Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ɓulɓul - Tana nufin ƙiba sosai. Misali; Jamila ta yi ɓulɓul tunda ta dawo daga Ikko. ENG; Excessive Fat (A turance tana nufin ɓulɓul)
Ɓuntu - Tana nufin kwanson da shinkafa ke ciki. Misali; Shinkafar da muka siyo cike take da ɓuntu, sai an gyara ta ƙwarai. ENG; Husks of Rice (A turance tana nufin ɓuntu)
Ɓuruntu - Tana nufin ɓare-ɓare da hayaniya. Misali; Ɓera yana ta ɓuruntu a ɗakin Kaka. ENG; Looting in a noisy manner (A turance tana nufin ɓuruntu)
Ɗa - Tana nufin matsayin yaro namiji a gurin iyayensa. Misali; Audu ɗa ne ga Malam Habu. ENG; Son (A turance tana nufin ɗa)
Ɗabi’a - Tana nufin hali. Misali: Yaran gidan suna da kyakkyawar ɗabi'a. ENG; Behaviour (A turance tana nufin ɗabi'a)
Ɗaci - Tana nufin wani yanayi mara daɗi da ake ji a maƙogwaro idan an ɗanɗana abubuwa kamar magani da sauransu. Misali; Maganin yana da ɗaci sosai. ENG; Bitterness (A turance tana nufin ɗaci)
Ɗaukaci - Dukkani, Gabadaya, Kafatani
Ɗauraye - Tana nufin sa ruwa a sake wanke abu. Misali; Na ɗauraye kwanon kafin in zuba abinci. ENG; Rinse (A turance tana nufin ɗauraye)
Ɗawafi - Tana nufin zagaye Ka'aba da zimmar ibada. Misali; Duk wanda ya je Umara sai ya yi ɗawafi. ENG; Circle the Ka'aba at Macca (A turance tana nufin ɗawafi)
Ɗazu - Tana nufin lokacin da be daɗe da wucewa ba. Misali; Ɗazu na dawo daga gidan bikin. ENG; A moment ago (A turance tana nufin ɗazu) Kishiyarsa; Yanzu
1 226 227 228 229