Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Wake up - A turance tana nufin Farka.
Misali; Jaririn ya farka tun ɗazu.
HAU; Farka (Tana nufin tashi daga bacci)
Wall - A turance tana nufin garu.
Misali; Ƙadangare yana yawo a juikin garu.
HAU; Garu (Tana nufin bango)
Warning - A turance yana nufin gargaɗi.
Misali; Shugaban ɗalibai ya yi wa ɗalibai gargaɗi akan zuwa makaranta a makare.
HAU; Gargaɗi (Tana nufin jan kunne ko yin hani)
Water from leaky roof - A turance tana nufin bi-bango.
Misali; Ɗakin ruwa yana bi-bango musamman idan ana ruwa da yawa.
HAU; Bi-bango (Tana nufin ruwa ya dinga biyo bango daga rufin kwano)
Wealth - A turance tana nufin daula.
Misali; Lami tana cikin daula saboda mijinta yana da kuɗi.
HAU; Daula (Tana nufin dukiya ko kayan alatu da ƙawa na duniya)
Wealthy person - A turance yana nufin mutum mai dukiya.
Misali; Maƙocinmu attajiri ne.
Kishiyarta; Talaka
HAU; Attajiri (Mutum mai tarin dukiya)
Wednesday - A turance tana nufin rana ta uku a mako.
Misali; Ranar Laraba za a fara jarabawar.
HAU;Laraba (Rana ce ta uku a cikin ranakun mako)
West Afirican College of Surgeons (WACS) - Kwalejin Likitocin Fiɗa Ta Yammacin Afirka
West African College of Physicians (WACP) - Kwalejin Likitocin Afirka Ta Yamma
West African Examination Council (WAEC) - Hukumar Jarabawar Afirka Ta Yamma