Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ɓarza - Tana nufin niƙa tishi ɗaya ko biyu, ma'ana ba mai laushi ba. Misali; Na kai wa Inna ɓarza, za ta yi dambu da yamma. ENG; Grind Coarsely (A turance tana nufin ɓarza)
Ɓata - Tana nufin a nemi abu a rasa. Misali; Ina tunanin takalmin ya ɓata, don na duba ko ina ban ganshi ba. ENG; Lost (A turance tana nufin ɓata)
Ɓauna - Tana nufin wata dabbar daji mai kama da saniya. Misali; A gidan ajiyar namun daji akwai ɓauna da sauran manyan dabbobi. ENG; Bush-cow (A turance tana nufin ɓauna)
Ɓaɓatu - Tana nufin magana ba ƙaƙƙautawa. Misali; Mun baro su suna ta ɓaɓatu a ɗakin taron. ENG; Noisy (A turance tana nufin ɓaɓatu)
Ɓaɓe - Tana nufin samun saɓanin da zai kai ga kowa ya kama gabansa. Misali; Talle ya ɓaɓe da budurwarsa jiya. ENG; Break Off relationship (A turance tana nufin ɓaɓe)
Ɓaɓɓake - Tana nufin jijjige abu daga tushensa. Misali; Ya ɓaɓɓake bishiyar daga ƙofar gidansa. ENG; Uproot (A turance tana nufin ɓaɓɓake)
Ɓingire - Tana nufin kwanciya ba tare da tsammani ba.  Misali; Ta ɓingire da bacci ana karatu. ENG; Topple Over (A turance tana nufin ɓingire)
Ɓoye - Tana nufin a ɗauke abu a kai shi inda ba za a ganshi ba. Misali; Yaran sun ɓoye kayan wasan su, mun nema mun rasa. ENG; Hide (A turance tana nufin ɓoye)
Ɓulele - Tana nufin mai ƙiba. Misali; Sabon ɗalibin da aka kawo mana ɓulele ne. ENG; Fat (A turance tana nufin ɓulele)
Ɓullo - Tana nufin fitowa. Misali; Rana ta ɓullo da wuri yau. ENG; Appear Suddenly (A turance tana nufin ɓullo)
1 225 226 227 228 229