Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Soak - A turance tana nufin jiƙa.
Misali; Ta jiƙa shinkafar tun safe saboda za ta yi wainar shinkafa.
HAU; Jiƙa (Tana nufin saka abu a cikin ruwa)
Society - Ƙungiya, Majalisa, Kadaura
Society for Gynecology & Obstetrics of Nigeria (SOGON) - Ƙungiyar Likitocin Matuci da Naƙuda Ta Najeriya
Society of Construction Industry Arbitrators of Nigeria (SCIARB) - Ƙungiyar Masu Daidaita Ayyukan Kwangilar Kamfanoni
Society of Nigerian Artists (SNA) - Ƙungiyar Mazana-Hoto Ta Najeriya
Socio-Economic Rights & Accountability Project (SERAP) - Gidauniyar Kyautata Tattalin Arziki da Zumunta
Son - A turance tana nufin ɗa.
Misali; Audu ɗa ne ga Malam Habu.
HAU; Ɗa (Tana nufin matsayin yaro namiji a gurin iyayensa)
South - A turance tana nufin kudu.
Misali; Gabas ake kallo idan za a yi salla ba kudu ba.
HAU; Kudu (Tana nufin wani ɓangare daga cikin ɓangarori)
Speech - A turance tana nufin jawabi.
Misali; A halin yanzu mai girma gwamna ne yake jawabi a ɗakin taron.
HAU; Jawabi (Tana nufin bayani a kan wani maudu'i)
Speech - A turance tana nufin batu.
Misali; A taron an tattauna batu mai amfani.
HAU; Batu (Tana nufin zantuka ko maganganu)