Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya (2006:374), ta bayyana roƙo da cewa; “Sana’ar maroƙa ta yi wa mutane kirari ko yabo don a yi musu kyauta” Ko kuwa, “Neman kyauta daga wani”.
Kenan roƙo, wata dabara ce ta neman abu a hannun wani ta hanyar zuga shi da yi masa kirari da yabon kyawawan halayensa; a wani lokacin ma da ƙoƙarin ƙarin gishiri kan halin da ba nasa ba.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Wayon Roƙo a Adabin Baka; Nazarin Roƙo a Wasu Waƙoƙin Kamilu Almajirin Mawaƙa wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.
Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Kamilu Almajirin Mawaƙa danna nan
Domin karanta bayani akan Kasuwanci Da Fatauci A Ƙasar Hausa danna nan








![Ciwon Kai Na Gado Wato [Migraine] Ciwon Kai Na Gado Wato [Migraine]](https://wikihausa.com.ng/wp-content/uploads/2024/05/Ciwon-Kai-Na-Gado-Wato-Migraine-100x70.jpg)

