A yau za mu koyi yadda ake ɗan sululu, ɗan sululu abincin gargajiya ne na Bahaushe wanda ya kasance ana samar da shi daga garin rogo, wannan abincin akasari na yara ne ko masu kwaɗayi.
Abubuwan da ake buƙata
Garin rogo
Ruwa
Manja
Yaji
Maggi
Gishiri
Albasa
Yadda ake haɗawa
1. A kwaɓa garin rogo da ruwa. Sai a mulmula kamar yadda ake mulmula gullisuwa.
2. Sai a ɗora ruwa a tukunya, idan ya tafasa sai a zuba, bayan ya dahu sai a tsame ana zubawa a ruwan sanyi. A Wanke Shi tas.
3. Sai a zuba a plate a zuba manja, yaji, Maggi. sai a yayyanka albasa.
Domin sanin Yadda Ake Faten Dankali danna nan