Ma’anar Bahaushe

0
29

Kalmar Bahaushe tana da ma’ana ta fuskokin harshe,  al’ada ko gado, siyasa, addini, wurin zama (muhalli) ko  xabi’ar mutum. 

Ta fuskar harshe, shi ne wanda harshensa na farko (L1)  Hausa ne, kuma ba ya jin kowanne harshe sai Hausa, ita  ce harshensa na mu’amalar yau da gobe (Bunza, 1990). 

Ta fuskar gado, shi ne wanda iyayensa da kakaninsa  Hausawa ne, koda shi ba ya jin Hausa (Bunza, 1990). 

Ta fuskar siyasa, Bahaushe shi ne wanda ya zauna ko  aka haife shi a qasar Hausa na sama da shekara ashirin,  koda iyayensa da kakaninsa ba Hausawa ne. Wannan  jimawar za ta ba shi damar amfani da harshen, da xabi’a  irin ta Bahaushe. Ta wannan fuskar, sauran qabilu ma na  iya zama Hausawa (Manby, 2016). 

Domin Karanta wane ne bahaushe Danna Nan

Ta fuskar addini, wasu na ganin wanda ba ya addinin  Hausawa, ba Bahaushe ba ne, shi ya sa Hausawa kan  cewa ‘yan uwansu da ba su karvi addinin Musulunci ba  da suna: Maguzawa (jam’i), Bamaguje (namiji),  Bamagujiya (mace) (Bunza, 1990). 

Ta fuskar muhalli (wurin zama), Bahaushe shi ne wanda  yake zaune a qasar Hausa (Bunza, 1990 da Adamu 1978) Smith (1970) duk mutumin da yake rayuwa a qasar  Hausa daga a qarni na 15th a lokacin garuruwan Hausa  sun kafu shi ne Bahaushe, sannan harshen Hausa ne  babbar alamar da za a iya gane Bahaushe da shi. 

Ta fuskar xabi’a, Bahaushe shi ne wanda ya tasirantu da  al’adun Hausawa suka yi tasiri a rayuwarsa ta yau da  kullum, koda ba Bahaushe ba ne (Bunza, 1990 da  Adamu 1978). 

Wasu kuma na kallo Bahaushe da fuska uku, Have,  Hausa-Fulani (Kaxo) da Banza. Havawa su ne asalin  Hausawa waxanda suka haxa da qabilun Gobirawa,  Kabawa, Rumawa, Adarawa da Maouri sune masu mulki qasar Hausa kafin zuwan Jihadin Fulani da Shehu  Usman Xanfodiyo (Omniglot, 2015)  

Hausa-Fulani, asali mutanen kudancin Nijeriya ne suka  qirqiro kalmar, don dunqule al’ummar Hausawa da  Fulani saboda alaqar kut-da-kut tsakanin Bahaushe da  Fillace. Fulani na zaune a qasar Hausa ta dalilin  auratayya, kiwo, kasuwanci ko neman ilimi tun kafuwar  Daular Sokoto. Waxannan Fulanin suna jin harshen  Hausa sosai, kuma sun xabi’antu da xabi’ar Bahaushe,  daga cikin qabilun Fulani akwai; Jovawa, DambazawaMudubawa, Mallawa da Sulluvawa da suke da asali daga  Futa Toor, ko Fouta Djallon ko Wolof (yanki da ke  tsakanin Senegal da Mauritania a yau).

Domin Karanta Al’adar Bahaushe Danna nan 

Su kuma Banza  jikokin Karaf-da-Gari ne mazauna garuruwan da jikokin  Bayajidda suka kafa. Su Hausawa ne da suka haxu da  wasu qabilun mazauna Illorin (tare da Yarbawa),  Gwarawa, Ajawa, gere, Bankal da wasu. Sune idan suka  yi magana da karin harshensu ake ce musu ‘gwarawa’,  ko ‘bagwari’.  

A yau, abu ne mai wuya a samu asalin Bahaushe, saboda  autayayya tsakanin wasu qabilu, hakan na nufin sauyin  halitta, yanayi da kama, Bahaushe ya yi auratayya da Fulani, Nupe, Kanuri, Shuwa, da sauran qabilun  Kudancin Nijeriya. Bahaushe a yau, haxuwar qabilu ce  daban-daban, da ke rayuwa Arewacin Nijeriya,  Kudancin Nijar, da sauran sassan duniya (Malumfashi,  2018). 

Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
labarin da ya wuceBayajidda da Tarihin Bahaushe
Labarin na GabaHarshen Bahaushe (Harshen Hausa)