Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Woman’s Shawl - A turance tana nufin gyale.
Misali; Kande ta yafa sabon gyale.
HAU; Gyale (Tana nufin mayafi ko abin rufe jiki na mata)
Woman’s Underskirt - A turance tana nufin fatari.
Misali; Ta shanya fatari a igiya bayan ta wanke.
HAU; Fatari (Tana nufin siket ɗin da mata suke sa wa a ƙasan kaya)
Women Trafficking & Child Labour Eradication Foundation (WOTCLEF) - Kadaurar Daƙile Safarar Mata da Bautar da Yara
World Association of Newspapers (WAN) - Kadaurar Kamfanonin Jarida Ta Duniya
World Bank - Bankin Duniya
World Boxing Association (WBA) - Ƙungiyar 'Yandambe Ta Duniya
World Boxing Council (WBC) - Hukumar Wasan Dambe Ta Duniya
World Boxing Organization (WBO) - Kadaurar 'Ƴandambe Ta Duniya
World Health Organization (WHO) - Hukumar Lafiya Ta Duniya
World Medical Association (WMA) - Ƙungiyar Likitoci Ta Duniya