Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Cheaply - A turance tana nufin bulus. Misali; Ya siyi gidan a bulus saboda mai gidan kuɗi yake buƙata. HAU; Bulus (Tana nufin samun abu a arha ba tare da an sha wahala)
Cheat/Trick - A turance tana nufin damfara. Misali; Samari na koyon damfara ta hanyar yanar gizo sosai. HAU; Damfara (Tana nufin a cutar da mutum ta hanyar yin dabaru a ƙwace masa kuɗi ko wani abu)
Cheek - A turance tana nufin kunci. Misali; Ya sha mari a gefen kuncinsa na hagu. HAU; Kunci (Tana nufin gefen fuska na hagu ko na dama)
Cheeks - A turance tana nufin kumatu. Misali; Fauziya ta shafa hoda a kumatu. HAU; Kumatu (Tana nufin jam'in kunci wato gefen fuska na hagu ko na dama)  
Chemical Society of Nigeria (CSN) - Ƙungiyar masana sinadarai ta Najeriya
Chemical Society of Nigeria (CSN) - Ƙungiyar masana sinadarai ta Najeriya
Chewing Stick - A turance yana nufin asawaki. Misali; Na tarar yana asawaki da na je gidan. HAU; Asawaki (Itace ne da ake goge haƙora da shi)
Chicken/Hen - A turance tana nufin kaji. Misali; An soya kaji za a yi mana miya da su. HAU; Kaji (Tana nufin jam'in kaza)
China Radio International (CRI) - Gidan Rediyon caina /sin
Christian - A turance tana nufin kirista. Misali; Makociyata kirista ce, kuma muna zaman lafiya sosai. HAU; Kirista (Tana nufin mabiya addinin kiristanci wato ahalil kitabi)
1 48 49 50 51 52 300