Tatsuniyar Biri Da Kare

0
6

Ga ta nan, ga ta nanku.

Wata rana Kare yana yawo a cikin gari, sai ya haɗu da Biri. Sai Biri ya tambaye shi inda za shi, ya ce: “Ina yawo ne ko zan sami ɗan abin da zan ci.” Shi ma Kare ya tambayi Biri inda za shi, ya ce: “Ai ni kullum a daji nake wuni, in ci abinci in ƙoshi.” Biri ya ce da shi: “Ko za ka bi ni ne?” Kare ya ce: “Ni ban taɓa zuwa daji ba.”

Daga nan Biri ya tambayi Kare: “Shin kai ma kana da wayo irin nawa?” Kare ya mayar da jawabi da cewa: “Wayona goma ne.” Biri ya ce: “Ka ga ni wayona ɗaya ne, amma kullum a daji nake wuni, ballantana kai babba mai wayo goma, shi ne ka zauna a gida? Haba, kada ka ba ni kunya mana.” Sai Kare ya ce: “To, bari in shirya mu tafi.”

Biri da Kare suka kama hanyar daji. Suna cikin tafiya sai suka isa wani lambu. Ba tare da ɓata lokaci ba, Biri ya tsallake shingen lambu, ya dinga cin kayan marmari, sai da ya ƙoshi. Kare kuwa yana jin yunwa amma tun da ba ya cin kayan lambu sai ya ce: “Kai Biri ni fa yunwa nake ji.” Biri ya ce: “To, shi ke nan mu je gaba, ko ma sami abin da za ka ci.” Haka suka ci gaba da tafiya.

Can sai Kare ya hango wata jaɓa ta fito daga rami; sai ya bi ta, ya kama ya cinye ya ce da Biri: “Yanzu kam na ɗan sami ƙarfi, mu ƙara gaba.”Suka ci gaba da tafiya. Can sai suka hango ‘ya’yan Kura su biyu, sai Kare ya ce wa Biri: “Kai ni fa zan koma na ga ‘ya’yan Kura.” Biri ya ji haka, kuma ya gane Kare ya tsorata, sai ya ce masa: “Haba, kada ka ba ni kunya mana.

Yanzu da girmanka kake tsoron ‘ya’yan Kura?” Sai Kare ya ɗaure suka ci gaba da tafiya. Da ‘ya’yan Kura suka ga Biri da Kare, sai ɗaya daga cikinsu ya ce da ɗayan: “Je ka kira iya, ka ce mata ga nama ya zo har guda biyu.” Ɗan Kurar ya sami uwarsu a rami ya ce mata: “Iya, mun ga nama har biyu suna yawo.” Nan take Kura ta yaƙe baki, yawu ya zubo, ta yi miƙa, ta tambayi ɗan ta ce: “Me da me kuka gani?”

Ya ce: “Biri da Kare.” Da ta ji haka sai ta ce: “Ka je ka kira ɗan’uwanka ku dawo gida.” Sai ya fita da gudu ya kira shi suka koma rami, uwarsu ta ce: “Ku je ku hura wutar da za mu dafa namansu idan sun zo.” Nan da nan’ya’yan Kura suka samo itace, suka hura wuta. Shi kuma Biri sai ya ce wa Kare ya raka shi zuwa wurin abokinsa.

Sai suka tafi, ba su tsaya ko’ina ba sai bakin ramin Kura sai ya ce: “Bari in shiga ka jira ni a nan.” Biri ya shiga, ya gai da Kura, kuma ya ce: “Yau na zo tare da wani amini na ne domin mu gaishe ki.” Da Kura ta ji haka sai ta yi murna, Biri kuma ya leƙa, ya kirawo Kare. Da ya shiga ya ga Kura a tsugune, sai nan take ya faɗi a sume.

Biri kuma da ya ga haka sai ya yayyafa masa ruwa, ya farfaɗo. Da Kare kuma ya lura an hura wuta, sai ya sake ƙifewa, ya ƙara suma. A nan ma dai Biri ya sake ta da shi ya ce da shi: “Ka je ka taya su hura wuta.”Da Kare ya je ya hura wuta sai ya riƙa yin waƙa yana cewa: “Biri ya kawo ni gidan mutuwa, Biri ya kawo ni wurin halaka, Da Biri ya ji haka, kuma ya tabbatar Kura ma ta ji, sai ya ce: “Kai Kare ba ka iya hura wuta ba; ba ni ka gani.”

Da Biri ya karɓi hura wuta, sai ya kama wannan waƙa: “Na kashe Kura tara, Yau zan kashe ta goma, Ni da Kare mu sha nama, Na hura wutar dafa Kura ta goma, Yau zan kashe Kura ta goma.” Da Kura ta ji haka sai tsoro ya kama ta; sai ta ce: “To, ashe sun zo kashe ni ne?” Sai wata dabara ta faɗo mata, yadda za ta gudu tare da ‘ya’yanta.

Sai ta kira ‘ya’yanta ta ce: “Ku je ramin kawuna ku gani ko ya dawo daga farauta. Maza ku dawo ku gaya mini fa; kada ku tsaya wasa a hanya.” Da suka fita suka ɗan daɗe, sai Kura ta ce: “Biri, ka ga fa yaran nan sun daɗe, bari in bi sawunsu in gani ko sun tsaya wasa a hanya.” Kura na fita ta hango ‘ya’yanta suna dawowa, sai ta yi sauri ta sha gabansu ta ce su gudu, idan ba haka ba Kare da Biri za su kashe su.

Da Kare da Biri suka gane abin da ya faru, sai suka fito daga ramin Kura suka ci gaba da neman abincinsu; ba sauran wani tsoro kuma, domin Biri ya yi wayo ya kori Kura da dabara. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Girman kai rawanin tsiya.
  • Durƙusa wa wada ba kasawa ba ne, ba ya hana ka tashi da tsawonka.
  • Ƙarfin hali da juriya suna karya gwiwar abokin gaba kome ƙarfinsa.
  • Haɗama da rashin godiya ga Allah sukan sa a yi da-na-sani.
  • Igiya ba ta ɗaure kaya, sai dabara.
  • Banza ta kori wofi.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta tatsuniyar Ɗan Kutungayya

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Arɗo Da Ndoffiwa
Labarin na GabaTatsuniyar Wani Mutum Da ‘Yarsa
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.