Tatsuniyar Yelwa Da Tsohuwa Da Sarki

0
6

Ga ta nan, ga ta nanku.

An yi wata yarinya mai suna Yelwa. Tana da ƙawaye da yawa. Wata rana Sarkin garinsu ya umurci ‘yan matan garin su je rafi, su kamo kifi bisa sharaɗin cewa duk wadda ta kamo ta yi masa miya mafi daɗi, ita zai aura. Da man sauran ‘yan matan sun tsani Yelwa.

Saboda haka bayan sun kamo kifi sai suka haɗa baki suka jefa ta a cikin kogin ta nutse. Da farko har ruwan zai tafi da ita, to amma ta yi sa’a, wata tsohuwa ta zo ta tsamo ta. Wannan tsohuwa kuwa tana da baiwa. Yelwa kuma ta kwashe labarin duk abin da ya faru ta gaya mata. NantTsohuwar nan ta ji tausayinta.

Nan da nan ta kama wani ƙaramin kifi ta ba ta, kuma ta ba ta wata ‘yar tukunya, ta ce mata ta sa wannan kifi a cikin tukunyar ta rufe, ta kiwata shi. Washe-gari da Yelwa ta buɗe tukunyar sai ta ga wani babban kifi a ciki. Ta yi mamakin yadda kifin ya girma haka. Ta kama kifin ta dafa, ta ɗauka ta nufi fada.

Kafin ta je an soma biki har an rufe ƙofa. Ta roƙi dogarai suka buɗe mata, ta shiga. Kafin zuwanta Sarki ya riga ya ɗanɗana dukkan miyar da ‘yan matan suka kai, amma babu wadda ya gamsu da ita. Saboda haka da Yelwa ta kai tata miyar, Sarki bai so ya ɗanɗana ta ba, sai da tsohuwar nan ta matsa kusa da shi ta raɗa masa cewa ya taɓa.

Sarki ya taɓa ya ji miyar Yelwa zaƙi cakwai, abin ba dama. Ba da ɓata lokaci ba washe-gari Sarki ya bayyana mata buƙatarsa ta aurenta. Yace in ta yarda ta je ta shaida wa iyayenta a ɗaura musu aure nan da kwana biyu Yelwa ta tafi tana kuka saboda baƙin cikin maraici, domin tuni mahaifanta suka mutu.

Ta fara batun zuci tana cewa: “Kaito, yaya zan yi da raina yanzu, ga ni ba ni da iyaye.” Can sai ta kama waƙa tana cewa:

“Ke tsohuwa mai ceto,

Ke tsohuwa mai baiwa,

Sarki na so ya aure ni.

Ke tsohuwa mai ceto,

Sarki yana so ya aure ni,

Amma ga shi ba ni da iyaye,

Yaya zan yi a halin yanzu?”

Can sai ga tsohuwar ta bayyana, ta ce mata ta daina kuka, kar ta damu, komai zai yi kyau. Ta umurce ta da ta je ta samo ƙwari biyu ta kawo mata. Da ta kawo sai tsohuwar ta mai da su mutane, mace da namiji, wato sun zama iyayen Yelwa ke nan. Daga nan suka tasam ma fada, aka ɗaura aure.

Nan fa sai ƙawayen Yelwa suka ji kunya, suka nemi gafararta. Yelwa kuma ta yafe musu saboda halinta na haƙuri. Ita da ƙawayen suka zauna lafiya, har kowaccensu ta yi nata auren. Sai dai akwai ɗaya daga cikin ƙawayen mai mugun hali. Ba ta daina jin haushin rasa auren Sarki ba.

Saboda ƙyashi da hassada, sai ta shiga ƙulle-ƙulle da haɗa husuma domin ta kashe wa Yelwa aure. Ba abin da take so a duniya kamar ta ga auren Yelwa da Sarki ya mutu. Wata rana ta kama hanya ta je fada da nufin kashe Yelwa, amma ba ta yi nasara ba. Dogarai suka kama ta.

Duk da cewa ta so kashe Yelwa, amma ita ba ta so a hukunta muguwar ƙawar nan tata ba. Ta roƙi mijin a ƙyale ta domin ƙila ta gyara halinta. Sarki ya yarda, ya kuma tara mutanensa kaf ya shaida musu matuƙar ƙaunar da ke tsakaninsa da Yelwa. Ya tabbatar musu har ita kanta cewa a ko da yaushe iya ransa zai yi duk abin da ya dace don ya kyautata zama da soyayyar da ke tsakaninsu. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Taimakon Allah yana samun bawansa ta hanyoyi daban-dabaninda bai zata ba.
  • Yafe wa wanda ya musguna maka wani alheri ne da zai sa mai laifin ya canza halinsa nan gaba.
  • Rabo dangi ajali.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Karanta Tatsuniyar Tatsuniyar Tsohuwa Da ‘Yan Mata Uku

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Tsohuwa Da ‘Yan Mata Uku
Labarin na GabaTatsuniyar Kwaɗayi Mabuɗin Wahala
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.