Abubuwan Dake Jawo Asarar Lokaci A Rayuwar Ɗan Adam

0
1117

Abubuwan Dake Jawo Asarar Lokaci A Rayuwar Ɗan Adam suna da yawa.

RAFKANA: Rafkana wata cuta ce dake kama zuciyar ɗan Adam, ta kuma raunana hankalinsa. Ta yadda zai rasa wattsakewa cikin cikakken hankali irin na mai tunani. Hatta kai bai iya tantance me ke zuwa,  ko kuma bambance abu mai amfani da mara amfani ba. Rafkanannen mutum, ba ya iya rarrabe al’amura da yadda ƙarshen su za su kasance. Shi dai kullum mutum ne kawai a gangar jiki amma ba a haƙiƙa ba.

Ubangiji Maɗaukaki ya nuna mana mece ce rafkana, kuma su wane ne rafkanannu inda yake cewa: “Haƙiƙa mun halitta wa jahannama da yawa daga aljanu da mutane (waɗanda) ke da zuƙatan da ba sa ganewa, kuma suna da idanuwa da ba sa gani da su, kuma suna da kunnuwan da ba sa ji da su. Waɗannan tamkar dabbobi suke har ma sun fi (dabbobi) ɓata, waɗannan su ne Rafkanannu”. Suratul-Aaraf :179

Rafkana ita ce babban dalilin dake sanya ɗan Adam ya yi asarar rayuwarsa ba tare da ya amfane ta ba. Misali a nan shi ne, ka ga mai arziki ya tsufa yana gani abokansa da sana’oinsa duk sun rasu, amma shi ya kasa fitar da dukiyarsa don neman yardar Ubangiji Maɗaukaki. Har sai mutuwa ta zo ta banke shi, kuma ya bar duniyar ba tare da ya mori dukiyar ba. Haka kuma rafkana ke sa ayyukan saɓo ke ci gaba har mutuwa ta riske shi ba tare da ya tuba ba.

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Abubuwan da ke Jawo Asarar Lokaci A Rayuwar Ɗan Adam sun haɗa da:-

Kallon Talabijin da Fina-Finai

Yara suna cinye lokutansu gaban akwatin talabijin fiye da lokacin da suke yi a gaban malamansu. Kallon fina-finai yana da matuƙar haɗari ga lafiyar ‘ya’ya da tarbiyarsu. Taurarin fina-finai sun fi soyuwa ga masu kallo, fiye da duk wani abu na ibada.

Da za a ƙididdige yawan awoyin da matan aure da ‘ya’yansu da samari da ‘yanmata da magidanta suke asara a gaban talabijin, da za a ga cewa kusan a yau 3/5 na lokutan rayuwarsu na tafiya ne wajen kallo da asara lokaci.

Domin kuwa kafafen yaɗa labarai na kasashen waje ba sa rufe tashoshinsu tsawon awanni ashirin da hudu. Ga fina-finai nan kullum sai sababbi ke fitowa. Kada dai mu manta kowannenmu zai amsa wa Ubangiji Maɗaukaki ta yadda ya ƙarar da rayuwarsa.

Hukuncin Kallon Talabijin Da Fina-Finai:

Idan aka kau da ido daga irin asarar da mutum ke yi a sababin kallon talabijin da fina-finai, sai mu ga shin mene ne hukuncin kallonta ne a Musulunci?

Hukuncin kallon talabijin da fina-finai na komawa ga hukuncin abin da ake gani a cikin akwatin talabijin. Idan dai kallon matar da ba muharrama ba haramun ne a fili, ko kan hanya to babu kuwa yadda za a ƙura mata ido cikin talabijin kuma ya zama halal?. Ubangiji Maɗaukaki na cewa:

“Ka faɗa wa muminai maza su runtse ganinsu kuma su kiyaye al’aurarsu, kuma ka faɗawa muminai mata, su runtse ganinsu kuma su kiyaye al’aurarsu. “Sura Nur-aya

Domin Karanta Cikakken Bayanin Abubuwan Da Sai Da Su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe Danna Nan

Nisa’i ya ruwaito Hadisi cewa dangogin mutane uku ba za su shiga Aljanna ba (Ɗabarani ya ce ba za su taɓa shiga aljanna ba”)

    • Mai saɓawa iyaye
    • Dayyus
    • Mai kwaikwayon mata

Dayyus shi ne mutumin da bai damu da kamewar ko rashin kamewar matarsa ko ‘yarsa ko ‘yar’uwarsa ko mahaifiyarsa ba. Dayyus ba ya damuwa in an ga maharramarsa tana yawo babu hijabi ko kuma tana cuɗanya da waɗanda bai halatta ta yi cuɗanya da su a shar’ance ba.

Ko kuma tana kallon mazaje daban-daban cikin fina-finai. Dayyus ba ya damuwa muharramarsa ta ƙosar da sha’awar masu fasadi da adonta da muryarta, ballatana ma ya yi kishin ‘yayan wasu ko matansu.

Wasan Ƙwallo Da Kallonsa

Babu shakka yin wasan ƙwallo da kallonsa na ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo asarar lokacin rayuwar musulmi a duniya. Kullum kamar ba su da wani batu na tattaunawa sama da na taurarin ‘yan wasa a Turai da ƙasashen duniya. Sai kuma batun sababbin kwafa-kwafai da za a ci wasanni daban-daban cikin shekaru masu zuwa.

Da yawan hankalin masu hankali ya ɓace. Waɗanda ko ba su samu cikakken hankalin ba sun ƙara shigewa daji.Irin waɗannan mutane kan bar komai don ganin yadda za a ƙarke da ‘yan wasan Ingila ko na Brazil, kuma daloli nawa Rooney ya samu. Wane kulob Mikel yake.

Shin Mene ne Hukuncin Wasan Ƙwallo Da Kallonsa A Musulunci?

Motsa jiki ba laifi ba ne a Musulunci. To amma fa dole ya dace da kowace ƙa’ida da Musulunci ya gindaya. Kamar yadda mai cin abinci ba zai ci da hannun hagu ba, don kawai Musulunci ya ce “Ku ci, ku sha”. To haka mai motsa jikinsa ba zai keta iyakokin Ubangiji Maɗaukaki da sunan motsa jiki ba.

“Wasan Ƙwallo dai ba wani abu ba ne, face bayyana cinyoyi da al’aura tare da tozarta lokutan sallah, da cusa ƙaunar maƙiyan Allah da Manzonsa cikin zukatan juna don cimma manufofinJ F LV  duniya da kuma samun nishadi da annashuwa a harbar dandalin shaiɗan”. Idan har mai da’awar halaccin motsa jiki a musulunci.

Abin tambaya a nan shi ne; yaya zai yi hukuncin son maƙiyan Allah Maɗaukaki da Manzonsa? Wanda wannan wani sharaɗi ne a. Ma’ana ba za a so maƙiyin Allah Maɗaukaki ko manzonsa ba koda kuwa iyaye ne ko ‘ya’yaye ko ‘yan’uwa.

Shin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) ko ƙungiyar wasanni na ƙasashe zasu amince musulumi su rufe cinyoyinsu ma’ana su rufe al’aura kamar yadda Musulunci ya shar’anta?
Yaya za a shawo kan matsalar sanya jadawalin yin wasanni daidai lokutan sallah? Ko kuwa babu komai uzurin ne wurin Ubangiji Maɗaukaki?

A ganina da za a lamunce wa Musulmi waɗannan matsaloli, da haɗarin wasan ƙwallo ya sassauta, su kuwa masu kallo da talabijin ya kamata su amsa tambayoyi masu zuwa:
Wace amsa za su ba wa Ubangiji Maɗaukaki ranar ƙiyama in ya tambaye su awoyin da suka narkar wajen kallon mutane cikin tsiraici ga kuma tozarta lokutan Sallah.

Yaya za su yi da irin soyayyar da suke nuna wa ga Beckham da Bergio da Messi da sauran su, alhali su ba su ɗauki Annabinmu ba a bakin komai ba?

Ubangiji Maɗaukaki na cewa ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku riƙi maƙiyana kuma maƙiyanku masoya, kuna jefa soyayya zuwa gare su, alhali kuwa sun kafirta da abin da kuka ɓoye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to lallai ya ɓace daga taskar hanya (hanya madaidaiciya). Sura Mumtahana-Aya:1.

Jin Kiɗa

Da yawa musulmi musamman matasa suna asarar lokutan rayuwarsu wajen sauraren kiɗe-kiɗe. Ta kai ta kawo akwai ‘yan ƙananan recorda da rediyo da aka fiya sauraro, maimakon ambaton Allah Maɗaukaki.

Asarar lokaci ta hanyar jin kiɗe-kiɗe ba ta tsaya ga samari ba. A yau harda manyan ofisoshi da ƙanana a bankuna da “Wuraren aiki, za ka ga suna kai rediyoyinsu tashar FM, ba don wani abu ba, sai don a yayyafawa zuƙatansu ruwan mugunyar disko mai sanyi da kwantar da zuciyar gafalallu.

Wani abin mamaki shi ne, irin yadda mutane ke sanyawa wayar tafi-da-gidanka (GSM) disko, wanda ke janyo wasu illoli ga imani.

Wanda da karatun Alkur’ani suka sa ko ambaton Allah, da an rubuta lada a gare su. Kar dai ku manta cewa ji da gani da zuciyar mutum abin tambaya ne game da su a ranar Alƙiyama.

Hukuncin Kiɗa A Musulunci.

Bukhari ya ruwaito hadisi daga Malik cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya ce… … “Za a yi wasu mutane daga al’ummata da za su riƙa halatta zina da alharini da giya da kiɗa”. An ruwaito Sayyidina Abubakar (R.A) na cewa kiɗa na tsirar da munafunci a cikin zuciya.

Abdullahi bn Mas’ud ya fassara faɗin Ubangiji Maɗaukaki… … daga cikin mutane akwai masu sayen yasasshen zance don ya ɓatar a barin hanyar Allah (Maɗaukaki) da cewa shi ne kiɗa.

Karta Da Ludo Da Dara

Da yawan mutane na buɗe wuraren hira da majalisai, musamman bayan dawowa daga kasuwa ko wuraren aiki da yamma. Babbar hanyar ɗebe kewarsu ita ce wassan karta ko ludo ko dara.

Irin waɗannan mutane kan kwashe awowi masu yawa suna sakaci ana hayaniya, kai ka ce yara ne ƙanana da ba su san lissafin numfashinsu kullum ƙasa yake yi ba.

‘Yan karta ko ‘yan dara kan cinye dare, ba tare da sun ƙosa ba. Kuma mafi yawansu ba sa ware ko minti talatin domin sanin yadda za su bauta wa mahaliccinsu.

Yawan Hira Da Zantuka Barkatai

Galibin mutane a yau, kan yi hirar awowi masu yawa ko kan siyasa a majalisai ba tare da fa’ida ba. yadda wannan na gadarwa da mutum asarar ba da za lissafu ba.

Domin karanta cikakken bayani akan Abubuwan da zasu taimakawa mutum wajen tsara lokacinsa, karka raina minti ɗaya danna koren rubutun nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Lokaci A Rayuwar Musulmi Tsakanin Riba Da Asara wanda Sunusi Iguda Ƙofar Nasarawa ya wallafa shi.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna Nan 

labarin da ya wuceYadda Ake Yin Sabulun Wanki
Labarin na GabaRashin Lafiyar Bayin Allah