Addinin musulunci addini ne da ya girmama ɗan Adam ya mutunta shi ya kuma yi umarni da ya kare mutuncinsa ya girmama kansa kada ya wulaƙanta kansa da kansa ya zubar da ƙimar sa ta ɗan Adam.
Domin tabbatar da wannan manufa Allah ta’ala ya umarci kowa ya tashi ya zage dantse wajen neman na kan sa; ya yi umarni ya kasance mai wadatar zuci da godiya ga Allah ta’ala; kuma ya hana bara, roƙo, maula, bambaɗanci da sauran su.
Wannan ɗabi’a ce mummuna wacce take kashe zuciyar mutum ta haifar masa da talauci da ƙasƙancin a duniya da lahira. A duniya talauci zai aure shi ya mamaye shi, a lahira kuma zai tashi babu tsokar nama ko ɗaya a fuskar sa.
Duk abin da mai karɓe-karɓe yake samu haramun ne tsantsa sai dai in yana da wani dalili da shari’a ta yarda shi; wanda ya halatta masa yin roƙon kamar yadda za a kawo hadisai da suke magana akan hakan.
Ya Allah ka ba mu wadatar zuci ka ba mu ikon godiya a gare ka da dagewa wajen neman halal; ka tsare mu da cin haram da zubar da mutunci mu wajen roƙe-roƙe. Amin Summa Amin.
Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Wadatar Zuci Take danna nan.
Domin karanta cikakken bayani akan Wane Ne Bahaushe? danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Jerin Littattafan Hadisai Arba’in (40) Littafi Na Biyu; Akan (Falalar Wadatar Zuci, Neman Halal Godiya Ga Allah Da Illolin Bara Da Roƙo); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.