Yadda Ake Faten Tsaki Da Wake

0
37

Fate abincin gargajiya ne wanda ya samo asali tun iyaye da kakanni. Yana ƙunshe da ganyayyaki masu ƙunshe da sinadarai waɗanda ke inganta lafiyar jiki.

Abubuwan da ake buƙata idan za a yi wannan fate su ne:

  • Wake
  • Tsaki
  • Kayan miya
  • Mai
  • Alayyahu
  • Yakuwa
  • Kabewa
  • Gyaɗar miya
  • Sinadarin ɗanɗano
  • Gishiri da kuma 
  • Tantaƙwashi

Da farko za ki dafa wake ya dahu ya yi luguf, sai ki ajiye shi a gefe. Sai ki zuba tantaƙwashi a tukunya ki ɗora a kan wuta, sannan ki zuba gishiri da sinadarin ɗanɗano da kayan ƙamshi a ciki. Ki bar shi ya dahu na tsawon minti goma zuwa sha biyar. Daga nan sai ki zuba kabewa da kayan miya a ciki, sai kuma ki ƙara ruwa madaidaici.

Bayan ya tafasa na tsawon minti goma sai ki kawo tsakin nan (wankakken tsaki) ki zuba, sai ki zuba sinadarin ɗanɗano da gishiri daidai gwargwado. Bayan kamar minti shida zuwa bakwai, sai ki ɗakko dafaffen waken nan ki zuba, ki zuba gyaɗar miya da alayyahu da kuma yakuwa. Sai ki ɗan zuba mai ki jujjuya, sai ki rufe ki rage wuta sosai.

Bayan kamar minti biyar sai sauke. 

Domin tuntuɓa ko ƙarin bayani a kira 07030353500

Ko kuma ka je kai tsaye cikin tasharmu ta Wikihausa 

 Don ganin yadda ake Faten doya da wake danna nan 

labarin da ya wuceYadda Alamomin Jinnu Yake
Labarin na GabaShin Menene Sihiri?