Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Whirlwind - A turance tana nufin guguwa. Misali; Bishiyar ta faɗo ne yayin da ake guguwa. HAU; Guguwa (Tana nufin iska mai ƙarfi)
Whistling - A turance tana nufin fito. Misali; Waye yake fito a waje? HAU; Fito (Tana nufin fitar da iska da baki har ya ba da wata siririyar ƙara)
Whole - A turance tana nufin ilahiri. Misali; Ya shafe ilahirin jikinsa da maganin. HAU; Ilahiri (Tana nufin duka ko gaba ɗaya ko bai ɗaya)
Wife of Gizo (a trickster hero in Hausa folklore) - A turance tana nufin Ƙoƙi. Misali: A tatsuniyar jiya, Ƙoƙi ta taimaka wa Gizo wajen warware matsalolinsa. HAU: Ƙoƙi (Tana nufin matar Gizo, wanda sanannen jarumi ne mai dabara a tatsuniyoyin Hausawa. Ana yawan ambatonta a cikin labaran gargajiya tare da Gizo)
wikiHausa - wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.
Wisdom - A turance tana nufin hikima. Misali; Ya yi amfani da hikima wajen daidaita abokan da suka samu saɓani. HAU; Hikima (Tana nufin dabara ko baiwa)
Wish - A turance tana nufin buri. Misali; Zuwa ƙasa mai tsarki shi ne babban buri na. HAU; Buri (Tana nufin abinda mutum yake so ya cimma)
With - A turance tana nufin da. Misali; Ni da yayana farare ne. HAU; Da (Tana nufin tare)
Without - A turance tana nufin babu. Misali; Babu kaya a cikin akwatin. HAU; Babu (Tana nufin wayam ko ba komai)
Woman’s Head-tie - A turance tana nufin kallabi. Misali; Ƙanwata ta iya ɗaura kallabi. HAU; Kallabi (Tana nufin ɗan kwali ko fatala)
1 315 316 317 318 319 337