Tatsuniyar Sarki, Gizo Da Kwarkwata

0
47

Ga ta nan, ga ta nanku.

Wata rana a can kusa da garin da Gizo ke sarauta, wani tsoho yana cikin gonarsa yana kashe kwarkwata, sai ya ga wata ƙatuwar kwarkwata, har ya haɗa manyan yatsunsa zai murtsuke ta, sai ta ce da shi: “Kada ka kashe ni, zan yi maka tsaro a gonarka, kada ka kashe ni.”

Sai ya tambaye ta: “Idan na bar ki, me za ki yi mini?” Sai Kwarkwata ta ce: “Kai dai ka sake ni a cikin gonarka ka gani.” Mamaki ya kamaTsoho, sai ya sake ta a cikin gonarsa. Ya yi kamar ya tafi gida, amma sai ya sami wuri ya ɓuya. Yana maƙe, sai ga wasu fadawan Sarki Gizo sun zo gonar sata.

Da suka je za su yanki harawar wake sai Kwarkwata ta fara waƙa tana cewa:

“Caca bille, caca bille,

Burabusko bille,

Fadawan Sarki Gizo,

Sun zo satar harawar wake,

Su kai wa dokin Sarki.”

Waƙar Kwarkwata da ta ratsa fadawan Sarki sai suka fara rawa. Da Sarki Gizo ya ga shiru, sai ya tura dogarawansa, watau su Kiyashi da Kyankyaso da Fara su kamo fadawan da ya tura don su yanko harawar wake. Dogarawa na zuwa suka ce da fadawa: “Yaya Sarki ya tura ku ciyawa kuka yi zamanku?

To, an ce mu kama ku.” Sai fadawan nan suka ce da dogaran Sarki: “Ku taɓa waken ku ma ku gani.” Da dogaran suka taɓa waken kamar za su yanki harawar, sai Kwarkwata ta shiga abin da ta saba:

“Caca bille, Caca bille,

Burabusko bille,

Fadawa sun zo,

Dogarawa sun zo,

Satar harawar wake,

Su kai wa dawakin Sarki.”

Su ma dogarawa suka kama rawa. Ba damar komawa fada, balle Sarki Gizo ya san me ake ciki. Da daɗewar ta yi yawa, sai Sarki Gizo ya taso baradensa, wato manyan mayaƙansa, irin su Kudan zuma da Kunama da Sari-kutuf da Macizai da Rina da Kwarkwasa domin su kamo masa fadawa da dogarawa saboda sun yi wa Sarki ƙyuya.

Suna isa suka fara daka wa fadawa da dogarawa tsawa, suna cewa: “Sarki ya aiko ku yankan harawar dawakinsa, ba ku koma ba. Kun raina Sarki ke nan ko?” Fadawa da dogarawa ba su tsaya wani wuni-wuni ba, suka ce da sojojin nan: “Ku taɓa waken nan kamar za ku yanki harawar ku ga abin da zai faru.”

Sai suka taɓa; sai Kwarkwata ta rera waƙarta:

“Caca bille, Caca bille,

Burabusko bille,

Fadawa sun zo,

Dogarawa sun zo,

Sojoji sun zo,

Garin satar harawar wake,

Su kai wa dawakin Sarki.”

Sai su ma suka kama rawa. Da Sarki ya ji shiru, sai ya je gonar shi da kansa a fusace. Yana isa sai ya ga baradensa da dogarawansa da fadawansa suna ta dirkar rawa ba ƙaƙƙautawa a wannan gonar. Sai ya faɗa su da faɗa. Da suka ga ran Sarki Gizo ya ɓaci, sai wasu daga cikinsu suka ce: “Ranka ya daɗe, taɓa waken nan kamar za ka yanki harawar ka gani.”

Gaya wa Sarki haka ke da wuya, sai ya ƙara harzuƙa, sai ya ce: “Zan sa a fille muku kawuna.” Baki ɗayansu sai suka ce: “Don girman ikon da ke hannunka ka taɓa waken ka ga abin damaki.” Sai Sarki ya taɓa wake, hannunsa na sauka a kan waken nan sai Kwarkwata ta shiga aikinta:

“Caca bille, Caca bille,

Burabusko bille,

Fadawa sun zo,

Dogarawa sun zo,

Barade sun zo,

Sarki ya zo satar wake,

Ya kai wa dawakinsa.”

To, Sarki Gizo bai yi rawar ba, saboda shirinsa ya fi na Kwarkwatar. Wato hatsabibancin Sarki ya fi na Kwarkwata ƙarfi. Sai ya ce da fadawansa: “Kai wannan gonar ta wace ce?” Tsoho da ke maƙe bai mabari fadawa sun yi wa Sarki jawabi ba sai furut ya fito ya faɗi a gaban Gizo ya ce: “Mai duniya ka daɗe, ni ne mai gonar nan.”

Sai Sarki Gizo ya ce: “Wane aiki ka yi wa gonarka take yin haka?” Sai Tsohon nan ya ba Sarki labarin yadda suka yi da Kwarkwata. Sai Sarki Gizo ya ce: “Tana ina?” Nan da nan ya ɗauko ta ya je gaban Sarki ya miƙa masa ita. Sai Sarki ya ce da Tsoho yana son ya bar masa Kwarkwatar nan, kuma ya sa ta saki fadawansa da dogarawansa da baradensa da ta sa su rawa.

Da ya roƙe ta sai ta sake su, suka daina rawar, kuma ya mallaka wa Sarki Kwarkwata. Sarki Gizo saboda jin daɗi ya kawo kuɗi masu yawa ya ba Tsoho, shi kuma ya tafi fada da wannan Kwarkwatar. Duk sanda yake cikin nishaɗi sai ya sa ta zo ta rera masa waƙoki iri daban-daban.

Duk sanda yake cikin raha kuma sai ya tsokani dogarawansa da fadawansa da sojojinsa ya ce: “Na gaban Sarki waɗanda Kwarkwata ta ci ku da yaƙi.” Sai duk a fashe da dariya. Haka dai Sarki Gizo ya ci gaba da tafiyar da mulkinsa tare da fadawansa da dogarawansa cikin jin daɗi. Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Tausaya wa halittar Ubangiji yakan yi sanadin samun nasara.
  • Adalci shi ne sinadarin samun nasarar kowane shugabanci; azzalumin shugaba kuma ƙarshensa nadama.
  • Kula da kaya, ya fi ban cigiya.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Kogi Mai Cinye Maƙaryata

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Kogi Mai Cinye Maƙaryata
Labarin na GabaTatsuniyar Talume
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.