Abubuwan Dake Sa Kishiyoyi Shiri da Zaman Lafiya.

0
537

Haƙuri da kau da kai game da kurakuren kishiya, shi ne mafi girman abubuwan da suke wanzar da zaman lafiya ts aakanin kishiyoyi. Ga abin da Allah (Subhanahu wata’ala) ya ce: a game da muhimmancin haƙuri.

Ma’ana “Kayi hakuri kan duk abinda ya same ka, haƙiƙa yin hakan na daga cikin muhimman al’amura”
Watsi da tsegunguma tare da nisantar munanan zato marasa dalilai game da kishiya, shi ma yana daga cikin abubuwan da suke inganta zamantakewar kishiyoyi, kuma dimantar kulawarmu, wanda hakan shi zai ba mu damar aiki da tarbiyyar da addininmu ya ɗora mu a kai, ta kyautata wa junanmu zato. Allah Ta’ala ya ce:
Ma’ana “Ina ma dai lokacin da ku ka ji (mummunan zaton da aka yi wa A’isha) muminai maza da muminai mata sun zatar wa kawunansu alheri, kuma su ce wannan ai ƙage ne bayyanan ne”.
Kuma an karɓo hadisi daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Na hana ku mummunan zato, haƙiƙa, mummunan zato shi ne mafi ƙaryar zance”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Kyautata wa kishiya da kuma mai da komai ba komai ba , dalili ne ƙwaƙƙwara da yake tabbatar da zaman lafiya tsakanin kishiyoyi.
Imamul Bukhari da Muslim sun rawaici hadisi da aka karɓo daga A’isha Allah ya yarda da ita ta ce: “Yayin da sauda ‘yar zam’a (matar Annabi) ta manyanta ta bai wa  Nana A’isha ranar kwananta, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya zama yana raba wa A’isha kwanan Sauda. (ƙari a kan nata kwanan). Wannan kyakkyawan misali ne da yake sanar da matanmu yadda ya kamata su zauna da kishiyoyinsu.

Domin karanta cikakken bayani a kan Duhun Kan Mace Mai Gaba Da Kishiya danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Duhun Kai Gaba Da Kishiya wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceDuhun Kan Mace Mai Gaba da Kisihiya.
Labarin na GabaShin ko ya Halatta A Je Wajen Boka Ko Ɗan tsubbu Domin Sihirce Kishiya?