION shekaru huɗu ƙodar da aka sama ta mutu, shi ne fa yake ta fama har zuwa yanzu da Allah ya karɓi ransa.

    Yace daga wannan lokaci zuwa sanda yake kwance yana neman taimako an masa wankin ƙoda sama da sau dubu ɗaya da ɗari huɗu da sabain da uku, inalillahi wa’inna ilayhir rajiun. Ya sha wahala ban da ciwon cancer na ƙoda da za ka iya haɗuwa da shi a sakamakon dialysis ɗin kanshi tare da ƙarancin jini.

    Don haka kuskuren da ƙananun ma’aikatan lafiya kuke ku gyara, kukan rubutawa me hawan jini maganin sha na kwana 10 ya tafi kurum shikenan ko ya aka duba aka ga jini ya yo kasa, ba kwa kuma faɗawa mutum me ya dace ya yi ko ya kiyaye. To ku sani da maganin ciwon sugar da na hawan jini shan su ba ya ƙarewa har ƙarshen rayuwa kullum ne kuma ko da jini ya dawo normal level in dai ba ƙasa da 90 aka ga ya tafi ba, ba za a taɓa cewa ka ɗaga ƙafa ba. Sannan wajibi ne kafin ka ba mutum kowanne irin maganin hawan jini ya zamto kana da masaniya a kai da side effect, dose ɗin da ya dace da kuma HALF LIFE na maganin wannan wajibi ne.

    Wani combination wani kuma magani ɗaya ne. Don haka a ƙalla ka rubutawa mutum maganin wata 3 wato kwana 90 in ya kare a kuma ƙara masa haka za a yi ta tafiya, kuma za a ci gaba da bibiyarsa, shi yasa muke cewa a sayi abin gwajin mutum ya riƙa recording a littafi duk sanda zai zo asibiti ya zo muna da shi muke ganin progress ɗin.

    Don haka kar ku yi sake da hawan jini ku kiyayi gishiri; yawancin maiƙo da su chocolates. Kar don kuna shan magani ku ɗauka za ku ci komai musamman mu baƙaƙen fata da hawan jinin mu bai fiye jin magani ba sai an yi da gaske abu kaɗan na sa shi ya hau.

    Idan ka kula da kanka za ka rayu cikin aminci kamar kowa kuma hawan jini ba zai ma illar can ba. In ko kai wasa toh sai dai Allah ya tsare. Allah ka yaye mana abinda ya dame mu amin.

    Domin karanta Hawan Jini Ga Mace Mai Juna Biyu danna nan

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Shawara Ga Masu Ciwon Suga

    Shawara Ga Masu Ciwon Suga

    Mutane masu larurar ciwon siga ku daure kullum musamman wajen alwalar safe ko la’asar kuke tsayawa ku lura da tafukan ƙafarku da tsakanin yatsu da kyau, saboda 60% kukan iya yin rauni ba tare da kun ji zafi ba ballantana ku sani, wanda a ƙarshe in aka yi rashin sa’a ƙwayoyin cutar da ke kan fata ko sarari, tsakar gida ko kan titi inda muke takawa suka sami damar hawa kan ciwom sai abu ƙarami ya zamto babba har ya yi muni.

    Da yawa ta inda matsalar gyambon ƙafa ke somuwa kenan a gareku, wanda ƙarshe sai an kai ga yanke kafa, A ƙalla duk awa 1 sai an yanke ƙafa dalilin ciwon suga, kimanin ƙafafu 24 ake cire wa a kullum cikin faɗin duniya.

    Don haka, muddin ka ga rauni a ƙafarka matsayinka na mai ciwon sugar, to ka hanzarta zuwa a duba a wanke a baka magani, kar ka kuskura ka ce ai zai warke da kansa tunda ba shi da girma.

    Haka nan wasu kan yi kuskuren cewa ai cin ruwa ne alhalin diabetic neuropathy ne don haka a lura da ƙafa, a lura da glucose control, Diabetes is not a joke. Banda yawo ba takalmi ko safa koda kuwa a tsakar gida ne, ake shafawa kafa mai sosai take santsi. Da an ji alamun ta fara yin dundurus, ko ba ta bari a iya bacci in dare ya yi to a nemi ɗaukin likita. A kuma dinga yanke farce koyaushe.

    Sannan a dinga rufe ido ana sa tsinken tsintsiya lokaci lokaci ana duddungurar tafin kafar musamman pressure points. ko kuma mutum ya rufe ido ya sa wani ya yi masa, ana jin cewa ba a jin sensation na taɓin ko kuwa in a taɓa mutum ba ya iya guessing yace guri kaza ne tunda idonsa rufe yake, to akwai buƙatar a je ga likita lallai kar a yi wasa, ba sai an jira an ga rauni ba.

    Allah shi taƙaitamana wahala, ya bai wa kowa lafiya.

    Domin karanta Ciwon Suga danna nan

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Yanayin Damuwa (Depression)

    Yanayin Damuwa (Depression)

    Depression dai wani yanayi ne marar daɗi da mutum ke tsintar kanshi bayan wani abu marar kyau ya faru da shi, ko kuma haka kawai mutum ya tsinci kanshi cikin wani yanayi na rashin jin daɗin komai kuma ba ya sha’awar komai da kowa, wanda zai sa mutum ya riƙa tunanin ina ma ya mutu ya huta. Wani lokacin kuma mutum ya kasa bacci, aiki, cin abinci, kula da iyali, kula da jiki da sauran su.

    Depression shi ne a kan gaba wajen saka mutane su hallaka kansu da kansu, ko ta hanyar rataya ko shan guba ko cakawa kai wuƙa ko faɗawa ruwa.

    Wannan depression ɗin yana ɗaya daga cikin manyan matsalolin ƙwaƙwalwa ko in ce “PSYCHIATRIC EMERGENCY”.

    A duniya baki ɗaya a ƙalla mutum (miliyan 264) ke fama da depression kuma daga cikin su kashi 87% cikin ɗari mata ne ‘yan shekara 15 zuwa shekara 40. Ya danganta daga tsawon lokacin da mutum ke yi yayin da yake cikin damuwar kamar SHORT TIME (kwana ɗaya zuwa kwana uku) ko kuma LONG TIME (kwana 3 zuwa sati biyu har abin da ya fi haka)

    DEPRESSION YA KASU KASHI KASHI KANSHI, AKWAI:

    1. Endogenous_depression: Wato mutum zai tsinci kanshi cikin yanayi marar daɗi ba tare da dalilin komai ba, wannan ya samo asali ne daga:
    ✍Gado daga uwa (mafiyawa)
    ✍Rashin lafiyar ƙwaƙwalwa ko taɓuwar ƙwaƙwalwa
    ✍Rashin isasshen bacci
    ✍Wata rashin lafiya da ke damun hormones da sauran jiki

    2. Exogenous_depression ko kuma REACTIVE DEPRESSION: Wato idan wani abu ya faru da mutum na yau da kullum kamar:
    ✍Mutuwar miji ko mata/uba ko uwa
    ✍Sakin aure/ ƙara aure/kishiya
    ✍Rasa aiki/kora daga aiki
    ✍Wani bala’i na rayuwa
    ✍Faɗa ko rashin jituwa tsakanin ‘yan uwa, miji, mata, iyaye, dangin miji, dangin uwa ko uba da sauran su
    ✍Faɗuwa jarrabawa
    ✍Asarar dukiya ko faɗuwa takarar siyasa
    ✍Kamuwa da ciwo kamar HIV ko diabetes
    ✍Fyaɗe
    ✍Bayan haihuwa (peupherial blues)

    Waɗannan su ne kashe-kashen depression da muke da su. Amma wani lokacin ba koyaushe depression ɗin ke kasancewa ga mutum ba, yakan iya zowa mutum kamar haka:

    Biopolar: Da safe kana cikin damuwa amma da maraice ka kasance cikin farin ciki kamar ba kai ba.

    Unipolar: Ko ka kasance cikin baƙin ciki koyaushe ko kuma ka kasance kana cikin baƙin ciki amma komai kana iya yi ba ka gajiya.

    ALAMOMIN DEPRESSION

    Alamomin shi suna zuwa ta fuska biyu Wato, yanda mai depression ɗin ke ji a jikin shi:

    • Tsananin baƙin ciki da damuwa,
    • Mummunan tunani,
    • Tunanin mutuwa,
    • Mutum ya ji ba shi da amfani
    • Tunanin ba mai sonka
    • Jin haushin kowa da komai

    Don karanta Amfanin Aya Wajen Samar Lafiya A Jiki danna nan

    Alamar da mutane za su gane cewa wannan mutum yana cikin depression

    • Ramewa
    • Gumi (zufa)
    • Turowar idanuwa
    • Rashin bacci
    • Rashin cin abinci
    • Bugawar zuciya da ƙarfi
    • Hawan jini
    • Kaɗaita cikin ɗaki ko gida
    • Rashin son magana da kowa
    • Fushi
    • Rashin kula da kai kamar wanka
    • Kuka dare da rana

    MATAKIN DA YA KAMATA A ƊAUKA IDAN AN GA MUTUM CIKIN YANAYIN DEPRESSION /MATAKIN DA YAKAMATA KA ƊAUKAR WA KANKA

    1- Psychological care: Babban abu na farko da mai depression ke buƙata shi ne shawarwari masu kyau a kan yanayin da ya tsinci kanshi.

    • Kada ka danmu da kanka a kan abin da dole sai ya faru ga ɗan Adam kamar:
      -Mutuwa, mutuwar ɗan uwa da sauran su
      -Kishiya ko sakin aure
      -Kora ko rasa aiki
      -Asarar dukiya da sauran su

    Mutane da dama kullum sai sun fuskanci wannan matsalar kuma ba za a daina ba har duniyar ta ƙare, to don haka kada ki damu kanki a kan abin da ba za ki iya canjawa ba idan ya faru. Idan ke kaɗai ce ga mijin ki yace zai ƙara aure kada ki damu, 4 Allah yace ya yi kin ga ko yanzu akwai 2 zuwa. To meye na damun kai?

    Ya sani cewa rayuwar duniya ba komai kake so za ka samu ba, ko kuma ko me ka samu mai yiwuwa ne ya kuɓuce ma musamman idan ba rabon ki ba ne kuma idan mutuwa ce, to tabbas dole ce a kan kowa.

    Ki nemi amintacciyar ƙawa ki gaya mata matsalolin ki kada ki bar damuwa a cikin zuciyar ki, idan ba ki da ita, ki nemi ‘yan uwa ko wani wanda kika fi jin sanyi a wurin shi koda addu’a aka yi miki za ki ji sanyi sosai. Idan kuma babu, ki nemi ƙwararru a wannan ɓangaren wato GUIDANCE AND COUNCELING SERVICES insha Allah za a dace.

    • Yan uwa kuma ku saka mai damuwa a jiki kada ku bar shi ya kai ga hallaka kanshi ko ya kai shi ga wani ciwo daban
    • Kada mutum ya zauna shi kaɗai, ya riƙa shiga mutane da abokai ana hira, idan ma babu hali, ki/ka nemi masu irin matsalar ka ku zauna tare ku riƙa samun nishaɗi.

    2- Rehabilitation and care:

    • Idan aiki ne mutum ya rasa ko wani abu, ya nemi wani abun wanda ko bai kai ga wancan ba ya yi haƙuri da shi, rayuwar duniya ta ɗan lokaci ce, ba dole ne sai an sami abin da ake so ba 100%
    • ‘Yan uwa da abokai, ku kula da mai depression iya gwargwado kada ku watsar da mutum, sannna ku tabbata babu wuƙa ko kwalba ko wani mummunan abu kusa da shi ko ɗakin shi wanda aka san zai iya hallaka kanshi da shi. Ku sani, ba yin kanshi ba ne duk abin da ya yi.

    3- Spiritual care: Dukkan mu musulmi mun yadda da Allah kuma mun yarda da ƙaddara, a nunawa mutum cewa komai ya gani daga Allah ne, kuma jarrabawa ce, mai yuwa ne ta yi masa sanadin shiga aljanna.

    4- Diversion: Ka yi wa kanka maganin depression da abin da ka san ya fi faranta maka rayuwa kamar rawa da waƙa, sauraren music ko ƙuran, karatun littafan na nishaɗi ko soyayya, kallon films ko drama ko games da sauran su. Duniyar mai ƙarewa ce, don haka NO NEED TO WORRY ABOUT ANYTHING. An haife ka ba ka da komai, kuma ba za ka koma da komai ba, to meye don ka rasa wani abun?

    5- Drugs: Idan abun ya gagara, ana bai wa mutum magungunan da ke sa bacci, tabbas suna rage depression kuma suna sa mutum bacci, amma kada mutum ya dogara da magani, ya yi ƙoƙari ya fahimci rayuwar duniya kuma ya yi ƙoƙarin ƙauracewa wannna abin da ke sa shi damuwa, saboda maganin zai iya zame ma mutum addiction ko maganin ya daina aiki.

    Abu na ƙarshe: Ba kowacce damuwa ce depression ba, rayuwa dama an yi ta da farin ciki da baƙin ciki, don haka mu lura, damuwa idan an ɓata ma rai ko ka yi asarar abu ta ɗan lokaci ba matsala ba ce, matsala ita ce idan waɗancan alamomin da na lissafa sun faru da mutum.

    Domin karanta Cutar Damuwa danna nan 

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Cikin Molo (Molar Pregnancy)

    Cikin Molo (Molar Pregnancy)

    Cikin Molo wani nau’in alamun juna biyu ne da wasu cikin mata kan samu kansu da shi wanda kuma a zahiri gaskiya ba ciki ne na haihuwa ba kamar yadda suke tsammani duk da abun ya tattara dukkan alamomin samuwar ciki na zahiri.

    Bisa ƙididdiga a dukkan mata dubu “1000” masu ciki akan sami guda ɗaya “1” ya zamto cikin molo ko cikin ƙarya, wanda 999 su ne ke ɗauke da ciki me ƙunshe da jariri. Viable Pregancy.

    SHIN YA CIKIN YAKE, ME KE JAWO SHI KUMA ?

    Wani cikin ne da ke faruwa sakamakon tangarɗar ƙwan haihuwa wanda wata ƙwayar halitta da ake kira TROPHOBLAST a turance da aikinta samarwa da jariri sinadaran abinci da rayuwa a cikin mahaifa kan rikiɗe ta hau girma a karan kanta ya zamto ta yi girman da ya mamaye cikin mahaifa ta samar da ƙaton tsiro me ƙunshe da ruwa ko tsauri WATO cysts ko TUMOR sakamakon waɗancan ƙwayayen haihuwa marasa rai ko inganci da suka shigo cikin mahaifar mace daga kututar ƙwayaye wato OVARY.

    Wanda wannan yasa a farkon samuwar abun duk wani alamu na ciki mace za ta ji ta fara fuskantarsa kama daga tashin zuciya, zazzaɓi ba me tsanani ba, rashin son warin abu, zubar da miyau, kasala da sauransu. Wani abu ma da za ta yi gwajin ciki na fitsari ko jini kai tsaye za ta ga ya nuna POSITIVE alamun ta samu ciki saboda HcG ɗin is High.

    Kuma zai cigaba da girma kamar yadda ciki ke girma a hankali har a ga tasowar cikin. Shi yasa da yawa in aka ce musu ba ciki ba ne ba sa yadda. Wasu sai a yi ta fama da su su ƙi, har su riƙa kiransa da kwantacce a lokacin da suka ga girman ya dakata. Ko kuma lokacin watannin haihuwa ya zo ya wuce har sun ƙara shekara sai ka ji ana kwantaccen ciki.

    SHIN DUK IRI GUDA NE KO YA RARRABU ?

    Ya kasu rukuni biyu ne kacal; akwai COMPLETE wato me gaba ɗaya, da kuma INCOMPLETE me ragayya.

    RUKUNI NA FARKO [COMPLETE]

    A irin wannan ainihin shimfiɗar cikin mahaifa wato (uterus layer) inda jariri ke kwanciya ciki ya zauna ita kanta shimfiɗar takan rasa ingancinta ma’ana takan tattare ta murmuɗe ta yi tudu da ƙwari, domin daga cikin ƙwayoyin halittun gado chromosomes 46 da Maxa suke saki wato 23 daga mace, 23 wanda ke ba da total na 46.

    Akan samu Chromosome ɗin mace ne kurum zai iya zamowa jariri wato viable egg. Shi MIJIN empty sperm cell ya saki. WANDA tunda kuwa sai da ƙwan namiji ciki zai tabbata amma ga shi sai mace ce ke da normal egg toh irin wannan ke sa zubin shimfiɗar mahaifar ya jirkice shi kuma wancan tumor ɗin na trophoblast sai ya yi amfani da wannan viable egg na macen ya girma ya cika cikin mahaifar mace (uterus). A riƙa ganin kamar ciki gareta. kuma ko yaushe in an duba HCG za a ga high kamar dai mai ciki, yadda dai kuka ji na faɗa a baya.

    RUKUNI NA BIYU [PARTIAL]

    A partial shi kuma cikin 23 pairs ɗin na chromosome MACE tana sakin normal egg tare da 1 pair na chromosome, shi kuma NAMIJIN sai ya saki 2 pairs na chromosome maimakon 1 wato shi kaɗai ya samar da 46pairs maimakon 23pairs wanda in ka haɗa da 23pairs ɗin na matar sun tashi 69 pairs maimakon a sami total na 46.

    Hakan shi ke sa ga cikin ya shiga akwai ciki na gaske ba tumor ba toh amma fa ba zai ta6a rayuwa ya zama cikakken jariri ba, kuma a daidai wannan lokacin ga growth ɗin trophoblast ɗin da ya kusa cika mahaifar mace, don haka nan ma za a yi ta ganin HCG high amma fa ba zai taɓa zama ciki ba.

    Sai dai a PARTIAL ɗin akwai kuma Partial me Normal Karyotype wato chromosome ɗin daidai ne kowa ya samar da 23 ana da total 46 amma kuma ga trophoblast ya samar da tumor kusa da jaririn. To a irin wannan ne yakan girma ya zama ciki a haifi jariri koda kuwa bai da cikakkiyar lafiya.

    A irin wannan ne ake jin hausawa na cewa kwantaccen wance dai ya tashi, duk da cikin kan shafe shekaru. Amma gaskiya ba a cika samun irin wannan ɗin sosai ba, sai dai dama irin wannan tun a ultrasound ake iya bambance shi.

    Domin karanta Cutar Maƙoƙo dannan nan

    ME KE JAWO HAKAN LIKITA ?

    Abubuwan da kan jawo haka sun ƙunshi;

    1. Akwai shekaru musamman macen da ke kusa ko kuma ta haura shekaru 35

    2. Kasancewar mace ta taɓa samun hakan a baya, akwai yiwuwar ƙara maimaitawa

    3. Sai rashin daidaiton sinadaran halitta (hormonal imbalance)

    Wannan matsala musamman a me COMPLETE MOLAR likitoci kan kalle ta a matsayin ɗaya daga cikin cuttukan cancer na mahaifa wato choriocarcinoma. Duk abin da ke iya ƙara girma a karan kansa tabbas ko dai ya zamo cancer ko kuma benign tumor wato wanda ba cancer ba amma in aka bar shi zai iya zama cancer.

    Domin idan har bayan an cire cyst ɗin kuma HCG ya cigaba da tsayawa High akwai zargin ya riga ya zama cancer dole a ɗora mace a kan CHEMOTHERAPY, kuma ana warkar da cancer ɗin cikin ikon Allah in an farga da wuri.

    Idan kuwa aka bar shi to ka san cancer tana iya yaɗuwa zuwa wasu sassan kuma hakan ce za ta faru wanda a ƙarshe mace za ta iya mutuwa a dalilin cancer hanta ko huhu ko hanji alhalin tushen ciwon a mahaifa ne. Wannan tasa da zarar likita yace miki cikin MOLO ne to kar ki ɓata lokaci kurum a cire shi.

    ALAMOMIN CIKIN MOLO

    Alamomin sun ƙunshi;
    Ganin Fitar jini me duhu ta gaba
    Ciwon baya ko mara
    Ganin jini na fita kamar dunƙulen grapes fruits da kuma
    Matsanancin tashin zuciya da amai.

    WAƊANNE GWAJE-GWAJE AKE YI

    Akan yi gwajin jini domin duba hemoglobin level saboda tunanin ƙarancin jini, sannan a kuma duba HCG wato hormone ɗin juna biyu da kuma ultrasound scan.

    MATAKIN ƊAUKA

    1. Kai tsaye bayan tabbatar da molar pregnancy ne abin da ake kira Dayilteshin & kyuritaj wato manuwal bakyum Asfireshan SHI NE abin yi, a cire tissue ɗin baki ɗaya, domin barinsa ba zai taɓa zama jariri ba, dama ba ciki ba ne kuma ko da partial ne wanda ke ƙunshe da ciki shi ma ba girma zai ba.

    Bayan kuma an cire ɗin ba a kuma barin mace ta ɗauki ciki, a ƙalla sai bayan shekara. Saboda ana so a cigaba da auna HCG level ɗin lokaci lokaci har zuwa shekara bayan cire molar ɗin domin idan ya cigaba da zama HIGH kamar de akwai ciki to alama ce ta PERSISTENT GESTATIONAL TROPHOBLASTIC NEOPLASIA wato ya tabbata cancer. Don haka dole a yi maza a fara mata chemotherapy a kashe shi, in ba haka ba za ta yaɗu zuwa sauran organs, kunga ko hakan is deadly.

    2. Ko kuma idan dama mace ba ta da sha’awar ƙara haihuwa tana jin ta gama shi kenan sai a cire mahaifar baki ɗaya kurum. Duk da nan gaba kuma lokacin menopause in estrogen ɗinta ya yi low wasu suna samun hot flashes wato premenopausal symptoms wanda ake musu hormone replacement therapy to amma fa macen da ba ta da mahaifa ita ba za a yi mata wannan ba, domin zai zame mata matsala tunda ya ƙunshi estrogen alhalin ba ta da uterus. Progesterone only method shi ne therapy ɗin da za ta iya amfani da shi.

    Don haka ake son ko yaushe in likita ya tambayi mace wani abu to ba ɓoye-ɓoye ko da dangane da mu’amalar auratayya ne ta faɗa masa gaskiya ba a yi wa likita ƙarya ko da kuwa kina yi wa mijinki shi likita in aka yi masa ƙarya kanki kika cuta.

    Wannan shi ne molar pregnancy a taƙaice.

    Danna nan don karnta Saiƙo Ko Sanƙo

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Cututtukan Haƙori

    Cututtukan Haƙori

    Cututtukan haƙori su ne matsalolin da suke kama haƙorin mutum, su haifar masa da ciwon haƙori, ko faɗuwar haƙori, ko rashin tsarin haƙori mai kyau. Cututtukan haƙori sun rabu gida biyu:

    a. Waɗanda suke samun haƙori sakamakon rashin tsabtar baki (poor oral hygiene) ko ɗabi’un mutum (lifestyle).

    b. Waɗanda suke samun haƙori sakamakon gado (genetic factors).

    CUTUTTUKAN HAƘORI NA RASHIN TSABTA (ORAL HYGIENE TOOTH DISEASES)

    Kaɗan daga cikinsu su ne:

    1. Lalacewar haƙori (tooth decay): shi ne mafi zama gama-gari a cikin mutane, wanda yake faruwa sakamakon taruwar ƙwayoyin halittar bacteria (streptococcus mutans) a jikin haƙori. Yana kawo rami ko kogo a jikin haƙori (tooth cavity). Abubuwan da suke kawo lalacewar haƙori su ne:

    • Yawan ci ko shan kayan zaƙi (consumption of sugary foods),
    • Yawan ci ko shan abubuwa masu danƙo (consumption of starchy foods),
    • Rashin tsabtar baki (poor oral hygiene),
    • Bushewar baki (mouth dryness),
    • Taruwar sinadarin acid a cikin baki (mouth acid buildup).

    Alamunsa (symptoms) su ne:

    • Ciwon haƙori (tooth ache),
    • rashin daɗin baki idan abubuwa masu zafi ko sanyi suka shiga cikin baki (sensitivity to hot or cold substances),
    • samuwar kogo a jikin haƙori (tooth cavity).

    Likita zai iya tabbatar da lalacewar haƙori ne (diagnosis) ta hanyar ɗaukar hoton haƙori (tooth x-ray) ko kuma duba haƙorin maras lafiya (visual examination). Rashin magance lalacewar haƙori bayan an tabbatar da shi zai iya haifar da munanan matsalolin baki, kamar taruwar gunya a cikin baki (mouth abscess) ko faɗuwar haƙori (tooth loss).

    Hanyoyin magance lalacewar haƙori su ne:

    • Yin cikon kogon haƙori (tooth cavity filling),
    • Buɗe jijiyoyin jini na haƙori (tooth root canal therapy),
    • Da cire haƙori (tooth extraction).

    2. Ciwon dasashi (gum disease): Shi ne kumburin dasashi, da kuma shigar ƙwayoyin cuta a cikin dasashi (gum inflammation and infection).

    Abubuwan da suke haddasa shi su ne:

    • Rashin tsabtar baki (poor oral hygiene),
    • Shan taba (cigarettes smoking),
    • Sauye-sauyen zubar ruwan sinadarai (hormonal changes),
    • Da laulayin magunguna (medication side effects).

    Alamunsa sun haɗa da:

    • Kumburin dasashi (gum inflammation),
    • Canzawar launin dasashi zuwa ja-zur (gum redness),
    • Warin baki (bad breath),
    • Faɗuwar haƙori (tooth loss),
    • Da jin zafi a lokacin tauna abinci (pain while chewing).
    • Likita zai iya tabbatar da kamuwa da ciwon dasashi ne ta hanyar yin hoton dasashi (gum x-ray) ko duba dasashi (gum examination).

    Rashin magance ciwon dasashi, bayan an tabbatar dashi, zai iya kawo faɗuwar haƙori (tooth loss) da lalacewar ƙashin muƙa-muƙi (jaw bone damage).

    Ana iya magance ciwon dasashi ne ta hanyar:

    • Wanke haƙori (teeth scaling),
    • Aikin tiyata (surgery),
    • Wanke jijiyoyin haƙori (tooth root planning),
    • Da yin amfani da magungunan antibiotics.

    Don karanta Hawan Jini  danna nan

    3. Rashin jin daɗin hakori (tooth sensitivity): yana faruwa ne sakamakon zaizayewar jikin haƙori (enamel wears) wanda yake sanya bayyanar shinfiɗar da take ƙarƙashin haƙori mai suna “dentin layer”.

    Abubuwan da suke kawo rashin jin daɗin hakori su ne:

    • Kogon hakori (tooth cavity),
    • Ciwon dasashi (gum disease),
    • Wanke baki da brush mai karfi (use of hard tooth brush),
    • Ci ko shan abubuwa masu acid (acidic foods consumption).

    Alamunsa su ne:

    Rashin jin daɗi ko zafin haƙori (tooth sensitivity) idan aka ci ko sha abubuwa masu zafi, ko sanyi, ko zaƙi, ko ɗaci, ko gishiri.

    Likita zai iya tabbatar da kamuwa da rashin daɗin haƙori ne ta hanyar duba haƙori, ko yi wa maras lafiya tambayoyi.

    Idan aka tabbatar da kamuwa da rashin jin daɗin haƙori, amma ba a magance shi ba, to, zai haifar da takura da rashin jin daɗin kowane irin abinci.

    Ana iya magance shi ta hanyar:

    • Yin amfani da mayukan goge baki masu ƙarfin sinadarai (desensitizing toothpaste),
    • Toshe zaizayewar da hakorin ya yi (dental bonding),
    • Ɗora maras lafiya a kan magungunan da za su ƙara masa yawan sinadarin fluoride a cikin jiki (fluoride treatment).

    4. Cutar daji ta baki (oral cancer): Tana kama tsokokin baki ne, kamar harshe (tongue), ko leɓe (lip) ko dasashi (gum), ko kumatu (cheeks). Tana sanya waɗannan halittun su kumbura suntum.

    Abubuwan da suke haddasa ta su ne:

    • Shan giya (alcoholism)
    • da kamuwa da ƙwayoyin cutar human papilloma virus (HPV).

    Alamunsa su ne:

    • Samun ishashen rauni a cikin baki wanda zai ƙi warkewa (persistent mouth ulcers),
    • Zubar jini (gum bleeding),
    • Jin zafi mai naci a cikin baki (persistent mouth pains),
    • Wahalar hadiyar abinci (swallowing difficulty),
    • Wahalar yin magana (talking difficulty),
    • Ɗaukewar ji idan aka taɓa fatar baki (numbness).

    Likita zai iya tabbatar da kamuwa da cutar ne ta hanyar duba baki (mouth examination) ko ɗibar samfurin cutar domin yin awo a ɗakin binciken kimiyya (biopsy test). Jinkirin warkar da cutar bayan an tabbatar da ita zai iya haddasa mutuwar mutum.

    Ana iya magance cancer baki ne ta hanyar yin aikin tiyatar (surgery), ko amfani da hasken na’urar computer (radiation therapy), ko ɗora maras lafiya akan magunguna masu ƙarfin gaske (chemotherapy).

    MATSALOLIN HAƘORA NA GADO DA NA TSARIN RAYUWA (CONGENITAL AND ACQUIRED TEETH DEFECTS)

    Kaɗan daga cikinsu su ne:

    1. Rashin daidaiton hakora (teeth misalignment): Ana kiransa “malocclusion” a likitance ko “gantso” a Hausa., Yana haifar da rashin tauna abinci da kyau (biting/chewing problems).

    Abubuwan da suke haddasa shi su ne:

    • Gado (genetic factors),
    • Ko tsotson ɗan-yatsa (thumb sucking),
    • Ko hura iska a cikin bakin mutum (mouth breathing) sakamakon ya kasa yin numfashi da kansa,
    • Ko yin amfani da kayan tsotso ga yaro (child use of pacifiers).

    Alamunsa su ne:

    • Rashin iya gutsura ko tauna abinci yadda ya kamata (bite or chewing problems),
    • Da samun wahalar yin magana (speech difficulties).

    Likita zai iya tabbatar da matsalar ne ta hanyar ɗaukar hoton haƙora (dental x-ray) ko duba baki (dental examination).

    Jinkirin magance matsalar, bayan tabbatar da ita, yana taɓa kwarjinin mutum (self-esteem).

    Ana iya magance ta ta hanyar:

    • Yin aikin tiyata (surgery),
    • Ɗaure haƙora da zaren daidaita su (use of teeth braces),
    • Sanyawa haƙora hular daidaita su (use of teeth aligners).

    2. Duhun launin haƙora (teeth discoloration): Yana haifar da dafewar haƙora (teeth staining).

    Abubuwan da suke haddasa shi su ne:

    • Shan taba (cigarettes smoking),
    • Tsufa (ageing),
    • Ci ko shan abubuwan da aka rina su da chemicals (consumption of foods prepared with coloring matters),
    • Rashin tsabtar baki (poor oral hygiene).

    Alamarsa ita ce dafewar haƙora. Likita zai iya tabbatar da shi ne ta hanyar duba haƙora. Daɗewa ba a magance shi ba, yana iya taɓa kwarjinin mutum.

    Ana iya magance shi ta hanyar amfani da hular haskaka haƙora (teeth veneers).

    3. Rashin fitowar wasu daga cikin hakora kwata-kwata (congenital teeth missing): Ana kiransa “hypodentia” a likitance.

    Abubuwan da suke haddasa shi su ne:

    • Gado (genetic factors),
    • Da kuma matsalolin rashin lafiya kamar ectodermal dysplasia, cleft lip, da cleft palate.

    Alamarsa ita ce rashin fitowar wasu daga cikin haƙora. Likita zai iya tabbatar da matsalar ne ta hanyar ɗaukar hoto, da kuma duba bakin mutum. Daɗewa ba a magance shi ba zai iya taɓa kwarjinin mutum, da kuma rashin iya cin abinci yadda ya kamata.

    Ana magance matsalar ne ta hanyar:

    • Yin dashen haƙora (dental implants),
    • Ko yin haƙoran roba (dentures),
    • Ko makala haƙoran roba na din-din-din (dental bridge)

    Danna nan don karanta Warin Baki

    Edita: @rumasau-kallamu

     

  • Cutar Maƙoƙo

    Cutar Maƙoƙo

    Maƙoƙo shi ne ake kira “goiter” ko “thyromegaly” a likitance. Maƙoƙo wani kumburi ne a cikin jakar sinadarin din thyroid (thyroid gland inflammation) wanda yake kasancewa a ƙasan wuya. Ba lallai ba ne maƙoƙo ya zamo ciwon daji, amma yana iya zamowa alamar matsalar jakar sinadarin thyroid.

    Abubuwan da suke iya haifar da maƙoƙo su ne:

    1. Ƙarancin sinadarin iodin a cikin jiki (iodine deficiency): Wannan shi ne mafi yawan dalilin samuwar maƙoƙo a faɗin duniya. Iodin yana da matuƙar muhimmanci wajen samar da sinadarin iodine na thyroid, kuma rashin shi zai iya sanya jakar thyroid ta kumbura don ƙoƙarin cike wannan giɓin.

    2. Graves’ Disease: Wannan cuta ce ta garkuwar jiki (autoimmune disorders) wacce take sanya jakar thyroid ta samar da sinadarin iodine fiye da kima (hyperthyroidism), kuma hakan yana haifar da kumburin maƙoƙo.

    3. Hashimoto’s Thyroiditis: Wannan ita ma wata cuta ce ta garkuwar jiki (autoimmune disorder) inda garkuwar jiki take kai hari ga jakar sinadarin thyroid, kuma hakan yana sanya ta kasa samar da sinadarin iodine yadda ake buƙata (hypothyroidism). Wannan yana iya haifar da kumburin maƙoƙo.

    4. Tsirowar Kari a Cikin Jakar Thyroid (Thyroid Nodules): Wannan wani kumburi ko ƙurji ne da yake fitowa a cikin jakar sinadarin thyroid, wanda yake haifar da kumburin maƙoƙo.

    5. Ciwon Daji na Thyroid (Thyroid Cancer): Ko da yake ba ya faruwa sosai, amma ciwon cancer yana iya haifar da kumburin jakar thyroid idan ya shafi tsarin halittar jakar.

    6. Juna Biyu (Pregnancy): Canje-canjen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone da sauransu, yayin da mace ta ɗauki ciki, yana iya haifar mata da kumburin maƙoƙo na wucin-gadi (temporary goiter) saboda jikinta yana buƙatar ƙaruwar sinadarin thyroid.

    7. Kumburi (Inflammation): kumburin jakar sinadarin thyroid (thyroiditis) yana iya haifar da kumburin maƙoƙo.

    Za a iya magance kumburin maƙoƙo ta hanyoyi kamar haka:

    1. Ƙarin Iodin (Iodine Supplementation): Idan ya samo asali ne daga rashin isasshen iodin a cikin jiki, to, ƙara yawan cin abincin da yake ɗauke da iodin ko shan magungunan ƙarin iodin yana iya rage kumburin.

    2. Yin Amfani Da Magunguna (Medications): Idan maƙoƙo ya samo asali ne daga ƙarancin sinadarin thyroid (hypothyroidism), to, shan maganin ƙarin sinadarin thyroid, kamar levothyroxine zai iya rage kumburin. Idan kuwa maƙoƙon ya samo asali ne daga yawan sinadarin thyroid fiye da kima a cikin jiki (hyperthyroidism), to, shan magungunan da ke rage yawan sinadarin thyroid ɗin (antithyroid medications) zai iya rage kumburin.

    3. Magance Maƙoƙo ta Hanyar Hasken Radiation (Iodine Radioactive Therapy: Ana amfani da wannan dabarar ta hasken radiation don rage girman jakar thyroid ɗin a lokutan hyperthyroidism.

    4. Aikin Tiyata (Surgery): A wasu lokutan, idan maƙoƙo ya yi girma sosai har ya kai yana kawo matsala wajen numfashi ko haɗiyar abinci, ko kuma idan ana zargin ciwon daji ne ya haddasa shi, to, ana iya cire wani ɓangare ko dukkan jakar sinadarin thyroid ɗin (thyroidectomy).

    5. Kulawa Ta Akai-Akai (Regular Observation): Idan maƙoƙon ba ya haifar da wata matsala, to, likita yana iya bayar da shawarar a cigaba da lura da yanayinsa ba tare da yin magani nan-take ba.

    A taƙaice, in mutum yana ɗauke da maƙoƙo ko alamunsa ya kamata a je asibiti domin a yi bincike a tabbatar da abinda ya haddasa wannan maƙoƙon, sannan a ɗauki matakin da ya dace.

    Domin karanta Cutar Damuwa danna nan
    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Cutar Damuwa (Depession)

    Cutar Damuwa (Depession)

    Cutar damuwa (depression) cuta ce da take shafar zuciya da ƙwaƙwalwa. Mutane da yawa suna ganin cewa depression shi ne mutum ya shiga cikin matsala ko ya rinƙa jin haushi da ɓacin rai na ɗan wani lokaci. Sai dai cutar ta wuce haka. A turance depression na nufin danne wani a hana shi rawar gaban hantsi ,ko kuma mutum ya shiga wani yanayi da bature yake cewa “Boredom”,wato yanayi na rashin abin yi.

    1-Clinical depression.
    Clinical depression ana kiran sa da major depressive disoder ko, biochemical depression, ko endogenous depression ko biological depression ko kuma unipolar disoder. Duk waɗannan sunayen ana amfani da su wajen kiran irin depression ɗin da yake zama matsala ga rayuwar mutum sosai, ta yadda in ba asibiti a ka je ba, sai dai abun ya ƙara muni.

    TA YAYA AKE GANE MUTUM YANA FAMA DA CLINICAL DEPRESSION?

    “International statistical classification of diseases and related health problems 10th revision (ICD-10) “ wata hanya ce da WHO ta samar don gano alamomin ciwuka irin depression. A tsarin ICD-10, ana tabbatar da cewa mutum yana da clinical depression ne idan ya shafe a ƙalla sati biyu ɗauke da alamomin clinical depression. Haka zalika sai waɗanan alamomin sun zama ana tare da su kusan kullum kafin a kai ga tabbatar da cewa akwai depression.

    ALAMOMIN CLINICAL DEPRESSION:-

    1. Baƙin ciki da ɗebewar tsammani da rayuwa (hopelessness). Da jin rayuwarka ba ta da ma’ana, wato mutum ya rasa abinda ke masa daɗi a duniya. Idan hakan ya zamanto yana faruwa da mutum a kowacce rana, to za a lissafa shi a cikin alamomin clinical depression. Yara ‘yan ƙananu masu shekaru 13-19 (teenagers) kuwa, idan suna fama da cutar depression, suna kasa zama wuri ɗaya, sannan ga saurin fushi da zafin rai maimakon baƙin ciki da ɗebewar tsammani irin na rayuwa.

    2. Mutum ya ji kwata-kwata ba ya sha’awar al’amuran rayuwa kamar yadda sauran mutane suke sha’awa. Kuma ko da ya yi wadannan abubuwan, ba zai samu farin ciki ko jin daɗi kamar yadda sauran mutane suke samu ba.

    3. Rama daga wajen mutanen da su suke nema ba misali (waɗanda ƙiba ta yi musu yawa suka rage cin abincinsu don rage ta wato dieting) Ramewa da kashi biyar daga cikin kaso ɗari na nauyin jiki ( 5% loss of body weight) ko sama da haka, yana nuni cewa akwai alamar cutar clinical depression.

    4. Yin bacci fiye da kima ko kuma matsala da wahala wajen yin bacci ga wasu.

    5. Yawan kai-komo fiye da kima (psychomotor agitation), ko kuma rashin motsi da zama waje ɗaya (psychomotor retardation) ga wasu.

    6. Yawan gajiya ko kuma rashin ƙarfi kusan kodayaushe ko kuma mafi yawan lokuta.

    7. Mutum ya rinƙa jin ba shi da wani amfani a duniya (worthlessness) ko kuma ya rinƙa jin kamar ya yi wani babban laifi (guilt).

    8. Mutum ya kasa yin tunani ko kuma mayar da hankali kan wani abu (lack of concentration). Ko kuma ya kasa yanke hukunci a rayuwa kamar yadda sauran mutane suke yi.

    9. Yawan tunanin mutuwa; ya zama kodayaushe ko kuma a mafi yawan lokuta shi mutuwa yake tunani. Wasu daga cikin masu cutar ba wai mutuwar suke tsoro ba, amma dai kullum cikin tunaninta suke, wasu kuma masu wannan matsalar suna tsoron mutuwa fiye da yadda sauran mutane suke, wato fiye da yadda hankali zai ɗauka.

    Kun ga kenan idan kuka duba abubuwan da na lissafo a sama, za ku gane cewa “Depression babbar matsala ce mai sarƙaƙiya”. Idan ba kai kake fama da ita ba, ba za ka taɓa gane yaya mai fama da ita yake ji ba. Shi yasa wasu a cikin jahilci suke hantarar masu cutar depression, a ganinsu ba rashin lafiya ba ne.

    Hakan ba ƙaramin matsala yake jawowa ba. Yana sanyawa mutane su ƙare rayuwarsu cikin baƙin ciki da damuwa, wasu ma har su yi tunanin kashe kansu. Ya zama dole a ilimantar da mutane akan cutar depression ,don kowa ya gane cewa mai depression taimako yake nema ba hantara da cin mutunci ba.

    Cutar damuwa (depression) ya kasu kashi biyar:-

    1-Melancholia ko Melancholic depression: (Yana jawo matsalar rashin cin abinci ko rashin bacci ko kuma mutum ya ji ya tsani zama cikin mutane) wannan depression ne me muni.

    2- Psychotic depression: Yana saka mai cutar rasa hankalinsa na wani lokaci. Ya rinƙa ganin abinda mutane ba sa gani ko kuma abinda babu shi a duniya. (Hallucination da delusion).

    3- Atypical depression: Yana sanya mutum ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya zama a birkice (anxiety) ko kuma cikin tsananin tsoro da razana (panic attack).

    4-chronic dysthymic disoder: Wannan depression ne da ba shi da tsanani amma akan shafe tsawon lokaci ana fama da shi. Yana farawa daga lokacin da aka balaga (adolescence) sannan akan shafe shekara biyar zuwa shekaru da yawa ana fama da shi.

    5- Seasonal Affective Disoder (SAD) depression ne da yake zuwa lokacin sanyi (winter) kuma yake tafiya lokacin zafi.

    Gano haƙiƙanin abinda ke jawo depression ya gaggara. Har yanzu ana tafka muhawara tsakanin masana kimiyya akan abinda ke jawo depression. Sai dai dukkan muhawarar ta ta’allaƙa ne akan abubuwa guda uku:-

    A-Wasu na ganin cewa depression ya shafi al’amura na biology (biological factors). Wato samun canji na wasu sinadirai da suke kai-komo tsakanin ƙwaƙwalwa da sauran sassan jiki. Waɗannan sinadirai su ake kira ‘yan aika (neurotransmitters).

    B-Wasu na ganin yanayin tunani ke jawo depression. Suna ganin cewa idan mutum yana yawan yin tunani mai jawo baƙin ciki (negative thoughts), to hakan zai haifar da matsala ga tsarin rayuwarsa, ya zamto yana jin haushin kansa da haushin sauran jama’a ba tare da dalili ba. Waɗanan su ake kira da “Congnitive factors”.

    C- Akwai kuma masu ganin cewa matsalolin rayuwa irin su rabuwar aure, kora daga aiki, cutarwa ko cin zali (bully), talauci, da sauransu su ke jawo depression. Wannan shi ake kira “Socio-cultural factors.

    Akwai abubuwan da ake zargin suna jawo cutar depression bayan waɗannan ukun da na lissafa a sama;

    • Gado
      Mutuwar iyaye
      Yawan tunani
      Raina kai ko abinda za ka iya (low self-esteem)
      Rashin aikin yi.
      Rashin wurin kwana (homeless).
      Yaudara ko daga saurayi ko budurwa.
      Cutarwa daga (‘yan fashi, ɓarayi, fyaɗe da sauransu).
      Shaye-Shaye (shan giya ko magunguna ba bisa ƙa’ida ba, magungunan hana haihuwa da sauransu).
    • Yawan amfani da magunguna masu ƙarfi wajen kashe (pesticides) ƙwari, binciken wasu masana ya tabbatar da yiwuwarsa na jawo depression.

    Kafin mai cutar ya sha kowanne irin magani ya fara zuwa ganin likita. Shan magani ba tare da shawarar likita ba zai iya haifar da wata larurar. Yawaitar ziyartar likita lokaci bayan lokaci.

    Manazarta:-
    World Health Organisation (WHO) (2022)

    National institute of Mental Health (NIMH). (2022) Depression.
    Depression: A cognitive Approach (2018).Routledge.

    Danna nan don karanta Ciwon Zuciya

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu