Yadda Ake Madarar Youghurt
Abubawan da ake bukata
- Madara kofi huɗu
- Ruwa kofi huɗu
- Sukari kofi
- Flavor mai ƙamshin madara cikin cokali.
- Corn starch kofi ɗaya
- Culture rabin cokali
Yadda ake hadawa:
-
Da farko za a kwaɓa madarar (ta gari) da sukari da corn starch sai a zuba ruwan sanyi a kai.
-
Daga nan sai a tafasa ruwan zafi a zuba a kai, idan an ɗan daɗe sai a juya shi, har sai an tabbatar babu ƙulalai ko kaɗan a ciki.
-
A murje haɗin ya zama ruwa, sannan a bar shi ya huce ya zama da ɗumi.
-
Kafin ya yi sanyi sosai, sai a zuba culture a ciki.
-
Bayan an sa culture, sai a rufe a bari ya yi awa takwas zuwa 12, ko ma ya kwana.
-
Idan aka buɗe shi, sai a zuba sukari da flavor sai a motsa.
-
Idan yogurt din ya haɗu sai a sa a fridge a bar shi ya yi sanyi.
-
Daga nan sai a sha shi yadda ake so.