Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Woman’s Large Wrapper - A turance tana nufin gyauto. Misali; Ta ɗaura gyauto mai matuƙar kyau da tsada. HAU; Gyauto (Tana nufin babban zani na mata)
Woman’s Shawl - A turance tana nufin gyale. Misali; Kande ta yafa sabon gyale. HAU; Gyale (Tana nufin mayafi ko abin rufe jiki na mata)
Woman’s Underskirt - A turance tana nufin fatari. Misali; Ta shanya fatari a igiya bayan ta wanke. HAU; Fatari (Tana nufin siket ɗin da mata suke sa wa a ƙasan kaya)
Women Trafficking & Child Labour Eradication Foundation (WOTCLEF) - Kadaurar Daƙile Safarar Mata da Bautar da Yara
Wood - A turance tana nufin icce. Misali; Idan aka samu icce busasshe wuta tana saurin kamawa. HAU; Icce (Tana nufin reshe ko gangar jikin bishiya da ake amfani da shi wajen hura wuta a yi girki)
Wooden Ladle - A turance tana nufin ƙoshiya. Misali: Ta jujjuya miyar da ƙoshiya kafin ta sauke tukunya. HAU: Ƙoshiya (Tana nufin cokali ko babban abin juyawa da aka yi da duma, wanda ake amfani da shi wajen ɗiba ko jujjuya abinci)
Words/Speech - A turance tana nufin kalami. Misali; Ya iya kalami mai daɗi shi yasa mutane ke son shi. HAU; Kalami (Tana nufin zance ko magana)
World Association of Newspapers (WAN) - Kadaurar Kamfanonin Jarida Ta Duniya
World Bank - Bankin Duniya
World Boxing Association (WBA) - Ƙungiyar 'Yandambe Ta Duniya
1 316 317 318 319 320 337