Wasu lokutan mukan karanta ko mu ji labaran da kan ce wani ya mutu yayin jima’i ko yayin gasar wauta akan hakan, musamman daga wani yanki na ƙasar nan ko ƙasashen ƙetare… har wasu cikin mu su yi ta dariya, wasu na mamaki, wasu kuma na faɗin albarkacin bakinsu.
Toh amma a zahiri na lura da yawa ba su fahimci me ke jawo hakan ba, illa iyaka wasu kan yi amfani da slang cewa; Matar ta ƙarar da shi, ko ta fi ƙarfinsa. Iya abinda mutane kan kawo ransu kenan…. Ga layman wanda bai san komi ba shi zai tafi akan ƙila ruwan maniyyi ne mutum ya yi ta zubarwa…har ya ƙare ya kai ga duk ƙarfinsa ya tafi ƙarshe ya mutu. Amma inaaa ba haka karatun yake ba.
Abinda ba ku sani ba ko a tsakanin mata da miji da ke auren sunna jima’i ya kai magidanta da yawa lahira ba tare da sun shirya ba. Kurum wani lokacin matan ne ba sa gane al’amarin, ko kuwa ba su san ya za su bayyana ba, ko kuma su zaɓi rufe sirrin a tsakaninsu.
Shi yasa wani za ka ji ana lafiya ƙalau aka rabu da mutum amma kashe gari da safe ake sanar da rasuwarsa. Amma da za ka bincika wataƙil a daren da zai mutun har kwanciya da iyalinsa ya yi. Don haka maza ku buɗe kunnuwanku da kyau, ku shiga taitayinku, ku san me yake muku ciwo.
BAKI ƊAYA ZAN MAGANA NE AKAN WANNAN JARABAR TA TALLAN MAGUNGUNAN MAGIDANTA
Shan Magungunan ƙara ƙarfin Jima’i walau na Hausa, Islamic chemist ko na Bature haka siddan hauka ne. Wannan maganin ba ya ƙarawa mutum jin sha’awa, shauƙi, ko daɗin jima’i. Abinda kurum yake ma shi ne miƙar da azzakari, sai kuma kan haɗa da jinkirta muku Inzali wato Delay Ejaculation. Wato ya zamto ka jima jikin mace.
Jimawa jikin Mace ko ba shi ne daɗin jima’i ba, Infact a lokacin an sauka ma daga ainihin dalilin jima’in, kurum yanzu kuna yi ne cikin fargabar kar iyalinku, ko farkarku ta yi ƙorafi ba ma don kuna jin daɗin al’amarin ba.
Toh amma abinda ba ku sani ba shi ne gwargwadon yadda kuka jinkirta ba ku kawo ba.. gwargwadon matsi da takurar da kuke sanyawa zuciyarku. A yayin da mutum ke jima’i dama a lafiyayyen yanayi ma adadin bugawar zuciyar mutum na ƙaruwa wato Heart rate.
Normal takan buga sau 60–100bpm a duk minti yayin da ake harkokin rayuwa…. Amma yayin jima’i bugunta kan iya ƙaruwa da kaso arba’in zuwa hamsin wato 40-50% ka ga kenan bugun zuciyar mutum na iya kai wa 140-150bpm wanda gudun ba kaɗan ba ne, tana bugawa tamkar sanda abin tsoro ya rarako ka a guje kake neman tsira.
Shi yasa ka taɓa tambayar kanka me yasa mafi yawan mutane ke mutuwa bayan jima’in?Yayin da ka sha maganin ƙara kuzarin jima’i za ka sami kanka a yanayin da kai kanka za ka ji ƙwaƙwalwarka na nusar da kai cewa ya isa haka, ba abinda kake so illa kai release amma kuma ya ƙi zuwa…
Don haka wannan buƙatar ta ka samu ka kawo don ka huta ba za ta yiwu ba har sai ka ƙarawa zuciyarka matsi wato stress akan matsin da already cikinsa take dalilin maganin da ka sha. Stress kan stress kenan… Dole sai ka sa ta ta yi aiki ɗoriya akan wanda ya wuce wanda take yi…. Toh ka ga a yanayin ne sai dai a ji zuciyar ta tsaya cak wato CARDIAC ARREST.
Sai dai a ce Allah ya ji ƙanka kurum, da safe aiki ya ga makwabta na shirye-shiryen zuwa jana’izarka, kuma wallahi. Wanda kuma zuciyar ta ɗauke pressure ɗin toh shi kuma wajen inzali yake haɗuwa da massive stroke, jijiyar jini cikin kwanyarsa ta fashe.
Don haka ba zancen dole sai ka birge mace, nutsu ka san me kake ciki.
Gara ta kira ka da duk sunan da za ta kira ka, kar ka ji ƙasƙanci, minti 2, minti 3 ya wadatar. Ba gasar cin kofin Olympics ba ne da za ka nuna bajintar burge mutane, wannan abu ne daga kai sai ita, ko awa 2 kake babu wanda ya sani, ba kuma me buƙatar ya sani, amma ran da ka mutu a sama kowa sai ya ji.
Sannan ɗoriya akan haka musamman ga wanda suke sama da shekara 50 ina gargadinku da kar ku kuskura ku ce wai ku sai kun birge mace da har za ku je kuna ɗebe-ɗebe musamman yadda hawan jinin nan ya lalata mutane da yawa, za ku haɗu da mummunan bugun zuciya.
Ko matar da ka je ka hallaka kanka a kanta wallahi daga baya wani za ta je ta aura, in ma kai sa’a dama kai kaɗai ɗin ta tsarewa mutuncinta kenan tun kana raye. Don haka ku yi nazari kan wannan.
Don karanta rashin jini a jiki danna nan
ABIN DA BA KWA LURA
Mafi yawan mata daga cikin mu nan gamsuwar su ba a tsawon lokacin da ka ɗauka jikinmu ba ne, Eh kana iya jimawa mu ji daɗi amma ba ta hanyar shan magunguna ba, kwai hanyoyi da yawa da za ka jima ba lallai Sai ka sha magani ba, ku lura da ita, ka saurare ta, ka laƙanci duk wani sashi da take da rauni in ka taɓa ta ta nan, da haka za ka birge ta, ka yi tsafta, ka iya magana, ya zamto ana haɗa gado wajen bacci ba lallai sai yayin da ake buƙatar juna ba, banda fushi, banda ƙullata a rai, duk sanda ake da matsala a tattauna kar ku ɓoye alhalin a ranku kuna jin haushin juna, in kuka kiyaye wannan ba ku da matsala.
Uwa uba wani raunin azzakarin daga hormone ɗinsa ne, don haka hormone replacement therapy yake buƙata ya magance matsalar sa in ma gaban ne bai miƙewa da sauransu, wani ciwon suga gare shi ya lalata nerves da blood supply na mararsa… Shi yasa ba ya iya jima’i…ka ɗebi wannan shirmen magungunan ka ba shi ba dole ya mutu ba dama ga zuciyarsa kullum danƙare da sigar.
In kana da matsala tafi asibiti likita ya ganka ya duba ka ya ba ka maganin da ya dace shi ne zaman lafiya, amma kiyaye zuwa Chemist da ka, ko wajen masu maganin gargajiya ko Islamic chemist, Ku kiyayi kanku tun kafin zuciyarku ta zamo WEAK ku mutu a banza.
Allah yasa mu dace. A yi hattara.
Danna nan don karanta mata ku ba ni kunnenku
Edita; Rumasa’u M. Kallamu