Ga ta nan, ga ta nanku.
A can kusa da dajin Ƙanzon Kurege, akwai wani mutum da ke zaune da matarsa. Mace ce mai haƙuri da son taimakon mijinta a hidimar da yake yi ta kula da gida. Suna nan, sai Allah ya ba matar ciki. Sannu a hankali, ciki ya girma, sai mijinta ya ce tunda cikinta ya girma, ta daina zuwa rafi ɗaukar ruwa, amma sai tace ai babu mai taimaka mata.
Ta ci gaba da zuwa ɗaukar ruwan. Ana nan, wata rana matar nan ta je ɗaukar ruwa sai ta fara naƙuda a bakin rafi. Da sauran matan da suka je ɗaukar ruwa tare suka ga halin da ta shiga, sai suka kai ta gida. Da haihuwa ta zo, sai ta haifi jarirai goma sha ɗaya. Goma daga ciki ba su da jiki; guda ɗaya ne kaɗai cikakken mutum.
Bayan kwana bakwai aka raɗa wa kowannensu suna. Karamin cikinsu, watau mai jiki, sai aka sa masa suna Kurma. Yaran nan suna nan yau da gobe har suka girma. To amma sai
aka lura sauran goman duk miyagu ne, har ma sun fara ƙoƙarin cinye ƙanen nan nasu. Da iyayensu suka ga haka, sai suka kira Kurma suka ce: “Tun da ‘yan’uwanka ba za su bar ka ba, gara ka sulale cikin dare ka yi tafiyarka wani gari.”
Can cikin dare sai babansu ya ta da Kurma daga barci ya ba shi wata sanda ya ce ya kama hanya ya tafi kawai. Kurma ya karɓi sandar da ubansa ya ba shi, ya kama hanya a cikin daren ya fice daga garin. Da gari ya waye, ‘yan’uwan suka leƙa ɗakinsa, ba su ganshi ba, sai suka tambayi uwarsu inda yake; ta ce ba ta sani ba.
Da suka tambayi ubansu, sai ya ce da su: “Kurma ya ce in ba shi sanda zai
je wani gari, kuma na ba shi ya tafi.” Da suka ji jawabin ubansu sai suka rasa yadda za su yi. Bayan Kurma ya koma wani gari da zama, sai ya haɗu da matar da yake so ya aura. Saboda ba shi da dukiyar da zai yi auren, sai ya sayar da sandar nan da ubansa ya ba shi lokacin da zai baro garinsu, ya biya sadaki aka ɗaura musu aure.
Kurma yana nan zaune da matarsa cikin jin daɗi. Bayan wani lokaci sai matar ta ce: “Mai gida ya kamata mu je garinku ganin gida domin in san garinku da danginka da mahaifanka.” Da ya ji abin da ta faɗa sai ya ce: “Mhm, watau ba ki sani ba ne, ai ‘yan uwana duk ba su da gangar jiki, kuma mayu ne, idan mun je za su cinye mu.” Sai ta ce a a, ita dai sai sun je tun da mahaifansa suna nan ba wani mugun abu da zai faru.
Da ya ga ta matsa sai sun je, sai ya ce: “To kada ki ce na hana ki zuwa, ki shirya mu tafi.” Bayan sun kammala shirye-shirye, sai suka kama hanyar garinsu Kurma. Da suka isa ƙauyen, suna shiga gidan sai suka ci karo da ɗaya yana mirginawa a ƙasa. Da matar Kurma ta ga kai ne yake mirginawa babu gangar jiki, sai tsoro ya kama ta, ta fashe da kuka.
Su kuwa ‘yan’uwan Kurma da suka ji shi ne ya zo har da matarsa, sai suka kama waƙa suna cewa: “Lale, lale, Maraba da Kurma, Kurma lale, Kurma sannu da zuwa, Kurma lale, Kurma ina sandarka ne?” Da Kurma ya ji sun nemi sanin inda sandar da mahaifinsa ya ba shi, sai ya ce: “Na sayar da sandar.” Sai ɗaya daga cikinsu ya ce: “Me ka yi da kuɗin?” Sai ya ce: “Na yi aure da su.” Suka ce: “Ina matar?”
Sai Kurma ya amsa wa mai tambayar: “Ga ta nan a bayana, tana kuka.” Wani kuma ya tambaye shi: “Me ya sa take yin kuka?” Haka dai suka rinƙa yi masa tambayoyi, har suka shiga cikin gidan. Da uwarsu ta ga ɗanta, sai ta zo ta tarye su shi da matarsa a cikin murna a tsakar gida, ta ce su shiga ɗaki, suka shiga. Suka ƙara hutawa, har zuwa faduwar rana.
Da dare ya yi sai uwar ta kira Kurma ta ce: “Ka san ‘yan uwanka mayu ne, me ya sa ka kawo ‘yar mutane a cinye ta?” Sai ya amsa da cewa: “Tana so ta gaishe ku ne da baba.” Sai uwar ta ce: “To shi ke nan, idan an ɗauke ƙafa zan ɓoye ku a rumbu, in sun tambaye ni in ce kun tafi; idan sun kwantasai kugudu.” Da dare ya tsala, sai ta ɓoye su a rumbu.
Can cikin dare sai ɗaya daga cikin ‘yan’uwan Kurma ya tambayi uwarsu inda Kurma da matarsa suke. Sai ta ce: “Ai sun tafi.” Sai ya ce: “To amma yaya nake jin ƙanshin mutum a gidan nan?” Sai ta ce: “Ai ni ma mutum ce, in kuma za ku cinye ni to.” Sai baki ɗayansu suka ce: “A a, ba za mu cinye wadda ta haife mu ba.”
Don uwar ta kwantar musu da maitar da ta motsa, sai ta ce musu: “Ai ba su tafi ba; sun je gai da ƙawayena ne; da zarar sun dawo zan dafa su.” Can cikin dare sai uwar ta taso Kurma da matarsa da ke barci a rumbu ta ce musu: “Ba ku ga babanka ba saboda ya yi bulagiro. Ga shi kuma lokacin gudu ya yi, sai ku kama hanya kafin su gane.”
Ashe da ma ‘yan’uwan tuni suka zaci za a yi musu dabara ne, suka fice daga gidan suka tafi jiran Kurma da matarsa a bayan gari. Kurma da matarsa sun kama hanya za su gudu, sai wani da ya sanshi ya gaya masa cewa ‘yan’uwansa suna can a kan hanya suna jiran sa shi da matar su cinye su. Yana cikin wannan tsoro da damuwa, sai ga wata tsuntsuwa ta zo.
Sai Kurma ya roƙe ta, ta ɗauki matarsa ta tsallakar da ita can gaba da inda ‘yan’uwansa suke fakonsu shi da matarsa. Nan take tsuntsuwa ta yarda, matarsa ta hau suka tashi sama. Shi kuma Kurma sai ya ɗauki ganga yana kiɗa har ya isa inda ‘yan’uwansa suke. Da ya isa sai ya fara waƙa.
Su kuma sai suka tambaye shi matarsa; sai ya ce ya bar ta a gida. Da jin haka sai suka kama hanyar gida da gudu. Shi kuma da ya ga sun yi nisa, sai ya kama hanya ya yi ta gudu, har ya je ya sami matarsa suka yi tafiyarsu. Ƙurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Bin iyaye bin Allah.
- Tarbiya ce garkuwar kowane yaro.
- Ceto daga Ubangiji yakan zo ne ta kowane hali.
- Makusancinka na iya zama makashinka.
- Zumunci maganin bala’i.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Wata Mata Da ’Ya’yanta
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Edita@rumasau-kallamu










