A yau za mu koyi Yadda Ake Miyar Karkashi Da Kubewa
Miyar karkashi da kuɓewa na da matukar daɗi da kuma amfani a jikin ɗan Adam, tana da matukar amfani musamman ma a wajen masu ciwon suga da kuma ƙarin jini ga marasa jini wato (anemic patients) dama wasu amfanin da dama. Yana da kyau a ƙalla ko sau ɗaya a sati mutum ya ci ta, amma idan ya tabbatar ya cika ta da nama
Abubuwan da ake buƙata
-
Ganyen karkashi
-
Kuɓewa ɗanya
-
Tokar miya ko kanwa
-
Attaruhu
-
Bandar kifi
-
Nama
-
Albasa
-
Ɗanyar tafarnuwa
-
Garin citta
-
Magi
Yadda ake haɗawa
- A kakkabe ganyen karkashin tsaf, sannan a yayyanka shi ƙanana sosai.
- A samu kuɓewa ɗanya, a yayyanka ta, sannan a saka a turmi a daka ta, ta yi laushi sosai.
- In kuma da kanwa za a yi miyar, sai a daka tare da kanwa kaɗan.
- Sannan a kwashe a ajiye a gefe, A daka attaruhu da tafarnuwa sannan a kwashe.
- A wanke bandar kifi da ruwan ɗumi, a cire ƙayoyin sannan a yayyanka albasa ƙanana.
- A ɗaura ruwa a tukunya sannan a tafasa nama har sai ya yi laushi.
- Sai a kara ruwa kaɗan a kan romon naman, sannan a zuba yankakkiyar albasar da jajjagaggen attaruhu da garin citta da bandar kifi har sai sun tafasa. Sannan a ɗauko kubewar da aka daka a zuba a riƙa gaurayawa har sai ta fara nuna.
- Sannan a ɗauki karkashin a zuba a dauki maburgi a buga, sannan a cigaba da juyawa.
- Idan har ba a sanya kanwa a miyar ba, a wannan lokacin ya kamata a sanya tokar miyar sannan a jiƙa magi ya narke, a zuba sai a cigaba da gaurayawa har sai ɗanɗanon ya fito sannan a sauke.