Asalin Yawon Bundi Ko Ƙaura Wurin Makaranta

0
498

Yawon bundi al’ada ce sananniya wajen ma’abota tsangaya. Ana kiran almajirai waɗanda ke tashi daga garuruwansu na haihuwa zuwa wasu sassa da sunan ‘yan yawon bundi, ko kuma almajiran kwargo.

Makaranta na fita da almajiransu don zuwa wajen mashahuran malamai ko tsangayu don Neman karatu. A wani lokaci ma don neman ƙasar noma, musamman idan wurin da suke babu irin yanayin da zai taimakawa karatunsu. Da ma dai kalmar almajiri ta samo asalin ne daga Almuhajir, ma’ana mai ƙaura. Kamar dai yadda Sahabbai (Radiyallahu Anhuma) suka bar Makka ya zuwa Madina, har ake kiran su Almuhajirun.

A wasu sassa na ƙasar nan, ana kiran su almajirai ne saboda suna yawo da ƙirgi ko buzu. Sannan kuma suna cin abinci a ƙwarya ko kwacciya kamar yadda baƙo ya ke yi. Babban dalili ko asalin yawon bundi wurin makaranta shi ne; rashin gwamnati makamanciyar gwamnatin Sayyadina Umar (Radiyallahu Anhu) wadda za ta ɗauki nauyin rayuwarsu. A ƙasashe Irin su Sudan da Libiya da Mauritaniya; makaranta a tsangaya ba sa ƙaura daga gari zuwa gari, kamar yadda muke gani a nan Nijeriya. Dalili kuwa shi ne galibin su suna samun taimako mai gwaɓi daga gwamnatocinsu da mawadatansu da al’ummarsu.

A taƙaice dai yawon bundi ko ƙaurar malamai da almajirai daga gari zuwa gari, al’ada ce da ta keɓanci makaranta a tsangayun Najeriya; da wani yanki na Jamhuriyoyin Nijar da Chadi, saboda dalilan da suka gabata a wannan babi da kuma babi na huɗu a sashe na ɗaya; mai bayani kan birane da garuruwan da suka shahara da tsangayu a Arewacin Najeriya.

Domin karanta cikakken bayani a kan Hausar Gardawa danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Kayan Karatu A Tsangaya danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceAsalin Tsibbu A Tsangayun Alƙur’ani
Labarin na GabaAzuzuwa Da Kashe-kashen Makaranta A Tsangaya