Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Skink Lizard - A turance tana nufin kulɓa.
Misali; Na ga kulɓa a filin da muke wasa a makaranta.
HAU; Kulɓa (Tana nufin dabba mai kama da ƙadangare amma jikinta yana da santsi kuma tana da launuka daban-daban, tana rayuwa a cikin ciyayi)
Slave - A turance tana nufin bawa
Misali; Ya siyo bawa kuma yana ta azabtar da shi.
HAU; Bawa (Tana nufin Hadimi, ko mai yin hidima ga wani. Wanda kuma galibi siyansa ake yi)
Sleep - A turance tana nufin barci.
Misali; Da na je gidan na tarar yana barci, sai na koma.
HAU; Barci (Tana nufin rufe ido don hutawa ba tare da sanin abinda yake faruwa ba)
Slovenly Person - A turance tana nufin kucaki.
Misali; Wani kucaki ne a bakin kasuwa yake siyar da gwangwanaye.
HAU; Kucaki (Tana nufin mutum mara tsafta)
Slowness in Eating - A turance tana nufin janjani.
Misali; Abdulhakim ya fiya janjani.
HAU; Janjani (Tana nufin ɗaukan lokaci wajen cin abinci, wato ci a hankali a hankali)
Small & Medium Enterprises Development Agency of Nigeria (SMEDAN) - Hukumar Bunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Masana'antu Ta Najeriya
Small Ant - A turance tana nufin kiyashi.
Misali; Kiyashi ya lulluɓe naman da na ɓoye a cikin ƙwarya.
HAU; Kiyashi (Tana nufin ɗan ƙaramin ƙwaro mara cizo)
Small black biting ant - A turance tana nufin cinnaka.
Misali; Idan cinnaka ya ciji mutum gurin har ɗan kumbura yake.
HAU; Cinnaka (Tana nufin ɗan ƙaramin baƙin ƙwaro, yana cizo mai zafi)
Small bowl-shaped drum which is hung from the neck and beaten with small flexible sticks - A turance tana nufin kuntukuru.
Misali; Na jiyo sautin kuntukuru, da alama an fara wasan.
HAU; Kuntukuru (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa)
Small Bridge - A turance tana nufin kadarko.
Misali; A hanyar gidan maigari akwai kadarko.
HAU; Kadarko (Tana nufin ƙaramar gada da ake yi da katako musamman don kwararar ruwa)