Abubuwan Da Ke Haddasa Yawan Zubewar Juna Biyu

0
111

Yawan yin ɓarin juna biyun da bai kai makwanni 20 ba, babu zato ba tsammani, shi ne ake kira “spontaneous abortion” a likitance. Abubuwan da suke iya haifar da shi su ne:

  1. Nakasa A jikin Jariri (Fetal Genetic Abnormalities): idan za a haifi jariri da wata nakasa, to, cikin hukuncin Allah SWT, sai cikin ya zube tun kafin a haife shi. Wannan hikimar Allah SWT ce, ma’ana maimakon a haife shi ya rayu cikin wahala, kuma iyayensa cikin wahala, sai a yi barinsa kawai. Binciken kimiyya na asibiti ya tabbatar da cewa kaso 50% na ɓarin da mata suke yi, abinda yake haddasa shi kenan.

2. Kamuwar Mai Juna Biyu Da Cututtuka (Maternal Health Conditions): Cututtuka masu ƙarfi, kamar ciwon sugar (diabetes), ko cututtukan jakar sinadarin thyroid (thyroid gland disorders), ko ko hawan jini (hypertension), da sauransu, suna haddasa yin ɓarin juna biyu, matuƙar ba a ɗauki matakin gaggawa na magance su ba.

Sa’annan kamuwa da ƙwayoyin cututtukan numfashi na rubella, ko cutar garkuwar jiki ta cytomegalovirus, ko cutar mu’amala da gurɓataccen abinci ta listeria. Bayan haka, rashin daidaiton zubar ruwan sinadarai a cikin jikin mace zai iya haifar da ɓarin juna biyu, kamar polycystic ovary syndrome (PCOS) da matsalar rashin ƙarfin bangon mahaifa na luteal phase defects duk suna iya haddasa yin ɓarin juna biyu.

3.Tsarin rayuwa (Lifestyle Factors): yin ɗabi’ar shan taba (cigarette smoking), ko shan giya (alcoholism), ko ƙiba wacce ta wuce misali (obesity), suna iya haifar da yin ɓari.

4. Shekaru (Age): matan da suka kai shekaru 35 a rayuwarsu, sun fi hatsarin yin ɓarin juna biyu idan suka samu ciki, saboda akwai yiwuwar kwayoyin halittar jariransu suna iya samun nakasa (fetal chromosomes defects).

5. Matsalolin Mahaifa Da Bakin Mahaifa (Uterine or Cervical Issues): cututtuka kamar ƙarin mahaifa (uterine fibroids), ko zazzagowar mahaifa (uterine polyps), ko rabewar mahaifa gida biyu (septate uterus), za su iya haddasa yin ɓari. Hakan rashin rufewar bakin mahaifa yadda ya kamata (cervical insufficiency).

6. Matsalolin Rashin Ƙarfin Garkuwar Jiki (Immune System Disorders): matsalar garkuwar jiki mai haddasa daskarewar jini  (antiphospholipid syndrome), za ta iya haifar da yin ɓari.

7. Matsalolin Muhalli (Environmental Factors): idan mai juna biyu tana zama a cikin muhallin da ya gurbace da warin hayaƙi, ko sinadaran chemicals, ko hasken radiation, ko ƙura da iska mai guba, to, hakan zai iya haifar mata da yin ɓari.

8. Bugewa a Ciki (Physical Trauma): idan mace ta buge a ciki sakamakon faɗuwa, ko rauni, ko tsautsayin duka, za ta iya fuskantar yin ɓari.

Danna nan don karanta Awon Juna Biyu

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceZinariyar Awa Ga Jariran Mu
Labarin na GabaKafar Sadarwar Zamani, Amfani da ƙalubalenta 2