Ɗabi’ar Gyaran Jiki A Yau, Shin Ina Hakan Zai Kai Mu

0
27

Al’amarin sankarar nono “Breast cancer” nema yake ya zama tamkar wani zazzaɓin cizon sauro na Malaria, matsalar kullum ƙara ƙamari take,abin takaici gwamnati ba abinda take akai, munin matsalar ya wuce duk yada kuke tunani amma inda wacce tasan me matsalar ko wata wacce ta rasa nonuwanta dalilin matsalar zata fahimta. 

A matsala irin wannan masu maganin gargajiya da Islamic chemist dinnan bawani abu da zasu iya yi akai,ba taimakawa suke ba, galibi damfara ce, tunda bazaka taɓa ganin sun kawo mutum guda da za zasu bugi kirji suce su suka warkar dashi ba, babu kaf,naga macen da ta kashe sama da Naira Milyan 5 dalilin matsalar nono hannunsu tare da kin zuwa asibiti, sai a karshe data ga uwar bari. 

Wanda tun farko da zakace kije asibiti a dubaki tunda wuri in ma ƙari ne acire ko kuma in kansa ce a fara chemo za suce ma ba kuɗi. 

Domin karanta bayani akan Warin Baki (Mouth Odour) Danna nan

Suko masu wadancan magungunan kurum cewa zasuyi bada kaza mu baki magani kisha zaki warke tas…suna iya dunkule cutuka 10 su baki magani guda suce duk zai warkar,toh banda kuma kana nun ƴan damfara da sun ma fi kowa illa mutum yazo da magani yana Naira 50 guda uku N100, kullum a haka mutanen mu ke sake da ciwo har sai ya ci karfinsu. ko yadda ake tallan maganin sanyi, shawara, rana basir ya dace ace zuwa yanzu wannan cuttukan sun zama tarihi a Nigeria amma ina saidai kullum aita sha domin dama karya ne.

Kuyi haƙuri masu magungunan nan amma dole na faɗi gaskiya,bakwa fadawa mutane gaskiya, ita kuma gwamnati indai zata sami haraji bata da damuwa, mutum yaje yaita hawking dinsa cikin taron mutane.

Galibi sanda mata zasu zo asibiti sai cancer ɗin ta tashi daga nono ta ƴadu zuwa sauran sassan jiki inda ba abinda zaka iya na hanasu tunkarar mutuwa.

Domin sanin menene Cutar Dundumi Ko Ganin Hazo-Hazo Danna nan

Gwamnati ba abinda ya dameta da wannan gagarumar matsala, illa iyaka surutunsu su kenan batun siyasa, fyaɗe, ƴancin mata, batun auren jinsi da sauran shirme,babu wata hukumar me zaman kanta dake ƙokarin zuba kuɗi ai binkice domin yaƙi da cutar cancer nono cikin mu,hankalinsu ma bakan nonon yake ba ballantana a fara binkice.

Abu guda ne dai nasani duk wadannan abubuwan da aketa magana dake haddasa kansar nono [risk factors] tabbas kwai wani boyayyen hatsarin da binkice ne kaɗai zaisa a ganosa, domin a yadda larurar ke fantsama akwai wani muhimmin abin da binkice ne kurum zai tabbatar, saidai ba’a ma fara ba kuma babu tunanin yi, wanda yana iya daukar shekaru 10 kafin ya kammala,don haka kowa yai ta kansa, musamman mata,ita ce lamba daya cikin cancer din dake kashe mana mata a yanzu.

A da wannan larurar ba common bace tsakanin mata masu matsakaitan shekaru, wato yan shekaru kasa da 45, galibi sai manya wanda ma suka daina haila amma ayanzu galibin wanda muke samu ko kusa da shekara 50 ma basuyi ba, Infact har Ƴar 20yrs, 27yrs, 32yrs 33yrs, duk mun samesu ballanta kuma yan 35 zuwa 40yrs.

Kusan cewa Haihuwa A Gida Ba Jarumta Bane Kuskure Ne Danna nan domin sanin dalili

Wata baiwar Allah yar shekaru 27 da tazo asibiti kwanaki gaba ɗaya tana cuso kai cikin emergency ɗinnan.. ba wanda hankali da zuciyarsa basu shiga damuwa tare da sanin wani mummunan abu yazo ba…. saboda wani irin mugun wari da gurin ya kaure dashi, tunda ta shigo ba’a kara samun iska me daɗi ba.

Bakomi bane ke wari sai nononta! inka kalla sau ɗaya In banda dole bazakai marmarin ƙara bude ido ka gansa ba, irin yadda yai wani bulli yayo cunkus, yai ɓamɓaronki, yai rami wani mugunyar ruwa me ɗoyi ke fitowa ta ciki, duk ya jiƙe gaban hijab din, ko zama sak bata iyawa saboda azaba…  wayyo Allah kurum take faɗi, nidai saida nai kwana na yini inajin wannan warin a hancina, wai ma sunan nasa face mask kenan.

Wata kwanaki data zo Allah likitan da ya kalla anan ya zube ƙasa ya sami syncope sai daga baya akai Resuscitation dinsa, ka rasa irin jahilicin da muke ciki, ai ko bani da ko sisi gara ai wacce za ai dana zauna gida da wannan abin ajika. Saidai ai kwaɓa abubuwa ana ƙara mulkawa jiki. 

To haka muke fama, baza a taho asibiti ba tun farko mutum inyaji matsala sai yaita bin gurin masu magungunan gargajiya suna nuna zasu warkar dashi amma a banza sai a karshe matsala taci karfin mutum sannan zai doso asibiti, kuma koya akai maganar kudi mutum ya shiga tashin hankali bayan da tun farko yazo kafin matsalar ta girma da saidai ai wani zancen amma ba yadda za’ai gwaje-gwajen da kudin aikin suke tsadar haka,wata saita ɓata dubunnai gun masu magungunan gargajiya ko Islamic chemist a banza wanda da asibiti tazo ba haka ba.

Domin karanta Yadda Zaka Bada Agajin Gaggawa Ga Wanda Ya Sha Kananzir (Kerosene) Danna nan 

Ita cancer ta wuce wasa, daga cancer din nono tana iya yaduwa zuwa huhu, hanta, ƙwaƙwalwa da dukkan wani sassan jiki, kuma intai wannan ba wani aiki da za kaiwa mutum ta zamo advanced’ saidai aita tafiya a hankali har ranar da ALLAH zai rabaka da mutum (mutuwa), wanda suke samu muyi aiki a yanke nonuwan adorasu kan chemo wannan fa sune wanda suka cika da imani kenan… don intai ƙamari bama bata lokacin cire nonon haka zamu barsa yaita zugwanyewa ahankali don aikin ciresa ba zai taimaka da komi ba. 

Shiyasa kwai ban haushi mutum ya share duwawu ya zauna har sai anfara kyamatarsa cikin mutane, saboda yana wari sannan ya doshi asibiti yana zaton likita zai masa siddabaru ya warkar dashi lokaci guda.

Wannan shine video na links irin yadda cancer kan yiwa nono ku gani da idonku: yadda cancer kan yiwa nono

Don haka bayin Allah musamman kannen mu da yayyen mu mata kuyi karatun ta nutsu.

Wannan kansar ta nono jikinku babban abinda ke taka rawa shine sinadarin Iyistrojin (estrogen), shi kuma wannan estrogen dama ajikinku yake, shine sinadarin da ya bambanta jikin mace dana namiji, shi ke haɓɓaƙa sha’awar ku, girman nonuwa, haila, daukar ciki zuwa haihuwa… Duk yana cikin aikinsa.

Toh ita wannan cancer muddin ya zamto jikin mace na cigaba da samun exposure da estrogen’ wato ya zamto ya cigaba da fita akai-akai batare da jikin mace na samun hutu ko tazara ba wannan shine babban hatsarin dake kai mace ga kansar nono, duk ture wani batu na tarihin ciwon cikin yan uwa, shan taba, da sauransu,wannan exposure din da jikin ke samu da estrogen shine muhimmin kuma akansa ne ya dace hukumomi a dukufa binkice a nemo yadda za ai.

Jiki Na Samun Exposure Ne Kamar Haka:
  • Fara haila da wuri ga mata, wato duk wacce ta fara haila tana yar tsakanin shekaru 10, 11, 12, 13 zuwa 14 wannan hatsari ne,domin hakan na nuna ta fara samun exposure da estrogen tun tana kankanuwa kuma haka abin zai zarce tunda duk wata sai tai haila, don haka dogon lokacin da zata dauka tana haila kafin ta cimma shekarun daina wa nada yawa ba kamar na wacce ta fara a 15yrs ba, hakan ke nuna hatsarin kamuwarta da ciwon
  • Rashin haihuwa da jinkirin aure kafin a dauki ciki… wannan ma suna exposing jiki ga estrogen, domin kunsan idan mace tai ciki to bata haila, har sai ta haihu, toh wannan watannin goyon cikin kariya ne ga jikinta, yana hana exposing jikinta ga estrogen, shyasa yawan haihuwa kariya ne,haka wacce aure yai mata jinkiri jikin zai cigaba da samun exposure tunda duk wata cikin haila take don haka kwai hatsarin ciwon tattare da ita.
  •  Rashin shayarwa, sanda ake shayarwa hakan kan dakile tasirin hauhawar estrogen ajika, ga matan da basa shayarwa ko kuwa basa yin cikakkiya yan watanni kadan sun yaye yaro saboda wani dalili nasu… To wannan gagarumin hatsari ne dake kusanta ki ga cancer nono da ayau ta zamo ruwan dare.
  •  Magungunan tazarar haihuwa, wannan magunguna galibi cikinsu akaran kansu dama suna kunshe da estrogen don haka gwargwadon jimawa da mace tai akansu gwargwadon hatsarin ta, duk da koda na wata 1 ne wata ya isa ya haddasa komi a zubin jikinta, wannan kuwa walau nasha, allura ko implant… Muddin masu kunshe da estrogen ne to kwai hatsarin kamuwa da kansa, shyasa sai an tantance mutum ma ake dorasa, yadda in aka ga matsala ana iya canza masa da magani mara estrogen a bashi iya me progesterone inma planning ya zama dole.
  • Shaye shayen magungunan mata da ya fantsama cikin al’umma. Wannan magungunan bazasuyi muku abinda suke muku ba inda babu estrogen a ciki, wanda ni ayau shi nafi dorawa laifin yawan adadin cancer da muke samu, domin wallahi inda kasan malaria yanzu haka samun mata da cancer nono yake. Wallahi duk masu wani gyaran nonon nan, hips da farji ku kuka da kanku, I’m serious…. Not joking. Kunga hatta wannan hulba da kuke raina wa da kuke amfani da ita wajen gyaran nono tana da estrogen cikinta sosai, shine ma yasa nonuwan ke tashi, in babu estrogen nono bai taba girma, duk wannan shirin da akema yarinya kafin aure da wanda ke gidan miji estrogen ne ake exposing jikinsu garesa. Don haka ai hattara
  • Jinkirin tsayawar haila, mace ta haura 50 ko 52 ba tare da ta daina haila ba hakan na nufin jikinta na cigaba da samun exposure da estrogen don haka kwai yiwuwar kamuwa da cutar breast cancer gareta.
Wannan sune muhimman hanyoyin da matan mu ke samun exposure da estrogen

Musamman al’amarin kayan matan nan yadda da yawa suka rungume sa ba inda zai kawo su karshe sai nan, cancer nono saima zuwa gaba. Kome matan mu dambarawa nono suke indai zasuyi girma ko su taso shikenan, amma tunanin ko me zai faru gaba sam ba ruwan su, shin kina jin mazan yanzu kaso 90% cikin 100% zasu zauna dake gaba in kin sami matsala a nono?

Mara lafiya na fama da kanta cancer nono ta ƴadu zuwa huhu cikin oxygen amma a haka mijinta ya saketa saboda ya gaji. Yai cacar kudi, nasa sun kare ya shiga cin bashi har ya rasa me bashi,… Babban abinda yaja hankali na da naga yan uwanta basu zargesa ba, budar baki cewa sukai gajiya yai… Bazamu ga laifinsa ba munsan me yayi. Karshe dai mutuwa tayi dama.

Kuma wasu zaka samu nada hawan jini basu sani ba, wasu kuma sun san suna dashi, amma gani suke ba matsala a irin abubuwan da suke sha…. Toh kusani shan wannan abubuwan ko shafasu gareki na kusantaki ga hatsarin samun shanyewar barin jiki baya ga cancer, kwai hatsarin hemorrhagic strokes…  Wato fashewar jijiyar jini a cikin kwakwalwa musamman a basal ganglia ko nucleic. Haka Koda baki da hawan jini, domin binkice ya tabbatar da hakan. Matan turawa duk basusan wannan haukan ba ballantana, kuma suna rike da mazan su,ballantana kuma ke da kina budurwa baki  yi aure ba amma kina exposing kanki ga estrogen bayan koda haila aka barki ta isheki hatsari amma sai shaye shayen abubuwa kike don ki tada nono.

Domin karanta bayani akan Warin Baki (Mouth Odour) Danna nan

Basal Nucleic wani network ne na jijiyoyin dake da alhaki wajen sarrafa motsin jikin mu na tafiya, ɗaga hannuwa da duk wani motsi, hakan wajen koyon abubuwa, zartar da abubuwa ko umarnin ayi, sarrafa ɗabi’un mutum da jin tausayi ko damuwa da halin da wani ke ciki, ko jin babu daɗi ko farin ciki in wani abu ya afku. Toh daga sanda wannan sashin a kwakwalwa ya sami matsala duk wadannan ayyukan nasa cikas zasu samu, kuna dai ganin yadda masu strokes ke kasancewa; jiki a jirkice, baki a kaikaice, magana bata fita, abinci baya ciyuwa a daɗin rai dadai sauran ɗawainiya da mai jinya har sai ya gajiya.

Toh daya daga cikin illar shaye-shayen da shafe-shafen wadannan supplements din kenan dake haɓɓaƙa shauƙin jima’i ga mata wanda aka fi fahimta da kayan mata, domin karara ansami cases din da hakan jita faru, Infact ita wannan sau daya tak tasha shikenan ya jawo mata strokes. Domin na faɗa, estrogen shine kacokan sinadarin da ke da alhakin haɓɓaƙa wannan abubuwan a mata, kuma shine ke cusasu a hatsarin cancer da shanyewar ɓarin jiki.

Batun maganin matsi, tsarki da wani ruwa ko wani turare kuwa…. dama wannan ku kuka da kanku kuna interfering da PH na vagina, kuma kansar bakin mahaifa da farji na nan na kwankwasa muku kofa akwana atashi. Maggots wato tsutsotsi haka zaka gani a farjin mace. amma ku ban hankalinku zuwa cikin wannan links din muga wani abu: Danna nan domin kallan video din 

Bari na takaita anan ba don na kammala fadin komi ba. Amma dai ya dace kowacce mace tai karatun ta nutsu. Bance kar mace ta lura da kanta ba, amma duk gyaran jiki ba sama da samun isashshen bacci, cin ingantaccen abinci, shan fruits, wanka, wanki, iya mu’amala, sanin bukatun miji da haƙuri da rayuwa. Wannan zasu kaiki dukkan matsayi gurin miji koda an cire miki nonuwa bazai taɓa dena sonki ba, domin ke din da halayenki yake so. In kunne yaji jiki ya tsira. Nayi nawa saura naku. 

labarin da ya wuceHaihuwa A Gida Ba Jarumta Bane Kuskure Ne
Labarin na GabaƘaiƙayin Matsematsi (Jock itch)