ZAFAFA GOMA: ABUBUWA 10 DA MUSULMI YA KAMATA YA SANI SANNAN YA KIYAYE A LOKACIN AZUMIN WATAN RAMADANA.
GABATARWA:
Alhamdulillahi Rabbil ‘Alamin. Tsira da amincin Allah (SWT) su tabbata ga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم, iyalansa da sahabbansa baki ɗaya. Muna yi wa Allah (SWT) godiya da Ya raya mu har muka sake gamuwa da watan Ramadan, watan rahama, gafara da tsira daga wutar Jahannama.
Ibadar azumin ramadana ibada ce wacce ta samo asali da umarni daga Allah (SWT) kuma ibada ce wacce aka umarci al’ummomin baya da ita. Dalilin haka shi ne faɗin Allah (SWT) “ya ku waɗanda suka yi imani an farlanta muku azumi kamar yadda aka farlanta ma waɗanda suka gabace ku domin ku yi taƙawa”. Duba bakara: 2:183.
Haka kuma Allah (SWT) yana cewa “watan ramadana shi ne wanda aka saukar da alkur’ani a cikinsa domin zama shiriya ga mutane……”Duba bakara: 2:185. Haka zalika, An ruwaito manzon Allah (SWT) yana cewa: “ haƙiƙa watan Ramadana ya zo muku. Wata ne mai albarka. Allah yana lulluɓeku (da rahamar sa) a lokacin sa.
Yana saukar da jin ƙan sa, yana kankare zunubai kuma yana karɓar addu’o’i. Allah yana kallon tsere da kuke yi ta ɓangaren kyawawan ayyukan ku sannan ya sanar da mala’iku cikin girmama ku. Saboda haka ku nuwa Allah nagartar ku. Tabbas matsiyaci shi ne wanda ya kasa samun rahamar Allah a lokacin Ramadan ”Duba “ Majma’uz-zaw’id 3:142
Haka kuma Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yace “duk wanda ya azumci Ramadana yana mai imani da kwaɗayin samun lada, za a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka
gabata….”.Duba Bukhari 2014 da muslim 759-760. A wani hadisin ƙudusi Allah (SWT) yana cewa “ dukkanin aiki (mai kyau) na ɗan-adam da ya yi yana da lada goma kwatankwacinsa har zuwa ɗari bakwai amma banda azumi.
Haƙiƙa azumi nawa ne kuma ni zany ni sakayyarsa. Shi mai azumi ya bar cinsa da shansa, da sha’awarsa saboda umarni na” manzon Allah ya cigaba da cewa “ mai azumi yana da farin ciki har guda biyu. Farin ciki lokacin da yake buɗa baki da kuma farin ciki lokacin da zai haɗu da ubangijinsa” ….Duba Bukhari 1904 da muslim 161-1151
A cikin wannan taƙaitacciyar tunatarwa, na ambaci abubuwa goma da Musulmi ya kamata ya kiyaye domin azuminsa ya zama karɓaɓɓe mai cike da falala. Allah (SWT) ya ba mu ikon amfana da wannan tunatarwa da kuma ikon aiki da waɗanan abubuwa (ZAFAFA GOMA) domin rabauta da dacewa.
NA FARKO: NIYYA
Azumi ibada ce, kuma ibada ba ta inganta sai da niyya tun daga dare kafin a tashi
da azumi. Wajibi ne mutum ya ƙulla niyyar azumi da zarar an ga wata tun kafin ya
kwanta bacci ko kuma kafin fitowar alfijir.
Hujja: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce:“Duk wanda bai yi niyyar azumi da dare ba, babu azumi a gare shi.” (Abu Dawud, Tirmizi)
NA BIYU: ƊAUKAR AZUMI DA GANIN WATA
Azumin Ramadana yana farawa ne da ganin wata ko kuma cikar wata (sha‟aban zuwa 30) kuma yana ƙarewa da ganin wata (na shawwal).
Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:“Ku yi azumi idan kun ga wata, ku buɗa azumi idan kun gan shi. ”(Bukhari da Muslim)
NA UKU: TSAYAWA DA SALLOLIN FARILLA
Ko da mutum yana azumi, idan ya raina sallah, ya jefa kansa cikin haɗari. Allah (SWT) yana cewa “ ku kiyaye sallolin ku musammam sallar (tsakiya) La‟asar….. Duba bakara 2:238
Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:“Abu na farko da za a tambayi bawa a ranar Alƙiyama shi ne sallah….” (Tirmizi)
NA HUƊU: YAWAITA KARATUN AL-KUR’ANI
Ramadan wata ne na Al-Kur‟ani, don haka ake ƙwaɗaitar da musulmi da ya dage
wajen yawaita tilawa da sauraron alkurani ba dare ba rana. Karatun alkurani shi ne
zikiri mafi girma kuma a watan ramadana aka saukar da shi.
Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya kasance duk watan ramadana mala‟ika Jibril yana zuwa sau biyu wajen sa domin tilawar alkurani tare da shi kuma an ruwaito sahabbai da magabata sun kasance suna duƙufa ba dare ba rana wajen raya dukkan kwanaki da karatun alkurani. Ana so mutum ya shagaltu sosai da karatun alkurani kuma ya zama shine mafi yawan ibadar sa acikin ramadana.
Hujja: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce:“Ku karanta Al-Kur‟ani, domin lallai shi zai zo ranar Alƙiyama yana yi wa masu shi ceto.” (Muslim)
NA BIYAR: YAWAN ZIKIRI
Zikiri yana rayar da zuciya kuma yana ɗaga darajar bawa.
Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:“Kalmomi biyu ne masu sauƙi a harshe, masu nauyi a sikeli, masu soyuwa ga Rahama…” (Bukhari da Muslim)
NA SHIDA: YAWAITA SALATI GA ANNABI صلى الله عليه وسلم.
Salati hanya ce ta samun rahamar Allah. Don haka yawaita salati ga manzon Allah
صلى الله عليه وسلم a kowane lokaci ibada ce mai albarka da ɗimbin lada musammam kuma a lokacin azumi.
Hujja: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce:“Duk wanda ya yi mini salati sau ɗaya, Allah zai yi masa sau goma.” (Muslim)
NA BAKWAI: YAWAITA ADDU’A, MUSAMMAN A SAHUR DA BUƊA BAKI
Mai azumi yana da matsayi na musamman wajen Allah. Lokacin da bawa ke azumi
lokaci ne na addu’a gaba ɗaya amma kuma akwai keɓaɓɓun gurare da aka ayyana cewa
ana so a yawaita addua kamar lokacin buɗa baki da lokacin sahur da sauransu.
Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:“Mai azumi yana da addu‟a wadda ba a mayar masa da ita ba a lokacin buɗa bakinsa.” (Tirmizi)
NA TAKWAS: SALLAR TARAWIHI DA TSAYUWAR DARE
Wannan wata dama ce ta gafara da gyaran rayuwa.
Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: “idan mutum ya tsaya domin sallar dare (tarawih ko ƙiyamul laili) tare da liman har aka ƙare sallar, Allah zai rubuta masa lada kamar wanda ya raya daren gaba ɗaya da sallah.” (Abu dawud 1375)
NA TARA: SADAKA DA CIYAR DA MAI AZUMI
Ramadan wata ne na tausayi da taimakon juna.
Hujja: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce: “Duk wanda ya ciyar da mai azumi, zai samu irin ladan azuminsa.” (Tirmizi)
NA GOMA: I’ITIKAFI, ZAKATUL FITR DA UMARA GA MAI HALI
Goman ƙarshe lokaci ne na ƙara kusanci da Allah da dagewa sosai domin ƙara yawaita ibadu musammam a kwanakin da ake sa ran dacewa da lailatul kadari watau daren 21, 23, 25, 27 da kuma 29. I’itikafi ibada ce mai tarin lada da samun kusanci da Allah (SWT) kuma ana shiga I’itikafi ne a goman ƙarshe a Ramadan.
Haka, zakkar fidda kai (zakatul fitr) ibace wacce aka shar’anta ta a kan dukkan musulmi namiji ko mace, babba ko yaro ko ɗan jariri kowa ana fitar masa da zakkar
fidda kai.
Hujja: An rawaito cewa Annabi صلى الله عليه وسلم yana yin I’itikafi a goman ƙarshe na Ramadan.(Bukhari). Haka kuma ya wajabta Zakatul Fitr (zakkar fidda kai) domin tsarkake azumi, kuma ya ce: “Umara a Ramadan tana da ladan Hajji.” (Bukhari da Muslim).
‘Ƴan uwa masu girma haƙiƙa duk wanda ya kiyaye waɗannan abubuwa goma, ya yi azuminsa da ikhlasi, to da yardar Allah zai samu cikakkiyar falalar Ramadan wanda Allah kaɗai ne ya barwa kansa sanin irin tanadin ladan da zai ba shi. Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana zunubanmu, Ya sa mu dace da Lailatul Qadr.
Ameen.
Husain M. Inuwa.
usainiskima@gmail.com
09042152353
Danna nan don karanta Shan Azumi Ga Matafiya
Edita@rumasau-kallamu








