Ratiban Nafiloli

0
660

Waɗannan nafiloli sune waɗanda ake yin su kafin ko bayan sallolin farilla; raka’o’insu goma ne ko sha biyu; ga yadda tsarin su yake :Raka’a biyu kafin Sallar Azahar ko raka’a huɗu bayan Sallar Azahar, raka’a Magariba raka’a biyu bayan Isha’I da raka’a biyu kafin Sallar Asuba waɗannan sunnoni ne masu karfi sosai.

Falalarsu

Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: “Duk wanda ya sallaci raka’a goma sha biyu a yini da dare, za’a gina masa gida a aljanna saboda su.” Ummu Habiba ta ce tun da na ji wanna daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) bai taɓa barinsu ba.” (Musulmi 728, Tirmizi 415, Abu Dawud 1250).

Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Raka’atil Fajr danna nan.

Wannan bayani anciro shine daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceNafilolin Sallah.
Labarin na GabaFalalar Raka’ Atil Fajr.