Tatsuniyar Darajar Neman Sani

0
6

Ga ta nan, ga ta nanku.

Wani mutum mai suna Duna wanda yake zaune da matarsa Delu a wani ɗan ƙauye da ke kusa da garin su Koƙi matar Gizo, sun jima da yin aure ba tare da Delu ta yi ko da ɓatan wata ba. Mijin dai bai damu ba, ita kuma ta dangana komai ga Mai sama.

Ana nan sai wata rana Delu ta yi ɓatan wata. Ita da mai gidanta Duna suka yi murna. Bayan wata tara kuma ta sauka lafiya, ta haifi ɗa namiji. Bayan sati guda aka raɗa masa suna Maishuni. Da ya ɗan data, sai Duna ya ce da Delu: “Kin ga dai ga shi mu mun rayu cikin duhun jahilci, ya kamata mu tura Maishuni makaranta.”

Ta ce: “Haka ne, amma fa ina tsoron kada ya galabaita a can.” Mai gidanta ya rarrashe ta, ta fahimci darajar sani, ta yarda a kai yaro wurin neman sani. Bayan mahaifin ya shirya sai ya ɗauki Maishuni suka tafi ya kai shi wani gari a wata tsangaya, ya haɗa shi da wani babban masani; ya kuma shiga cikin ƙolaye.

Da Duna zai tafi sai ya ce da ɗan: “Ko da bayan na rasu, idan ka dawo gida kana so ka gane mahaifiyarka, sai ka yi cigiya. Duk wadda ta ce ita ce sai ta gaya maka a inda ta haife ka.” Yaro ya yi shiru yana saurare. Da uban ya gama sai ya ce: “To, me za ta faɗa in gane ita ce?” Sai mahaifinsa ya ce: “Idan ta ce a tsakar ɗaki ta haife ka, to ita ce mahaifiyarka.”

Ya yi ban kwana da Maishuni ya koma garinsu. Uban bai fi wata tara da komawa ba sai ya rasu. Delu ta yi baƙin ciki matuƙa, domin ba ta san garin da mai gidanta ya kai ɗansu karatu ba. Ta cigaba da zama cikin haƙuri. Ana nan bayan kamar shekara ashirin da bakwai, sai Maishuni wanda tuni ya zama babban malami, kuma mai dukiya, ya ji yana son zuwa ganin mahaifarsa.

Amma fa bai san sunan garinsu ba. Ya yi ta bincike, har a ƙarshe ya sami waɗanda suka yi masa kwatancen garin. Bayan ya shirya sosai, sai ya kama hanyar garinsu. Da ya shiga garin sai ya kama wannan waƙa ta cigiyar mahaifiyarsa: “Wace ce mahaifiyata? Wace cemahaifiyata?”

Sai wata mata wadda ba ta wuce sa’arsa ba ta ce: “Ni ce mahaifiyarka, Samari ai ni ce mahaifiyarka.” Da ya dube ta sai shakka ta kama shi. Da gani ya san ba ta yi shekarun da za a ce ta haifi kamarsa ba, amma dai saboda halaye irin na masu sani da kuma bin umarnin mahaifinsa sai ya ce: “A ina kika haife ni? Faɗi inda kika haife ni.”

To da yake ta ga alamun sukuni tare da Maishuni, sai ta ƙirƙiro zancen da take ganin ya dace da matsayinsa ta ce: “A kan gadon ƙarfe, A kan gadon ƙarfe.” Sai da ya bari ta gama hauragiyarta, sai kawai ya mayar mata da wannan jawabi inda ya ce:“Ba ke ce mahaifiyata ba, Ba ke ce mahaifiyata ba.”

Sai ya kama hanya tare da masu raka shi, suna ta tafiya dai a cikin gari. Da suka kai tsakiyar gari sai ya fara rera waƙarsa. Mata suka fito, wata ta ce a kan gado, wata kuma ta ce kan tabarma, wata ma cewa ta yi a kan gadon zinariya. Haka dai, ba wadda ta faɗi gaskiyar magana.

Har sai da shi da abokan tafiyarsa suka fara gajiya, sai can ya ga wata mata a zaune ta kasa rogo. Da gani ka san ta jigata, ko da yake ba ta karaya da rayuwa ba sai ya dube ta ya ce: “Wace ce mahaifiyata?, Wace cemahaifiyata?” Wannan waƙar ta sa Delu yin murmushi da tunanin baya.

Ta so ta gane muryar Maishuni, to amma sai ta yi shakka irin ta natsuwa, sai kawai ta mayar masa da waƙa: “Ni ce mahaifiyarka, Ni ce mahaifiyarka.” Sai Maishuni ya ji kamar ya gamsu da maganarta, saboda muryarta ta yi kama da wata murya da ke tsakiyar birnin zuciyarsa, sai ya ce: “Ina kika haife ni?, Ina kika haife ni?”

Wannan tambayar da ya yi ta sa ta tunanin cewa lallai ga alama Maishuni ne Allah ya dawo mata da shi gida. Ga bayanin da ta yi: “Na haife ka a tsakar ɗaki, Nahaife ka a tsakar ɗaki.” Da jin jawabin da ta mayar masa, sai farin ciki ya cika masa zuciya. Nan take idanunsa suka cika da ƙwalla, amma ya yi ta maza ya kanne.

Ya je gabanta ya durƙusa, ya gaishe ta yana mai cewa: “Lallai ke ce mahaifiyata, Lallai ke ce mahaifiyata.” Ta tashi suka shiga cikin gida. Bayan shi da abokan tafiyarsa sun huta, sai ta shiga ba shi labarin rayuwarta da rasuwar mahaifinsa da yadda jikinta yake gaya mata cewa za su gana.

Shi kuma ya ba ta labarin baiwar da ya samu daga Allah, ta ilimi da dukiya mai amfani, kuma ga shi tana da rai za ta more shi. Suka yi koke-koke na jin daɗi. Bayan Maishuni ya huta, sai ya nemi izinin mahaifiyarsa a kan ya gina mata kataferen gida. Aka gina ya kawo kuɗi ya cika mata tukwane da wani ɗan ƙaramin rumbu.

Kafin ya koma kwaso iyalinsa kuma, ya yi magana da dattijan gari da sauran shugabanni don a nuna inda za a gina makaranta. Ya kawo kuɗin aikin kuma ya bayar. Bayan ’yan kwanaki ya koma garin da ya yi karatu da nufin ya kawo iyalinsa mahaifarsa. Aka gama ginin makaranta, shi kuma ya kwaso iyalinsa da dukiyarsa ya dawo garinsu ya zauna shi ne babban malami a garin inda ake zuwa ɗaukan karatu daga ko’ina a wannan yanki nasu. Kurunkus.

Abubuwan DaLabarin Yake Koyarwa 

  • Ilimi shi ne gishirin rayuwar duniya. Ilimi shi ne tushen duk wani alheri da ake samu.
  • Maƙurci, mawadaci.
  • Ƙaddara ta riga fata.
  • Arziki a ƙasa yake, tako shi ake.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Karanta Tatsuniyar Ladi Da Dodo

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Ladi Da Dodo
Labarin na GabaTatsunyar Ɗan Buwaila Da Ɓangorinsa
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.