Tatsuniyar Ɗan Agwai Da Kura

0
5

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wani Ɗan Agwai yana kiwon ɗan akuyarsa, har ya girma ya yi ƙiba. Sai wata rana ya kama shi ya kai shi kasuwa. Namun daji da yawa suka yi ta taya ɗan akuyar, to amma da zarar sun ji tarihinsa, sai su wuce, su ƙi saye. Ana nan, ana nan, har labari ya kai ga kunnuwan Kura, uwar son na banza.

Sai ta shirya, ta je a yi cinikin ɗan akuya da ita. Kura ta ga ɗan akuya ya yi ƙiba, kuma tana so. Sai ta tambaya: “Nawa kuɗin ɗan akuyan nan?” Sai Ɗan Agwai ya ce wa Kura: “Ni fa kokawa ce za ki yi da ni ta kwana bakwai a jere. Idan kullum kina ka da ni har kwana bakwai ɗin a jere, to ɗan akuya zai zama naki.

Idan kuma kin kasa, to mun dinga yin kokawar ke nan har sai ranar da kika sami nasara.” Sai Kura ta ce: “To na yarda.” Aka tara ’yan kallo, aka ce da su Kura za ta sayi ɗan akuyar Ɗan Agwai. Kowa ya share wuri ya zauna don kallon ciniki. Can sai Kura ta shirya, ta fito fage suka kama kokawa da Ɗan Agwai.

Kura ta ka da Ɗan Agwai; ta rinƙa cin nasara har tsawon kwana shida. A kwana na bakwai sai Ɗan Agwai ya ka da Kura, ya yi mata shegen duka, har ta kasa tashi. Da ta murmure, da ƙyar ta kai gida. Sai ta ce: “Yau ban fita da sa’a ba.” Washe-gari ta fita, Ɗan Agwai ya sake tiƙa ta da ƙasa, har ta suma.

Da ta samu aka kai ta gida, washe-gari sai ta ce da ’ya’yanta su ɓoye ta a cikin rumbu, kuma idan an zo neman ta, su ce ta yi tafiya. Da Ɗan Agwai ya yi jira a fagen kokawa, shiru bai ga Kurar ba kuma babu labarinta, sai ya je gidanta, ya yi sallama, amma sai ’ya’yanta suka ce mahaifiyarsu ta yi tafiya.

Sai Ɗan Agwai ya ce: “To, amma bari in ɗan buɗe rumbun nan, don in ga hatsin da ke ciki.” Kafin yaran su hana, Ɗan Agwai har ya buɗe rumbun, ya leƙa; sai ga Kura a cikin rumbun. Sai ya ciro ta, ya kai ta fagen kokawa. Suka fafata; ya ɗauke ta sama, ya danƙara ta da ƙasa. Daga ƙarshe dai Kura ta koma gida, da rarrafe.

Da ’ya’yanta suka ga haka, sai suka ce: “Baba, wannan sai fa mun nemi asirin da za ki sha ki sami nasara, in ba haka ba, wannan Ɗan Agwai zai kashe ki.” Washe-gari tun da sassafe suka shirya, suka tafi gidan wani boka neman asirin samun nasara a kan Ɗan Agwai. Da suka isa, suka yi wa boka bayani, sai ya ce: “Babu magani, amma akwai wata dabara ɗaya da zan taimaka muku da ita.”

Suka yi shiru, suna ji. Sai ya ce: “Akwai wani mutum mai suna Mai-barci-bana ya tashi-baɗi; yana can a ɗakinsa yana barci. Yadda ake ta da shi shi ne, za a samo garwashin wuta a kai ɗakinsa, sai ku je ku ce da Ɗan Agwai: ‘Ga wani zai yi cinikin ɗan akuyarka da kokawa.

A guje zai yarda zai bi ku; idan kun isa ɗakin mai barcin, sai ku zuba barkono a wuta, ku fita, ku bar su.’” To, da ma duk wanda ya ta da shi daga barci, sai ya kashe shi, muddin ya je kusa da shi. Sai suka je suka shirya yadda boka ya gaya musu. Kuma suka kawo Ɗan Agwai ɗakin Mai-barci-bana ya tashi-baɗi suka kulle su tare.

Can sai hayaƙin barkono ya tashi. Da Mai-barci-bana ya-tashi baɗi ya ji zafin hayaƙin barkono, sai ya ce: “Wane ne yake damu na?” Yana tashi sai ya ga Ɗan Agwai a kansa. Sai kawai ya kashe shi, ya fito ƙofar ɗaki. Sai ya hango Kura gefe tana jiran ta ga abin da zai faru, ya ce mata ta raka shi farauta, yana jin yunwa.

Kura ta yarda. Suka kama hanya. Da suka shiga daji, sai suka tarar da mutane masu yawa suna noma a gonar Sarki. Sai ya ce: “Ga nama, amma ba zai ishe ni ba. Amma bari mu ɗan taɓa.” Nan take ya kama mutanen nan ya murɗe wuyan kowannensu. Ya tara itace zai gasa, amma babu wuta. Daga nan ya hura bakinsa, wuta ta fito, suka gasa mutanen nan.

Ya yi wa Kura tayi, ta ce tun da shi ne babba, ya fara ci. Yana cin naman mutanen nan, har ya ƙare, Kura ba ta ci ba. Bayan ya gama, sai ya sa Kura ta samo masa tsinken sakatar haƙora. Ta samo, ta ba shi. Duk sanda ya sakato nama daga bakinsa, sai Kura ta amsa, ta cinye.

Da haka har ta ƙoshi. Daga nan Mai-barci-bana ya-tashi-baɗi ya ce, su je rafi shan ruwa. Da suka je, ya nemi Kura ta fara sha, ta ƙi, saboda shi ne babba, gara ya fara sha. Da ya kafa bakinsa, sai ya shanye duk ruwan rafin da ya taru a cikin shekara ashirin. Da ya fara cire haƙorinsa sai Kura ta razana, sai ta faɗi ta suma. Da Mai-barci-bana ya-tashi-baɗi ya ga haka, sai ya sa hannu ya ɗauki Kura, ya kama hanyar ɗakinsa. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
  • Duk inda ka kai ga zalunci sai ka haɗu da wanda ya fi ka zalunci.
  • Wani lokaci dabara ta fi ƙarfi tasiri.
  • Kaddara ta riga fata.
  • Kura da shan bugu, gardi da amsar kuɗi.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsunyar Ɗan Buwaila Da Ɓangorinsa

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsunyar Ɗan Buwaila Da Ɓangorinsa
Labarin na GabaTatsuniyar Ya Tsinci Dami A Kala
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.