Category: Kiwon Lafiya

Mun samar da wannan ɓangaren ne domin koyar da ilimin yadda ake kula da lafiya a cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Za ku iya kai wa gare su ta hanyar amfani da kwamfutoci ko wayoyin hanu.

wikiHausa ta kowa ce. Kowa zai iya taimakawa da ilimi ko gyara. Bugu da ƙari, kowa na iya amfani da wannan kafa domin koya ko koyarwa.

  • Yadda ake fita daga cikin cutar damuwa.

    Yadda ake fita daga cikin cutar damuwa.

    Fama da matsanancin yanayi na damuwa abu ne wanda yake hana walwala da jin daɗi na rayuwar yau da kullum. Idan kana fama da tunani na baƙin ciki, kaɗaici, ko kana yiwa kanka kallon wanda bashi da amfani ko kallon banza, sannan kana ganin cewa kamar al’amuran ka bazasu daidaita ba, to ƙila fa kana fama da cutar damuwa ne.
    Idan kanaso kasan yadda ake fita daga cikin cutar damuwa sannan ka koyi yadda zaka koma jin daɗin rayuwarka, ka bi waɗannan hanyoyin:

    1. Hanya ta farko;
    Fahimtar cutar damuwarka.

    i. Kaje wajen likita ya duba ka.
    Sai idan mutum yaje yaga likita ko masani akan fannin ciwuwwukan halayyen dan Adam ne tukunna za’a gane yadda cutar take da kuma asalinta.
    Dayawa daga cikin magunguna suna iya bada gudun mawa izuwa ga cutar damuwa. Saboda haka, likitan ka shi zai baka gwaje-gwajen da ya kamata kayi, shi zai duddubaka ta yadda zai gano ta inda ƙarƙashin lamuran alamomin cutar suke.

    ii. Ka gane cewa kana fama da cutar damuwa.
    In kanaso ka fita daga cutar damuwar da kake ciki, sai ka fara tantancewa idan abubuwan da kake ji a jikin ka alamomin cutar damuwa ne. Duk da cewa alamomin cutar damuwa sun banbanta a gurin kowane mutum, ga wasu kaɗan daga cikin manyan alamomin cutar damuwa. Kana fama da cutar damuwa, idan:

    • kana jin kamar rayuwarka bata da amfani, ko kai kanka, kana cikin yanayi na rauni, ko kana jin kamar kana ganin kanka a matsayin mai laifi kana tsarguwa da kanka ba tare da sanin dalili ba.
    • kana jin rayuwar ka a raunane take sannan kana ganin ba abinda zai iya inganta maka rayuwarka.
    • kana yawan jin gajiya da kasala a jikin ka a ko mai kayi.
    • kana fama da rashin nutsuwa da rashin kwanciyar hankali da daddare, kuma kana fama da rashin barci da daddare da/ko tashi da safe.
    • ka daina jin daɗin abuwan da suke maka daɗi kuma suke sa maka farin ciki a da, kamar zama da abokai, yin abubuwan da suke saka ka nishaɗi, ko kuma jima’i.
    • akwai babban sauyin yanayi a yadda kake barcin ka ba kamar yadda ka saba ba, kamar rashin barci, tashi da sassafe, ko kuma nauyin barci.
    • bakajin kana son cin abinci ko kuma cin ka ya ƙaru sosai, amma kuma ka kasa dainawa.
    • yafi maka sauƙi ka zauna cikin kaɗaici akan kayi mu’amala da mutane.
    • abu kaɗan ne yake ɓata maka rai kuma ba tare da ƙwaƙwƙwaren dalili ba.
    • kaji ranka yana ɓaci ba tare da dalili ba.
    • ka taɓa yin tunanin kashe kanka. Idan kana tunanin kashe kanka to ka gaggauta neman taimako nan take.

    iii. Ka fahimci abubuwan da suke da alaƙa da saka ƴiwuwar ciwon damuwa.
    Duk da dai likotoci da masana fannin cutar basu bada dalili ɗaya kacal da yasa mutane suke fama fa cutar ba, suna ganin cutar tana tattare da mutane ne masu ƙwayoyin halitta iri ɗaya ta yadda zasuyi gadon ta, da kuma yanayi.
    Ko wani ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai iya zama shine silar faɗawar ka cikin cutar damuwa:

    • sabo da shan giya, ko ƙwayoyi, ko duk wasu abubuwan kayan maye.
      Idan ka saba da shan giya ko ƙwayoyi ko duk wani abu da zai saka maye, to wannan zai iya zama silar da ta jefa ka cikin ciwon damuwar da kake fama dashi. Likita ko wani masani kan lamuran sabo da shaye-shaye zai iya taimaka maka ya ɗora ka akan ƙa’idojin da ya kamata kabi domin fita daga cikin sabo da shaye-shayen ka.
    • samuwa ta gado. Idan akwai masu fama da ciwon damuwa daga cikin ahalin ka, musamman ta ɓangaren iyaye da kakanni, to fa kaima zaka iya kamuwa dashi ta gado.
      Zaka iya tattaunawa da mutanen gidanku ka tambaya ko da kuwa akwai wanda yake da cutar a cikin ahalinku, ko da kuwa ba’a taɓa gano asalinta ba; zaka iya tambayar iyayen ka ko wasu daga cikin ƴan’uwan ka ko an taɓa samun masu cutar a ahalinku da kai baka sani ba.
    • rashin daidaiton ƙwayoyim sarrafa abubuwa a jikin ɗan Adam. Idan kana fama da rashin daidaiton wasu ƙwayoyi na cikin jikinka masu sarrafa abubuwa, ƙila shine yake saka maka ciwon damuwar ka.
    • wata cutar daban. Likita zai iya taimaka maka ya gani ko kana fama da wata cutar daban ce wadda zata iya saka maka cutar damuwa, kamar cutar juyayi ko cututtukan da suka shafi tunanin mutum.
    • sakamakon wani magani da kake sha.
      Idan kana shan wani magani na wata matsalar da kake fama da ita, likita zai iya faɗa maka idan cutar damuwa yana daga cikin sakamakon wannan maganin kuma zai iya baka wani maganin da yake da amfani iri ɗaya wanda baya saka wannan sakamakon.
    • sauyawar yanayi.
      Wasu mutanen sukanyi fama da cutar damuwa saboda sauyawar yanayi. Misali, alamomin cutar suna iya bayyana a cikin yanayi na sanyi ko zafi.

    iv. Ka duba abubuwan da zasu iya saka ka a cikin cutar damuwa masu dalili.
    Ka fara tunanin abubuwan da suke da tushe na ciwon damuwar ka wanda suke saka maka zafin ciwon a rayuwarka ta kullum. Akwai yiyuwar cewa wasu abubuwan da suke faruwa da kai, da yadda kake tafiyar dasu, sune suke bada gudunmawa izuwa ga cutar damuwar ka. Ga wasu daga cikin abubuwan da kan iya janyo silar jefa ka cikin cutar damuwa ko kuma ma suke ƙara dagula lamarin cutar damuwar ka:

    • mutuwar aboki ko masoyi.
      Shiga cikin yanayi na baƙin ciki da alhini na rashin mutum abu ne wanda aka saba kuma mara aibu, amma, bayan wani lokaci, yawanci daga cikin mutane sukan dawo daidai. Idan baka daina jin baƙin ciki ba bayan watanni, to fa kila kana fama da cutar damuwa ne.
    • lalatacciyar dangantaka, mara daɗi, ta soyayya ko zamantakewar ma’aurata.
      Idan kana fama da zafin rabuwa da kayi da masoyinka, ko kana cikin dangantakar da take baka rashin kwanciyar hankali, zai iya bada gudunmawa izuwa ga cutar damuwar ka.
    • sana’a mara amfanuwa a gareka.
      Idan bakajin daɗin sana’ar da kakeyi, ko kuma kana wa kanka kallon banza a sana’ar da kakeyi, to ƙila aikin ka yana bada gudunmawa izuwa ga cutar damuwar ka.
    • yanayin zama mara kyau.
      Idan kana zaune ne da maƙotan da suke takura maka, ko kuma bakajin daɗin gidan ka ko unguwar da kake ciki, toh yanayin ka ƙila yana bada gudunmawa izuwa ga cutar damuwar ka.
    • matsalar kuɗi.
      Yawan damuwa akan inda zaka sake samun kuɗi ka biya kuɗin haya, ko abinci, ko wani abu mai amfani kan iya zama gagarumin silar jefa ka cikin ciwon damuwa musamman idan matsalar kuɗin mai cigaba ce.
    • yanayin damuwa da baƙin ciki da mata suke shiga bayan haihuwa.
      Yawancin mata sukan shiga cikin hali na baƙin ciki da damuwa bayan sun haihu. Wannan na iya zama mai tsanani wanda ake kira da cutar damuwar bayan haihuwa. Sai ayiwa likita bayani idan alamomin ki yayi kama da na wannan.

    v. Fahimtar zaɓin hanyoyin magance cutar damuwar ka.
    Likita zai faɗa maka zaɓin hanyoyin magance cutar damuwar ka da ya dace da kai. Ya danganta da yadda tsananin cutar damuwar ka take, ƙila kana buƙatar a haɗa maka da magunguna da kuma samun zama da masani kan halayyar dan Adam. Duk da magunguna suna iya ƙoƙarinsu na kawar da cutar damuwa, amma yanada matuƙar amfani mai fama da cutar damuwa ya fahimci cutar sannan ya koyi dabaru masu lafiya wanda zai jure wa cutar. Yawanci, ƙananan cututtukan damuwa a kan warkar dasu da zama da ƙwararru da masana halayyar dan Adam, da kuma gyara salon yadda mutum ke tafiyar da rayuwarshi.

    • akwai magungunan da an tabbatar da suna magance cutar damuwa.
    • akwai samun zama da akeyi da ƙwararru da masana halayyar dan Adam wanda shima yana taka babbar rawa a wajen kawar da cutar damuwa.
    • akwai kuma wata hanya da ake yiwa masu fama da matsananciyar cutar damuwa magani, itace hanyar da ake tayar da ƙwaƙwalwar mutum da na’ura. Wannan hanyar ana bin ta ne idan mai fama da cutar damuwa magunguna basuyi mishi aiki ba, ko kuma zama da ƙwararru bai mishi aiki ba.

    vi. Ka samu littafi ka fara rubutu akan abubuwan da suka shafi rayuwar ka.
    Fara yin rubutu akan abubuwan da suka shafi rayuwar ka kan taimaka wajen gano inda cutar damuwar ka take, da tunane-tunanen ka, sannan kuma zai sa kayi duba izuwa ga yadda kake tunanin ka a kullum. Ka ƙudurce yin rubuta a littafin ka a ƙalla sau ɗaya a kullum, musamman da yamma ko dare, ta yadda zaka kammala dukkan abubuwan da wannan ranar ta kawo a gareka.
    Rubutu yakan sa kaji kana da alaƙa da tunanin ka, ya kan sa kaji kamar ba kai kaɗai bane, sannan yana sa kasan abubuwan da suke saka ka farin ciki da abubuwan da suke saka ka baƙin ciki.

    • rubutu yana taimakawa wajen sa ka mai da hankali izuwa ga kanka, sannan yana rufe zuciyar ka ga tunanin abubuwan da ke janyo rashin jin daɗi a rayuwarka.

    2.
    Hanya ta biyu;
    Inganta rayuwarka.

    i. Ka cire duk wata lalatacciyar zamantakewar da bata da amfani a rayuwar ka.
    Idan zamantakewar da kake ciki yana saka maka baƙin ciki, to lokaci yayi da ya kamata ka daina shiga cikin halin rashin jin daɗi saboda wannan.
    Ka rabu da duk wani wanda yake haddasa maka baƙin ciki, idan wanda yake saka maka wannan baƙin cikin ɗan’uwan ka ne wanda bazaka iya rabuwa dashi ba, to ka zauna da wannan mutumin a mafi ƙarancin lokacin da zaka iya.

    • idan akwai abinda yake damun ka a cikin wata zamantakewa, ka zauna ku tattauna sosai da wanda kake cikin zamantakewar tare. Misali, idan kana fama da cutar damuwa ne saboda matar ka tana cin amanar ka, ko kuma aminin ka yana satar maka kuɗi, to mafi dacewa shine ka tunkare su da maganar ta yadda za’a nemi mafita.

    ii. Kulawa da lafiyayyen dangantaka da zamantakewa.
    Duk da dai zaka ji wani lokacin ka fi son zaman kaɗaici ba tare da mutane ba, yana da kyau ka sani cewa abu ne mai kyau ga yanayin ka zama cikin mutane. Ka dogara ga abokan ka da kuma ƴan’uwan ka, sannan ga masoyinka in kana da shi.
    Ka zauna da mutanen da suke saka ka farin ciki da nishaɗi na mafi yawan lokacin da zaka iya. Abokai na ƙwarai ba iya taimaka maka sukeyi wajen kawar da cutar damuwarka ba, har da taimaka maka wajen yadda zaka ji daɗi da kuma sanin cewa ana sonka da goyon bayanka sukeyi.

    • idan kana da aboki ko ɗan’uwa wanda yake fama da cutar damuwa, ka musu magana, sannan kaga wani irin shawarwari zasu baka. Magana da wanda yake fama da irin cutar da kake fama da ita kan sa kaji bakai kaɗai bane.
    • idan kana cikin zamantakewar auratayya ne, ka samu ka samar da lokacin soyayya da kai da wanda kuke cikin zamantakewar tare. Ku samu lokacin da zaku zauna ku kadai kuna jin daɗin ku.
      Kaji daɗin zamantakewar ka da samar da lokacin zama da abokin zamantakewar ka a mafi yawan lokacin da zaka iya.
    • ka ƙarawa iyalanka lokacin ka. Iyalanka ya kamata su zasu saka ka kaji ana ƙaunar ka da goyon bayan ka, saboda haka, kayi ƙoƙarin zama a cikin iyalan ka a mafi yawan lokacin da zaka iya. Idan kana da nesa da iyalanka, musamman idan ba’a ƙasa ɗaya kuke ba, to ka dinga samar da lokacin da zaka dinga kiransu ta wayar salula.

    iii. Ka tsara jadawalinka na kanka ta yadda zaka ciki shi da abubuwan da kakeso kuma kake ƙauna.

    Idan ka tsara jadawalinka ta yadda zaka kasance kullum kanada abinda zakayi, to wannan zai sa dole zaka zama kana cikin aiki, zaka kasance kana jin karsashi, zaka zama kana mayar da hankali, sannan zaka dinga tunanin abu na gaba da zakayi.
    Zaka iya tsara jadawalinka na kowace rana daga farkon mako, ko kuma ka tsara na kowace rana a kullum, a kowani dare kafin wannan ranar. Duk hanyar dai da ka ɗauka, ka tabbatar ka ƙudurce manufar riƙe wannan hanyar.
    Ga wasu daga cikin abubuwan da ya kamata ka basu lokaci na kansu:

    • abota da mutanen kirki, nagari, masu goyon bayanka.
    • motsa jiki
    • ayyukan hutu da abubuwan da kakeso wanda suke baka nishaɗi.
    • lokacin da za ka zauna ka nutsu, kayi rubutu a littafin ka, ko kayi tunani.
    • lokacin da zakayi abubuwa na wauta wanda suke saka nishaɗi da dariya, tunda murmushi da dariya sukan saka mutum cikin farin ciki.
    • wasanni wanda akeyi a waje. Kada ka ɓata duka lokacinka a cikin gida. Maimakon hakan, ka fita waje cikin rana, ko kayi wasu ayyukan da ka saba yi a cikin gida a waje, kaman a gidan cin abinci mai kyau ta yadda baza kaji kana cikin kaɗaici sosai ba.

    Idan ka kai bugun zuciyar ka sama na tsawon minti 27 ta hanyar yin wani abu na motsa jiki, ya kan iya ɗaga sinadarin da yake sawa ƙwaƙwalwarka nutsuwa. Saboda haka, zuwa yin gudu ko iyo a ruwa kan taimaka sosai.

    iv. Ka nemo wani abu sabo wanda kake so.
    Ba lallai kanason aikin da kakeyi a yanzu ba, kuma ƙila baka cikin matsayin da zaka sauyawa kanka aiki a yanzu. Neman abinda kakeso kan taimaka maka wajen jin cewar kanada manufa a rayuwarka kuma wannan shi zai baka dalilin tashi da safe kullum da zumma. Abinda kakeso kan iya zama duk abinda kake ganin kana muradin yin shi, ko da kuwa baka ƙware sosai a yin wannan abin ba.
    Ga wasu daga cikin hanyoyin da zasu taimaka maka wajen neman abu/abubuwan da kakeso:

    • ka bincika bangarenka na fasahar da kake dashi. Ka shiga koyon zane na rubutu, zane da launuka, ko ajin koyon yin abubuwa da yumɓu.
    • ka bayyana kanka ta hanyar yin rubutu. Ka gwada rubuta ɗan taƙaittacen labari, ko zube.
    • ka samo sabuwar soyayyar son koyon yaren da ba naka ba.
    • ka samo sabon wasa mai tawagar mutane, kamar wasan ƙwallo ko wasan ƙwallon kwando. Zaka samu abinda kakeso a yanayin da kakeyin sababbin abokai.
    • ka samo soyayyar ka da karatu ta hanyar shiga wata ƙungiya ta masu son karatu.
    • kayi ƙoƙari kasan manufarka a rayuwa. Menene abunda ya kamaceka kuma kakeso kayi a duniyar nan? Samo/ nemo waɗannan amsoshin kan iya taimaka maka wajen nema wa kanka mafita a kowane irin yanayi.

    v. Ka ƙara akan yadda kake taimako, ka zama mai taimako da taimakawa.
    Ka juyar da rayuwarka daga cikin cutar damuwa ta hanyar zama mai taimako izuwa ga mutanen da kakeso da kuma mutanen unguwarku. Idan kana taimako, hakan nasa mutum yaji rayuwarshi tanada amfani, kuma zaisa ka gina alaƙa mai ƙarfi tsakaninka da mutanen da kake tare dasu.

    • kayiwa abokan ka makusanta alfarma. Ba lallai sai alfarmar ta zama babba ba- idan babban abokin ka yana fama da aiki sosai, zaka iya zuwa ka daukeshi ko kuma ka mishi wanki da guga. Zakaji daɗi idan ka taimaka.
    • ka sa kanka cikin aikin taimako a masallacin unguwarku, ko gidan karatun unguwarku, ko makarantun unguwarku.
    • ka sa kanka cikin aikin taimako a gidan marayu, gajiyayyu, marasa muhalli, yan gudun hijira, sannan kaga irin gudunmawar da kaima zaka iya bayarwa.
    • ka sa kanka cikin aikin taimakawa wajen gyaran muhallinku a unguawarku, ko gonaki, ko lambu.
      Iya zama a cikin lambu mai shukoki da halittun Allah na tsawon wani lokaci kan taimaka wajen inganta yanayin ka.

    3.
    Hanya ta uku;
    Sabarwa da kanka lafiyayyun halaye da al’adu na yau da kullum.

    i. Ka inganta halayyar baccin ka.
    Gyaran halayyar baccinka kan iya zama babban cigaba ga lafiyar ƙwaƙwalwarka. Ka duba kaga lokacin bacci da tashi wanda yafi dacewa dakai. Ga wasu daga cikin abubuwan da zakayi:

    • ka fara kwanciya da tashi a lokaci guda a kowani dare da safiya. Wannan zai sa kaji kafi samun hutu, kuma zai sauƙaƙa maka wajen yin bacci da tashi a koda yaushe.
    • ka fara sauka daga kan gadon ka da ƙafar dama. Ka tashi nan take daga kan gadon sannan kasha kofi daya na ruwa maimakon kayita juyi kafin ka taso daga kan gado.
    • ka gyara ɗabi’unka wanda kakeyi kafin ka kwanta bacci. Idan lokacin baccinka ya kusan zuwa, ka kashe talabijin, ka ajiye wayar ka ta salula a gefe, ka guji hayaniya da kuma karatu akan gado.
    • ka rage/daina shan sinadaren da suke hana mutum bacci, musamman wanda suke cikin shayi, goro, musamman da yamma ko dare. Basa sa mutum yayi bacci.
    • ka guji yin ƙananan baccin da suke wuce rabin sa’a, sai dai in kana buƙatar su- su na sa ka dinga jin kasala sannan su gajiyar da kai.

    ii. Motsa jiki.
    Motsa jiki na minti 30 kacal a rana yana yin tasiri sosai akan inganta lafiyar jikin ka da lafiyar ƙwaƙwalwarka. Motsa jiki yana ƙara maka ƙarfi sannan yana sa maka ƙwarin gwiwar yin abubuwa a kowace ranar da kayi shi.
    Ka nemo tsarin motsa jiki wanda yafi dacewa da kai sannan ka riƙeshi ka dinga yi.

    • iya tafiya a ƙafa na minti 20 a kowace rana yana iya zama motsa jiki.
    • ka nemi wajen/gidan motsa jiki, ko ka nemi aboki wanda zaku dinga motsa jiki tare, hakan na taimakawa wajen kaji kana jin daɗin motsa jikin.
    • ka ƙudurce manufar motsa jiki na tsawon wani lokaci ko yin wani abu sabo, zaka iya ƙudurce niyyar motsa jiki na tsawon sa’o’i ko kayi wani sabon salon motsa jikin da baka saba yi ba.

    iii. Ka inganta cimarka ta cin abinci.
    Cin abinci mai kyau, lafiya, ingantacce, a daidaice kan taimaka wajen kawar da cutar damuwa. Ko da kuwa bakajin kanason cin abinci, ya kamata ka jajirce kaci abinci sau uku a rana. In kana fama da cutar damuwa, kar ka bari ka rame sosai saboda rashin cin abinci, cin abinci mai kyau da lafiya akai-akai zai taimaka wajen inganta lafiyar jikinka da kuma lafiyar ƙwaƙwalwarka.

    • kada ka dinga ƙetare cin abincinka- musamman karin kumallo. Cin abinci sau uku a rana zai baka ƙarfi da karsashin da kake buƙata ka fatiyar da lamuran rayuwarka, sannan yana sa maka nutsuwa da mai da hankali.
    • ka ƙara ƴaƴan itace da kayan lambu sosai a cikin cimarka. Ka koma cinsu a maimakon kayan zaƙi ko abincin da bai da amfani.
    • ka tabbatar da kana cin daidaitaccen ƴaƴan itace, kayan lambu, hatsi, kifi, da abinci mai gina jiki a kullum.
    • kar ka matsawa kanka, idan kanajin kwaɗayin cin wani abu wanda kake marmari, zaka iya ci daga lokaci zuwa lokaci. Zaka fi jin dadin bin ƙa’idar inganta cimarka idan kana cin abubuwan da kake ƙwadayi da marmari daga lokaci zuwa lokaci.

    iv. Ka dinga tunani mai kyau.
    Yin tunani mai kyau na taimaka maka ka dinga kallon rayuwarka da duniyarka ta yadda zaka dinga fatan yin wani abu mai kyau ba akasin haka ba. Idan kanaso ka dinga tunani mai kyau, sai ka fara koyon yadda zaka iya gane tunani mara kyau, kuma ka yaƙe su da ƙarfin tunani mai kyau a duk lokacin da zaka iya.
    Ta yadda zaka iya fara tunani mai kyau, ka nemi a ƙalla abubuwa guda 5 wanda kake godewa Allah a kansu sannan suke saka jin daɗi a koda yaushe.

    • kayi ƙoƙarin ajiye littafi wanda yake cike da abubuwan da kakeso ko suke saka ka farin ciki. Kullum ka rubuta abubuwa wanda kakeso ko suke saka ka farin ciki guda uku, ko fiye da haka, sannan a kowani sati ka karanta abubuwan da kakeso. Wannan zai sa ka dinga hangen rayuwa ta fanni mai kyau sannan zai taimaka maka wajen mayar da hankalinka akan abubuwa masu kyau akan marasa kyau.
    • idan kana aiki mai kyau ko kana kallon rayuwa ta mahanga mai kyau, hakan zai sa ka dinga tunani mai kyau.
      Kayi tsari a rayuwarka ta yin magana akan abubuwa masu kyau na rayuwarka ko ka dinga tafiyar da lokacinka a gurin yin abubuwan da suke saka farin ciki da nutsuwa.
    • idan kafi tafiyar da lokacinka akan yabon abubuwan da suke saka murmushi da farin ciki akan abubuwan da basu da kyau, ko abubuwan da suke saka baƙin ciki, ko abubuwan da baka so, tunanin ka zai karkata izuwa tunani mai kyau. Ka faɗawa kanka iya “ranar yau zata zama babbar rana a gareni” ko kuma “hakan yamin daidai, yau ina cikin farin ciki, ranar yau tana yimin daɗi, bazan bari a ɓata min ranar nan ba!” zai sauya yanayin ka izuwa ga yanayi mai daɗi sosai da sauƙi a gareka, zaka kasance kanajin daɗin yanayin da kake ciki a iya faɗawa kanka irin waɗannan kalaman.
      Ka kasance kana murmushi a koda yaushe, hakan yana saka cikin farin ciki, ko da kuwa baka cikin farin ciki.

    v. Ka inganta yanayin shigarka da tsaftarka.
    Banzatar da inganta yanayin da yadda kake shigarka da tsaftarka yana daga cikin abubuwan da suke nuna sakamakon cutar damuwa.
    Duk da dai bazaka fita daga cutar damuwa ta iya inganta yanayin shigarka da tsaftarka kacal ba, idan ka ɗauki lokacinka ka gyara yadda ake ganinka, idan ka ɗauki lokacinka kana kula da yanayin yadda kake shigarka da kuma tsaftarka a koda yaushe, kai kanka zaka fi jin daɗi a kanka.
    Ka dinga wanka kullum kuma ka dinga wanke bakinka da gashinka.

    • kayi aiki wajen inganta yanayin yadda kake shigarka da tsaftarka a lokacin da kake zaune kai kaɗai da kuma lokacin da zaka fuskanci mutane, ko da kuwa baka jin kanason kayi hakan. Wannan zaisa ƙwarin gwiwarka na fuskantar mutane da kuma jin cewa kaima kanada amfani duk su ƙaru.
    • idan kana ganin cewa ƙibar da kake da itace, itace sanadiyyar jefaka cikin cutar damuwa, to ka samar da wani tsarin da zai inganta kuma ya kula da wannan al’amarin na rage ƙibar da kake dashi, wanda zai inganta kuma ya ɗaga yanayinka izuwa ga yanayi mai kyau da bayyanar ka.

    Rubutun nan a taƙaice
    Shawo kan cutar damuwa yakan zama abu mai wahala, amma zaka iya koyon yadda zaka koma jin daɗin rayuwarka kamar yadda ka saba ta hanyar inganta zamantakewarka, dangantakarka, da kuma yin zabi mai kyau da lafiya a rayuwarka.
    Misali, kayi ƙoƙarin samun lokaci ka zauna da ƴan’uwanka da iyalanka. Sannan ya zamana cewa mutanen da zaka kewaye kanka dasu mutane ne na kirki, masu tunani mai kyau, masu goyon bayanka idan ka shiga cikin wani hali. Bacin samun lokacin zama da mutane, kaima ka warewa kanka lokacin kanka, ka tabbatar da cewa ka ware lokacin da zaka dinga yiwa kanka aiki. Misali, ka inganta yanayi da halayyar baccinka ta hanyar kwanciya da tashi a lokaci guda a kullum domin hakan ya taimaka maka wajen jin cewa ka huta sosai yadda ya kamata, sannan ya ƙara maka ƙarfi da karsashi a jikinka. Kayi amfani da wannan ƙarfin ka haɗa wani tsari da zaka dinga motsa jikinka a kullum tunda iya minti 30 na motsa jiki kullum yana inganta lafiyar jikinka da ƙwaƙwalwarka sosai.
    Domin koyon yadda zaka kawarda abubuwa marasa kyau wanda zasu dinga janyo ka baya, kaci gaba da karatu!

  • Ciwon Suga (Diabetes)

    Ciwon Suga (Diabetes)

    Ciwon suga sinadari ne mai matuƙar amfani a jikin mutum. Ana samun sa daga abincin da muke ci da kuma abubuwan da muke sha.

    Idan suga ya yi yawa, ko kuma ya yi kaɗan a jikin mutum, ana iya kamuwa da rashin lafiya wadda za ta iya sanadiyar mutuwar mutum idan ba a ɗau mataki ba.

    Akwai wani sinadari da ake kira insulin a jikin ɗan Adam. Sinadarin insulin shi ne yake kula da daidaituwar sinadarin suga a cikin jini. Idan mutum ya ci abinci mai dauke da sinadarin suga (carbohydrate), sai sugan ya koma cikin jini bayan ya narke. 

    Sai sinadarin insulin ya zo ya daidaita suga, domin kada sugan ya cutar da jiki. 

    Ma’anar ciwon suga, cuta ce wadda take faruwa sanadiyyar ƙaruwar yawan sinadarin sikari (suga) a cikin jini na tsawon lokaci. Cutar tana faruwa ne idan jikin mutum ya daina samar da sinadarin insulin, ko kuma insuin ɗin ya daina aiki gaba ɗaya.

    Rabe-raben Ciwon Suga

    Rabe-raben ciwon suga suna da yawa, amma za mu yi magana a kan guda uka kawai:

    1. Type I Diabetes

    Wannan nau’in ciwon sugan, yana faruwa ne idan jikin mutum ya daina samar da sinadarin insulin.

    Idan sugan  mai wannan nau’in ciwon sugan ya ƙaru, ba zai sauka ba, saboda babu insulin. Idan kuwa ana so ya sauka, to dole sai an yi allurar insulin.

    Wannan nau’in  ya fi kama yara. Haƙiƙanin abin da yake janyo wannin  nau’in ciwon ba a san shi ba, amma dai an tabbatar da cewa ana iya gadon ciwon daga wurin mahaifa(iyaye)

    2. Type 2 Diabetes

    Wannan nau’in yana farawa ne idan sinadain insulin ya daina aiki, ko kuma aikinsa ya ragu. Idan sugan mai wannan nau’in ya ƙara, ba zai sauka ba, har sai an sha maganin da zai dawo da aikin insulin.

    Wannan nau’in ya fi kama manya.

    Abubawan da suke janyo haɗarin kamuwa da wannan nau’in sun haɗa da:

    Ƙiba: Ƙiba mara misali, musamman wadda ta haura ma’aunin Body Mass Index (BMI) 3okg/M2.

    Rashin kazar-kazar: Waɗanda ko yaushe a zaune suke, ba sa kai-kawo, ba sa aiki kuma ba sa son aiki.

    Cin abincin da ba shi da inganci a likitance: Yawan cin abinci, musamman wanda yake ɗauke da sinadaran cholesterol, suga, fat masu yawa a cikin su. Misali butter, chees, lemukan roba da na gwangwani, Askirin (lce cream) da sauransu.

    Shan giya

    Gado: Idan mahaifi ko mahaifiya suna da ciwon suga.

    3. Gestational Diabetes

    Wannan nau’in ciwon suga yana faruwa ne ga masu juna biyu (ciki).

    Yanayin su ɗaya da Type 2 Dm. Sai dai ana warkewa daga wannan nau’in bayan an haihu. Ana iya ba su magani su sha, ko kuma a yi musu allurar insulin idan ana so suga ya daidaita.

    Alamomin ciwon suga

    i. Yawan fitsari  fiye da misali.

    ii. Yawan shan ruwa fiye da misali.

    iii. Yawan cin abinci fiye da misali.

    Illolin ciwon suga

    Masu gajeren zango: Su ne waɗanda suke faruwa a ɗan ƙanƙanin lokaci, kuma suna iya sanadiyyar mutuwar mutum nan take. Sun haɗa da:

    a. Suga ya yi yawa sosai a jinin mutum, yawan da ya wuce hankali; irin wannan matsalar tana janyo mutum ya yanke jiki ya faɗi ko kuma mutum ya rasa ransa a nan take.

    b. Suga ya yi ƙasa; wannan idan mutum yana shan maganin suga ko allurar cutar suga (insulin) fiye da yadda jikinsa yake buƙata; yana iya janyowa mutum ya yanke jiki ya faɗi ko kuma ya fita daga hayyacinsa.

    Masu dogon zango: Su ne waɗanda suke faruwa bayan mutum ya daɗe da ciwon suga a jikinsa.

    Misali:

    Ciwon ƙoda.

    Ciwo ko kuma gyambon ƙafa, wanda zai iya janyowa a yankewa mutum ƙafa.

    Ciwon ido wanda zai iya janyowa mutum ya makance.

    Ciwon zuciya.

    Cutar shanyewa ɓarin jiki

    Da sauransa.

    Magani/Shawarwari

    Magungunan ciwon suga, kala biyu ne. Akwai na ƙwaya da kuma allura.

    Idan mutum yana da ciwon suga, yana da matuƙar muhimmanci ya dinga yin waɗannan ababuwan:

    Shan magani ko yin allura a kan ƙa’ida.

    Yawan duba sinadarin suga akai-akai.

    Yawan motsa jiki a ƙalla san huɗu a sati kamar tafiyar ƙasa ta tsawon minti talatin.

    Daina shan giya

    Rage shan kayan zaƙi masamman lemukan gwangwani ko na roba.

    Rage cika ciki da abinci mai sinadain sikar (carbohydrate) a ciki kamar shinkafa, tuwo, masara, doya da sauransu.

    Yawaita cin ganyayyaki kamar su alayyahu, zogale, rama, ganyan salak da sauransu.

    Kammalawa

    Ciwon suga ciwon ne mai haɗarin gaske. Har yanza babu maganin da yake warkar da ciwon gaba ɗaya.

    Amma ana iya shan magani ko ayi allura domin a zauna lafiya. Don haka shan magani da zuwa asibiti ya zama wajibi ga duk mai cutar.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mene Ne Hawan Jini (HYPER TENSION) danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mene Ne Ciwon Sikila (SICKLE CELL DISEASE) danna nan.

  • Hanyar Warkar Da Ciwon Sanyi Da Maganin Sa

    Hanyar Warkar Da Ciwon Sanyi Da Maganin Sa

    Akwai hanyoyi da mace za ta bi domin rabuwa da wannan mugun ciwon.

    Shawarar farko game da wannan ciwon za ta bi; ko da ma ba ki da wannan ciwon in har an kusa auranki tom ki guji tsarki da ruwan sanyi sannan ki rinƙa yawan yanke farcenki kina wanke hannunki; ko da zai kai ki sosa gabanki kin ga datti ba zai shiga ba.

    Ki samu waɗannan haɗin ki rinƙa wanke gabanki da su;

    • Gishiri
    • Ganyen magarya
    • Ganyen lalle
    • Kanunfari

    Waɗannan za ki rinƙa dafa su ki samo flask ki rinƙa kama ruwa da su a kodayaushe. Sannan pant ɗinki ki rinƙa dafa shi da ruwan zafi da gishiri da Dettol kina wankewa ki sanya a rana ya bushe ki goge su, sun zama sababbi kenan.

    Maganin Ciwon Sanyi

    Ki nemo waɗannan itatuwan ki dafa su dan kawar da ciwon sanyi, musamman ki fara yin su two months kafin bikinki. Da yardar Allah kin rabu da ciwon sanyi, in kin gan ki da shi to sai dai a jikin mijinki kika samu. Shi ma namijin zai iya waɗannan haɗin dan ya rabu da shi.

    Ga abubuwan da za a nema kamar haka;

    • Sayen zogale ma’ana saiwarsa
    • Kanunfari
    • Jema
    • Jar kanwa
    • Gogamaso
    • Kaimin ƙadangare ko kuma ciyawar wutsiyar ƙadangare
    • Cini da zuga, wasu na cewa bini da zugu

    Waɗannan su ne za a tafasa su sosai sai sun fita hayyacinsu sai a tace a zuba a kofi; a sa zuma a sha sau biyu a rana. In Sha Allah za a rabu da matsalar sanyi kowanne iri ne.

    Don karanta cikakken bayani akan Yadda Za ki Kare Kanki Daga Ciwon Sanyi (Toilet Infection) danna nan

    Domin karanta cikakken bayani akan Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad kallamu

  • Cututtukan Da Ba Su Da Magani

    Cututtukan Da Ba Su Da Magani

    Aya ta (68) Allah (Subhanahu Wata’ala) ya ce:

    Cikin suratul Yaasiin “Duk wanda muka tsawaita rayuwarsa,tabbas za mu tauye shi a halitta, shin ba sa hankalta ne?”.

    Don haka, duk wanda shekarunsa suka zarce shekarun ganiyar ƙarfi (wato shekara arba’in (40) ), to fa ba ya zai rinƙa yi ba gaba ba.

    An karɓo hadisi daga usamatu ɗan Sharik Allah ya yarda da shi ya ce: “Ƙauyawa sun ce: Ya Manzon Allah! Ko ma yi magani? Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; I, ku bayin Allah ku yi magani, haƙiƙa Allah bai sanya wata cuta ba, face sai da ya sama mata waraka (da magani), sai dai ciwo ɗaya, suka ce, “Wane ciwo ne?” ya ce, “Tsufa.” Ahmad, Abu Dawud da wasunsu ne suka rawaito shi.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin A Kula Da Lafiya wanda Abubakar Abbas Ibrahim ya wallafa shi. Domin karanta cikekken littafin danna koren rubutun nan.

  • Mene Ne Ciwon Sikila (SICKLE CELL DISEASE)

    Mene Ne Ciwon Sikila (SICKLE CELL DISEASE)

    Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum yaji ciwo, ko kuma ya yanke jikinsa, yana ɗauke da abubuwa iri daban–daban, kamar su ‘plasma‛, ‘Red Blood Cells (RBC)’, ‘White Blood Cells (WBCs)‛, ‘Platelets‛ da sauransu.

    Cutar sickler tana faruwa ne idan aka samu matsala a RBC.

    RBC yana ɗauke da sinadarin ‘Haemoglobin (Hb)’ a cikinsa. Haemoglobin (Hb) kala–kala ne; akwai Haemoglobin A (HbA), Haemoglobin B (HbB), Haemoglobin C (Hbc), da sauransu. HbA shi ne lafiyayyen haemoglobin. Sauran Hb ɗin ba lafiyayyu ba ne.

    Cutar sickler tana ɗaya daga cikin cututtukan da ake iya kauce musu kafin samuwarta. Idan kuma cutar ta samu, to tana da wahalar magani.

    Ma’anar cutar sikila

    Cutar sickler tana nufin mutum yana ɗauke da sinadaran haemoglobin guda biyu marasa kyau (ba lafiyayyu ba) a jikinsa. Ma’ana dai ya gaji gurɓatattun sinadaren haemoglobin daga wurin mahaifiya da mahaifi

    Yadda ake samun cutar sikila

    Ana samun cutar sickler ne daga wurin iyaye (uwa da uba). Uba shi kaɗai ba zai iya haifar ɗa/’ƴa mai sickler ba, haka ma uwa ita kaɗai ba za ta iya haifar ɗa/’ƴa mai sickler ba. Dole sai da gudunmawar kowanne daga cikinsu (uwa da uba).

    Kowane mutum yana da sinadaren haemoglobin a jikinsa nau’i biyu. Zan yi magana a kan haemoglobin A da kuma haemoglobin S kawai saboda su ne suka fi yawa. kowane mutum yana da ɗaya daga cikin waɗannan Haemoglobin ɗin:

    (1) Haemoglobin AA (HbAA)

    (2) Haemoglobin AS (HbAS)

    (3) Haemoglobin SS (AbSS)

    • Wanda HbAA yana da lafiyayyun haemoglobin guda biyu.
    • Mai HbAS yana da lafiyayyen Haemoglobin guda ɗaya da kuma wanda ba lafiyayye ba (ba mai kyan ba) guda ɗaya
    • Mai HbSS yana da haemoglobin guda biyu marasa kyau.
    • Mai HbAA lafiya ƙalau yake. Ma’ana ba shi da ciwon sickler.
    • Mai HbAS shima lafiya ƙalau yake, ba shi da ciwon sickler, amma zai iya haifar ɗa/’ƴa mai sickler idan ya auri mai HbAS. Don haka, HbAS shi ake kira da ‚carrier‛
    • Mai HbSS, shi ne yake da ciwon sickler

    Lokacin da za a halicci mutum a cikin mahaifiyarsa, uwa tana ba da gudunmawar haemoglobin guda ɗaya, sannan uba ma yana bada gudunmawar haemoglobin guda ɗaya.

    Idan uba ya bada gudunmawar haemoglobin maras kyau (HbS) sannan uwa ma ta bada gudunmawar haemoglobin maras kyau (HbS), to tabbas ɗan da za’a haifa, zai kasance sickler ne (HbSS).

    Ga dai yadda za ta kasance idan aka yi aure.

    Iyaye (Uwa da Uba)

    Yanayin ‘Ya’Ya

    AA da AA AA a kowane Lokaci
    AA da AS AA, ko Kuma AS
    AS da AS AA ko AS ko SS
    AS da SS AS ko kuma SS
    SS da SS SS a kowane lokaci
    AA da SS AS a kowane lokaci
    Don haka, idan ana so a kauce wa cutar sikila, to kada a yi aure tsakanin.

    ‘AS’ da ‘AS’,

    ‘AS’ da ‘SS’,

    ‘SS’ da ‘SS’.

    Alamomin cutar sikila

    Suna bayyana ne tun yaro yana ƙarami a mafi yawancin lokaci. Alamomin sun haɗa da

    • Kumburin ƴan yatsu
    • Ciwon ƙashi mai tsanani
    • Ɗashewar jiki (ƙarancin jini)
    • Ƙanƙantar jiki
    • Da sauransu
    Illolin ciwon sikila

    Ciwon sickler yana haifar da illoli daban–daban, kamar:

    • Yawan rashin lafiya akai–akai kamar ciwon ƙashi, ƙirji, ciki da sauransu
    • Shanyewar ɓarin jiki (stroke)
    • Ciwon ƙoda
    • Rashin zuwa makaranta ko kuma yawan tangarɗar karatu
    • Yawan ƙarancin  jini
    • Shaye–shaye
    • Saurin mutuwa (mutuwa lokacin ƙuruciya da sauransu).
    Maganin ciwon sikila

    Babban maganin ciwon sickler shi ne kada a yi aure idan akwai yiwuwar a haifi ɗa mai sikila. Kuma ana iya gane haka ta hanyar yin gwajin genotype. Amma idan ciwon ya samu, to hanya ɗaya ce wadda ake iya maganin wannan cuta.

    Ita ce, dashen ɓargo (Bone marrow transplant), shi wannan dashen ɓargo yana tare da irin tasa matsalolin kuma ba kowane lokaci ake yin nasarar warkewa ba. Sannan kuma yana da tsada matuƙa da gaske.

    Ana ba wa masu sickler wasu magunguna domin samun sauƙin rashin lafiya akai-akai. Shi yasa ake so masu sickler su dinga zuwa wajen likita lokaci zuwa lokaci, koda babu abin da suke ji na rashin lafiya.

    Abubuwan da suke tayar da rashin lafiya ga masu ciwon sikila
    • Zafi mai tsanani
    • Zazzaɓi (ko na malaria ko kuma wani abu daban
    • Motsa jiki mai yawa
    • Ɓacin rai. Da sauransu

    Don haka yana da kyau a kaucewa waɗannan abubuwan.

    Kammalawa

    Ciwon sickler yana saka rashin lafiya akai–akai, yana hana jin daɗin rayuwa, sannan kuma yana sanadiyar mutuwar mutum yana ƙarami. Ana iya kaucewa ciwon idan aka bi shawarwarin likitoci ta hanyar yin gwajin genotype.

     

  • Mene Ne Hawan Jini (HYPER TENSION)

    Mene Ne Hawan Jini (HYPER TENSION)

    Akwai wani ma’auni da ake amfani da shi wajen kula da ƙarfin gudanar jini a cikin jijiyoyin jini. Wannan ma’auni ana kiransa da ‘Blood Pressure (BP)’.

    Yadda ake so BP ɗin babban mutum ya kasance shi ne:

    90 – 139/60 – 89 MMHg. ma’ana dai:

    (1) Ma’aunin sama ya kasance daga 90 zuwa 139. Kar ya yi ƙasa da 90, kuma ka da ya yi sama da 139.

    (2) Ma’aunin ƙasa ya kasance daga 60 zuwa 89. Kar  ya yi ƙasa da 60, kuma kada ya yi sama da 89.

    Ma’anar Hawan jini

    Hawan jini shi ne, BP ɗin mutum ya fi 139 (ma’aunin sama) ko kuma ya fi 89 (ma’aunin ƙasa)

    Abubuwan da suke janyo hawan jini.

    Hawan jini kala biyu ne:

    (1) Primary hypertension.

    (2) Secondary hypertension.

    Abin da yake janyo primary hypertension.

    Babu abu guda ɗaya, wanda bincike ya nuna cewa yana janyo irin wannan hawan jini. Amma dai akwai wasu abubuwan da suke da alaƙa mai ƙarfi da irin wannan hawan jinin. Waɗannan abubuwan sun haɗa da:

    • Gado: idan ɗaya daga cikin mahaifinka, ko mahaifiyarka ko kuma ɗan uwanka shaƙiƙi yana da hawan jini, to kai ma za ka iya kamuwa da hawan jini.
    • Shan giya: Idan mutum yana shan giya, to zai iya kamuwa
    • Shan taba sigari.
    • Jinsin baƙar fata: idan mutum shi baƙi ne (ɗan Afrika), to zai iya kamuwa da hawan jini.
    • Ciwon suga (diabetes)
    • Ƙiba.
    • Shekaru sama da 40.
    Abin da yake janyo secondary hypertension.
    • Ciwon ƙoda
    • Juna biyu (pregnancy)
    • Ciwon zuciya
    • Shan giya
    • Shan wasu ƙwayoyi kamar ‘Steroids’ da sauransu
    Alamomin hawan jini

    A mafi yawanci lokaci, hawan jini ba ya nuna wasu alamomi sai dai idan ya haifar, ko kuma ya fara haifar da matsala. Wannan dalilin ne ya sa ake kiran hawan jini da ‘Silent Killer’

    Matsaloli ko kuma illoli da hawan jini yake haifarwa
    • Cutar shanyewar ɓarin jiki (stroke)
    • Ciwon zuciya
    • Ciwon ƙoda
    • Matsalolin ido
    • Mutuwar farar ɗaya da sauransu
     Abubuwan Masu Muhimmanci

    A sani cewa, lokacin da jinin mutum ya hau ko kuma yake hawa, ba lallai ne mutum ya ji wata alama ta rashin lafiya ba. Shi yasa ake cewa hawan jini ‘Silent Killer’ ma’ana ‘mai kisa ba tare da an sani ba‛

    Don haka yana da kyau mutum ya dinga zuwa ana duba masa BP ɗinsa lokaci zuwa lokaci

    Maganin hawan jini

    A likitance, babu wani magani guda ɗaya wanda idan mutum ya yi amfani da shi zai warke daga hawan jini, musamman ‘primary hypertension‛.

    Amma idan mutum yana da ‘secondary hypertension‛ to zai iya samun waraka idan aka yi maganin abin da ya janyo masa hawan jinin.

    Magungunan hawan jini, suna daidaita ‘BP‛ ne amma ba sa warkar da hawan jinin. Shi yasa ake shan maganin a kowace rana muddun mutum yana da rai.

    Idan mutum ya daina shan maganin ba tare da shawarar likita ba, to jinin nasa zai iya ci gaba da hawa kuma ya haddasa masa matsalolin da aka lissafa a baya.

    Shawarwari
    • A rage gishiri a abinci: gishiri ya kasance ɗan kaɗan, sannan kuma a daina barbaɗa gishiri a abinci
    • A daina shan taba sigari
    • A daina shan giya
    • A rage amfani da kayan da suke ƙarawa miya zaƙi, sai wanda likita ya bada shawara. A daina shan magunguna barkatai ba tare da shawarar likita ba
    • A yawaita motsa jiki
    • A rage ƙiba ta hanyar motsa jiki da kula da abinci
    • A rika zuwa wurin likita lokaci zuwa lokaci domin duba BP
    Kammalawa

    Mutane masu hawan jini suna da yawa a cikin al’ummarmu, kuma yana janyo illoli da suke da wahalar magani. Idan mutum yana shan magani, kuma yana bin dokokin likita, to zai iya samun sauƙi ko kuma kariya daga Waɗannan matsaloli.

  • Yadda Ake Gyaran Jiki Ya Yi Laushi Kuma Ya Yi Kyau

    Yadda Ake Gyaran Jiki Ya Yi Laushi Kuma Ya Yi Kyau

    Gyaran jiki yana taimaka wa Namiji ko Mace ta daɗe tana more jikinta. Fatar mutum ta zama lafiyayya, kuma abin sha’awa. Shi ne za ka ga mace komai yawan shekarunta, haka komai yawan haihuwarta, Tana da kyakkyawan jiki.

    Gyaran jiki ya samo asali ne daga wajen Larabawa. Sai Barebari wato daga Maiduguri, a nan Ƙasar NIjeriya. Haka ma Turawa sun yi mayuka kala-kala domin gyara fata.
    Sai dai duk Sanda mutum yake so zai dinga gyara jiki. To ya zama tilas ya kula da mafi muhimmanci, wato ya bi matakai na gyara jiki.

    MATAKAN GYARAN JIKI:

    1 – Cin lafiyyen abinci.
    2 – Yawan Shan ruwa .
    3 – Yawan Cin ‘ya’yan itatuwa.
    4 – Atitsaye ( motsa jiki) .
    5 – Amfani da kayan gyaran jiki ( Dilka).

    GYARAN JIKI NA DILKA:

    Za a zuba Dilka a cikin mazubi. Sai a zuba masa ruwan zafi. Bayan jimawa sai a zuba kurkum, da mai zaitun , da ƙwai .
    Sai a ƙara ruwa ɗan dai-dai. A shafe dukkan jiki har fuska. Idan ya bushe sai a murje jiki da shi.

    GYARAN JIKI NA ALKAMA:

    Za a niƙa Alkama ne, a tankaɗe ta, tai luƙwui. Sai a soya ta kamar yadda ake idan za a yi kunun alkama.
    Za a zuba wa soyayyiyar alkama yis. A zuba ruwa a kwaɓa ta. A shafe duk jiki da ita. Bayan ɗan lokaci, sai a dinga murje jiki ko’ina.

    GYARAN JIKI NA KHALDA ( OATS):

    Za a zuba wa khalda (Oats) madara. Sai kuma a matsa lemon tsami kaɗan. A juya shi a kwaɓa sosai. Sai a shafa amma shi duk jiki. Bayan ɗan lokaci sai a murje duk jiki.
    A ƙarshe, lallai akwai buƙatar mu dinga waiwayar gyaran jikinmu, duk sati in da hali. Ko kuma duk Wata. Ya danganta da yadda ake da hali, lokaci da himma.
    Duba yadda ake ado da kwalliya ta Musamman.
    Litattafai da aka duba
    Amina Mar’atussaliha
  • Yadda Ake Wa Mai Gida A Lokacin Al’ada

    Yadda Ake Wa Mai Gida A Lokacin Al’ada

    Akwai wasu lokuta da Ma’aurata ke shiga damuwa sosai. Kaɗaici na addabar su sabo da larura ta rashin lafiya, da juna biyu, da haihuwa ko jinin al’ada.

    Mazaje da yawa na ƙyama da ƙaurace wa matayensu. Har sai mace ta gama jinin al’ada. To yin hakan kuskure ne babba.

    Haƙiƙa Allah (S.A.W) Ya hana miji ya sadu da Matarsa alhali tana haila. Amma ba a hana ya sumbace ta ba, da haɗa jiki da ita ko yin wasa da ita ba.

    Mazaje su yi nazari na wannan ingantacce Hadisi. Domin koyi da Annabi ( S. A. W).

    A’isha (RA) ta ce :” Ya kasance yana umarta ta da in yi ƙunzugu, sai ya yi mubashara da ni alhali ina jinin haila “.
    (Bukhari da Muslim).
    Wasu mata kuma su ne ba sa kulawa da sha’awar mazajensu, a irin wannan hali. Suna ɗauka cewa a dole babu dama da za a iya komai.
    Wasu ƙarni na jini ne. Ba sa ƙoƙarin tsafta da amfani da turare. Shi ke sa wa miji ya yi nesa da matarsa.
    Miji dai ba shi da wacce ta fi matarsa. A koyaushe ita ce wacce zai huta da ita. Domin samun natsuwa da kwanciyar hankali. Saboda haka, za ka taimaka mata da abubuwa buƙatun ta. Irinsu turare kala-kala, da turaren wuta , da wanduna, auduga da dai Sauransu.
    Mace ma ba ta da abin tattali da kuma inda za tai shagwaɓa kamar mijinta.

    Amma fa dole sai Mace ta fara kulawa da kanta. Sannan miji ya samu sakata ya wala.

    HANYOYIN DA MACE ZA TA KULA DA KANTA A LOKACIN JININ AL’ADA
    1 – Aske mara akai-akai.
    2 – Wanka sau 2/3 a rana.
    3 – Canja wando da ɗan tofi.
    4 – Canja Auduga 4 a rana. Duk da cewa ya danganta da yanayin al’adar mace.
    5 – Wanka humra da turaren wuta na jiki.
    6 – Kulawa da yin azkaar na safiya da maraice.
    Babu tunani a ce ke kaɗai a wajen mijinki. Kuma ba kya damuwa da halin da zai shiga. Tun samu ciki har sai arba’in.

    Mace sai ta lura da irin yanayi mijinta. Yadda sauƙi ko ƙarfin bukatarsa take.

    Idan mace na jinin haila ko na biki. Kuma mijinki na cikin sha’awar ki. Mace za ta yi ƙunzugu. Ta kuma yi wa mijinta wasanni . Ya ji daɗi da ita, ba tare da ya keta Shari’a ba ( ba saduwa).

    A taƙaice akan so ma’aurata su kula da juna a kowanne irin yanayi. domin sanin yadda za ki mayar da kidanki masarautarki danna kuren rubutun nan

    Litattafai da aka duba: Aure A Musulunci

  • Hanyoyi 11 Da Ake Rage Ƙiba Ba Tare Da An Kashe Ko Sisi Ba.

    Hanyoyi 11 Da Ake Rage Ƙiba Ba Tare Da An Kashe Ko Sisi Ba.

    1. Ka tabbatar ka karya kumallo a kowacce rana, domin ƙin karin kumallo ba zai taimaka maka wajen rage ƙiba ba, sai dai ma ya hana ka samun kuzari a tsawon ranar da ba ka yi karin kumallon ba.

    2. Ka ci abinci na yau da kullum. Domin hakan yana taimakawa wajen ƙone sinadarin (calories) a cikin sauri a lokutan da rana ta take.

    3. Ka ci ‘ya’yan itace da ganyayyaki a mafi yawan lokaci, domin ‘Ya’yan itace da ganyayyaki suna da ƙarancin sinadarin ƙiba wato (fat).

    4. Ka ƙara yawan motsa jiki ko ayyukan da kake yi na yau da kullum.

    5. Ka sha ruwa mai yawa, kuma ka da ka bar kishirwa a tare da Kai.

    6. Ku ci abincin dake ƙunshe da (fiber) mai yawa, hakan zai taimaka maka jin ƙoshin lafiya, da rage maka teba da rage nauyi. Ana samun fiber a cikin abinci daga tsirrai, irin su ‘ya’yan itace da ganyayyaki, hatsi, da shinkafa da taliya, da wake.

    7. Ka guji cika cikinka da abinci, a maimakon haka, sai ka rinƙa haƙura da abincin kafin ka ji ka ƙoshi. Domin ciki na ɗaukar kimanin mintuna 20 kafin ya gayawa ƙwaƙwalwa ya ƙoshi.

    8. Kada ka haramta wa kanka abincin da kake so, a maimakon haka, kawai sai ka rage yawan cin sa.

    9. Ka musanya cin kayan kwalam da maƙulashe ya zuwa cin ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki.

    10. Ka guji sha ko cin abin dake da sinadarin giya a ciki.

    11. Ka tsara wa kanka lokacin cin abici.

  • Yadda Za ki Kare Kanki Daga Ciwon Sanyi (Toilet Infection)

    Yadda Za ki Kare Kanki Daga Ciwon Sanyi (Toilet Infection)

    Cikakken bayanin ciwon sanyi daga likitan Asibitin Murtala Muhammad Special Hospital, Kano. Dr Adam Bala Husaini

    Mutane da yawa, musamman mata, suna fama da yawan fitar da ruwa daga al’aurarsu. Wannan fitar ruwan yana iya kasancewa na cuta ko kuma wanda ba na cuta ko rashin lafiya ba. Mata sun fi yawan samun kansu a wannan yanayi na fitar ruwa daga mafitsararsu fiye da maza. Wannan bayanin da zan yi, zan fi karkata a kan mata.
    Yanayin yadda Allah (SWT) ya yi cikin al’aurar mace shi ne, ya kasance a jiƙe (mai danshi-danshi) a kowane lokaci. Ruwan da yake jiƙa a gaban mace yana fitawo ne daga wasu ɓangarori daban-daban da suke cikin gaban nata. Yawan ruwa yana iya ƙaruwa, raguwa ko kuma yana ɗauke gaba ɗaya. Zan yi bayani a kan ƙaruwar ruwa.
    Wannan zubar ruwa ana kiransa “vaginal discharge” a likitance. Hausawa suna kiransa da “ciwon sanyi”, wasu kuma suna kiransa da “toilet infection (ma’ana, cutar da ake ɗauka a banɗaki maras tsafta)”. Ya kamata a sani cewa, har yanzu, a likitance, ba a tabbatar da cewa yin amfani da banɗaki marar tsafta yana ɗaya daga cikin hanyar da ake kamuwa da wannan cutar zubar da ruwan ba, amma dai ana zargin hakan, kuma ya kamata a yawaita tsaftace banɗaki.

    ME YAKE JANYO YAWAN ZUBAR DA RUWAN
    Kamar yadda na faɗa a baya, shi yawan zubar da ruwan zai iya kasancewa na cuta ko kuma wanda ba na cuta ba.
    Abubuwan da suke janyo zubar da ruwa na cuta sun haɗa da:
    1. Juna biyu (ciki): Amma fa wani lokacin, juna biyu yana iya janyo zubar ruwa na cuta.
    2. Yin amfani da ƙwayoyin tsarin iyali.
    3. Lokacin jinin al’ada
    Abubuwan da suke janyo zubar ruwa na cuta sun haɗa da:
    1. Shan magunguna barkatai, musamman waɗanda ake kira da Antibiotics ko Steroid da sauran su.
    2. Cututtuka a jiki kamar Diabetes (ciwon suga), HIV, Cancer da sauransu
    3. Juna biyu (ciki): yana iya janyo zubar ruwa na rashin lafiya da kuma wanda ba na rashin lafiya ba.
    4. Saduwa da wanda yake ɗauke da cutar: namiji zai iya dauka daga wurin mace, sannan mace ma za ta iya dauka daga wurin namiji
    5. Zinace-zinace
    6. Yawan wanke cikin gaba da wani sinadari (vaginal douching)
    7. Masan tangaran (toilet seats): musamman idan wadda take dauke da cutar ta yi amfani da shi kuma ba ta wanke masan ba. Amma fa har yanzu ba a tabbatar da wannan hanyar ba.
    Idan mace tana da, ko kuma, tana aikata ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan, to za ta iya kamuwa da wannan cuta ta zubar da ruwa.
    YADDA AKE GANE ZUBAR RUWA NA CUTA
    1. Idan ruwan yana da ɗaya daga cikin waɗannan siffofin:
    • Ya kasance yana Wari ko ƙarni
    • Launinsa ya kasance ruwan ɗorawa (yellow) ko ruwan toka ko kuma kore.
    • Yanayinsa ya kasance kamar dusar awara ko kuma kamar zare
    2. Kaikayin gaba
    3. Jin zafi lokacin saduwa (jima’i)
    HANYAR KARIYA DAGA KAMUWA DAGA WANNAN CUTA
    1. A daina amfani da magunguna barkatai, ba tare da shawarar likita ba, musamman waɗanda ake kira da antibiotics da kuma steroid.
    2. A ƙauracewa zinace-zinace
    3. A daina tura ko kuma zura wani abu a cikin gaba (al’aura)
    4. Wadda take da cutar, ta je ta nemi magani a asibiti saboda ka da ta shafawa wani ko wata.
    KAMMALAWA
    Zubar ruwa daga gaban mace yana damun mata kwarai da gaske, amma ba kowanne ba ne yake na cuta ba. Idan na cutar ne kuma, ana iya warkewa idan an sha magani. Kuma har yanzu, a likitance, ba a tabbatar da cewa ana ɗaukar cutar a banɗaki ba.
    Allah ya ƙara mana lafiya da zama lafiya da ilmi mai amfani.
    Allah shi ne mafi sani.

    Za ku iya turawa da tambayarku ta hanyar wajen tura sako dake ƙasan rubutun nan ko kuma danna koren rubutun nan

    Dr. Adam Bala Husaini
    Murtala Muhammad Spacial Hospital, kano