Bahaushe ya riqi sana’o’i da dama da aka yi bayaninsu a sama don samun abun dogaro da kai. Bahaushe kan adana kuxinsa a adaka, ko asusu. (Yakasai, 2012). Bahaushe yana gina rumbun ajiyar abincin na ci, ko na shekara ko zuwa wani lokaci.
Tun ma kafin zuwan addinin Musulunci, Bahaushe na tara haraji, jangali, kuxin fansa da ganimar yaqi don gudanar da aiyukan raya qasa da samar da tsaro. Bayan zuwan Musulunci sarakuna suka qara da sarautar sa’i (mai tattara zakkah). Da Bature ma ya zo, ya ci gaba da karvar harajin kasuwa da manoma.