Tatsuniyar Musare Da Hodanego

0
1

Ga ta nan, ga ta nanku.

An yi wani mutum mai mata biyu, da ’ya’ya biyu. Uwargidan tana da ɗanta mai suna Musare; amaryar kuma tana da ’ya wai ita Hodanego. Ana nan har yara suka girma. To da ma shi mahaifinsu yana da dabbobi masu yawa, sai ya ba Musare Akuya guda, ita kuma Hodanego da take ƙarama, ya ba ta Kaza.

Suna nan, duk sanda Musare ya nemo wa akuyarsa abinci ya zuba mata, sai Hodanego ta saki kazarta ta je ta watsar da abincin. Kullum haka, har dai rannan yunwa ta kashe akuyar Musare. Ya yi haƙuri bai ce komai ba, amma kuma sai kullum ƙanwar ta riƙa yi masa dariya, tana tsokanar sa.

Daga ƙarshe dai sai ya ɗan yi magana, sai uwar Hodanego ta kama shi da duka. Amma saboda kara irin ta matan kirki, mahaifiyarsa ba ta ce komai ba. Wata rana sai uwar Musare ta kwanta ba lafiya, har jikinta ya fara ruɓewa ta fara wari, sai kishiyarta ta fara yi mata tsiya da ’yan maganganu, har da zagi tana cewa ita fa wari ya fara damun ta a gidan.

Haka dai, kullum sai Musare da mahaifiyarsa su shiga ɗaki su yi ta kukan baƙin ciki. Da ciwo ya tsananta, sai ta ce da shi: “Ka tashi ka shiga dajin nan ka nemo mini magani.” Sai ya ce da uwar: “To.” Washe-gari da sanyin safiya ya fita, ya kama hanyar dajin don nemo magani.

Yana cikin dokar daji sai ya haɗu da wata tsohuwa ita kaɗai tana dogara ’yar sanda. Da ta ji motsinsa sai ta ce: “Don Allah ɗan nan ka taimake ni ka ɗora ni kan hanya wadda zan bi
in shiga gari.” Sai ya dube ta cikin murya lallausa ya ce: “Ayya, ai kin baro hanyar da nisa, amma bari in kai ki.”

Tsohuwa ta ce: “Yawwa, na gode.” Ya shiga gaba, tana biye da shi har suka isa hanya. Sai tsohuwa ta ce da shi: “Ɗana da ma ina so in gwada kirkinka ne, kuma zan taimake ka a kan abin da ka fito nema.” Mamaki ya kama Musare, sai ya ce: “To.” Sai tsohuwa ta ci gaba da yi masa bayani tace:

“Ka bi wannan hanyar, kada ka tsaya har sai ka tarar da wata babbar tsamiya, sai ka tsuguna a gindinta ka roƙi duk abinda kake so.” Musare ya yi mata godiya, ya bi inda ta nuna masa har ya isa gindin tsamiyar da ta kwatanta masa. Musare na isa ya tsuguna, ya roƙi maganin ciwon da ke damun mahaifiyarsa.

Sai kawai ya ga ƙullin magani ya faɗo daga wata sheƙa da ke kan tsamiyar. Ya ɗauka ya yi
kamar zai miƙe tsaye, sai ya ji an ce: “Idan kana da wani abu da kake buƙata, ka tambaya a ba ka.” Ya waiga bai ga kowa ba, amma sai ya ce: “Ciwon da ke damun uwata ne kan gaba da komai; maganin nan ma ya isa. Na gode.”

Kafin ya gama rufe baki sai ya ga an fito masa da wani Doki ya sha ado da gwalagwalai da kayan sa wa iri-iri da dukiya mai yawa, sai ya ji an ce: “Dokin da kayan nan duka naka ne.” Ya sake dubawa bai ga kowa ba, sai ya sake yin godiya. Da ya lura dai an sallame shi, sai ya ɗare kan Doki, ya kama hanya bai zame ba sai gida, ya shiga ya ɗaure Doki, ya doshi ɗakin mahaifiyarsa.

Da ya shiga ɗakin sai ya tarar saboda ƙarfin maganin da aka ba shi, har mahaifiyarsa ta warke. Sai ya ba ta labarin yadda suka yi da tsohuwa. Ita kuma ta gaya masa cewa kishiyarta ma bayan tafiyarsa ta kamu da irin ciwon. Mahaifiyarsa ta yi masa godiya, kuma ta umarce shi da ya kai wa kishiyarta maganin ita ma ta sha.

Nan take ya ɗauki maganin ya fita tsakar gida, ya kira Hodanego ya ba ta maganin ta kai wa mahaifiyarta. Da kishiyar uwar ta karɓi maganin ta sha, kuma nan take ta warke. Wannan lamari ya sa ta shiga cikin wani hali na jin kunya, sai kawai ta fashe da kuka, ta tashi ta shiga ɗakin uwar Musare tana ba ta haƙuri.

Ita kuma ta ce da ita ta yafe mata. Da haka suka ci gaba da zama gidan mijinsu, kamar ya da ƙanwa, ba sauran kishi. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Kyakkyawar tarbiya jari ce ga mai ita; sai mai tarbiyar ƙwarai ne yake yin afuwa.
  • Idan ka ga mutum mugu kuma maƙetaci to dama ba shi da tarbiya.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Marayu Biyu

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Marayu Biyu
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.