Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Worth, Value - A turance tana nufin daraja.
Misali; Zinare na da daraja a halin yanzu.
HAU; Daraja (Tana nufin muhimmanci ko tsada)
Wrestling - A turance tana nufin kokawa.
Misali; Su Lado sun tafi kallon kokawa a dandali.
HAU; Kokawa (Tana nufin ɗaya daga cikin wasannin gargajiya, inda maza biyu ke doke-doke a tsakaninsu har a kayar da ɗaya)
Yam - A turance tana nufin doya.
Misali; Doya za mu dafa yau da rana.
HAU; Doya (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abinci wanda ke sa ƙarfin jiki)
Yandagaji - Waɗanda ba kwararrun 'yanwasa ba a harkar wasanni.
Yawning - A turance tana nufin hamma.
Misali; Tun ɗazu nake hamma saboda yunwa nake ji matuƙa.
HAU; Hamma (Tana nufin fitar da iska ta hanyar buɗe baki wanda jin yunwa ko bacci ke sa wa)
Yelling - A turance tana nufin ihu.
Misali; Matasan na ihu ne don sun ci ƙwalo.
HAU: Ihu (Tana nufin ƙara ko fitar da sauti da ƙarfi)
Yesterday - A turance tana nufin jiya.
Misali; Jiya ban je makaranta ba saboda babanmu ya aike ni.
HAU; Jiya (Tana nufin ranar da ta gabata kafin yau)
Youghurt - A turance tana nufin kindirmo.
Misali; Ina son shan kindirmo da safe.
HAU; Kindirmo (Tana nufin Nonon da ya kwana ya yi kauri)
Young cow who has not yet given birth - A turance tana nufin karsana.
Misali; Naman karsana yana da taushi da sauƙin dahuwa.
HAU; Karsana (Tana nufin matashiyar saniya wadda ba ta taɓa haihuwa ba)
Yuli - Wata ne na bakwai a shekara.
Misali; A watan Yuli zai cika shekara biyar da gama makaranta.
ENG; July (A turance yana nufin wata na bakwai a shekara)