Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Balarabe - Balarabe mutum ne wanda yarenshi larabci ne,larabawa maza sunfi amfani da farar jallabiya matansu kuma bakaken abaya ko kuma alkyabba. Jam'i : Larabawa
Bambanci - Tana nufin kasancewa ba iri ɗaya ba. Misali; A tsakanin maza da mata akwai bambanci, a ɗabi'a da halitta sun sha bamban. ENG; Difference (A turance tana nufin bambanci)
Bambarakwai - Tana nufin abu ya kasance ba yanda ya kamata ba. Misali; Abin ya zama bambarakwai namiji da suna Hajara. ENG; Strange (A turance yana nufin bambarakwai)
Bammi - Abin sha ne mai gusar da hankali. Misali; Bammi yake sha shi yasa kullum ba ya cikin hayyacinsa. ENG; Palm wine (A turance tana nufin bammi)
Bana - Tana nufin shekarar da ake ciki. Misali; Bana damina ta yi harshe, ma'ana an yi ruwa sosai. ENG; This year (A turance tana nufin bana)
Banana - A turance tana nufin ayaba. Misali; Biri yana son ayaba sosai. HAU; Ayaba (Ɗaya ce daga cikin kayan marmari)
Banasare - Tana nufin mai bin addinin kiristanci. Misali; Wani banasare ya tare a yankin nan. ENG; Christian (A turance tana nufin banasare)
Bandage - A turance tana nufin bandeji. Misali; An naɗe ciwon da bandeji saboda kar ƙudaje su hau. HAU; Bandeji (Tana nufin farin ƙyalle da ake naɗe ciwo da shi)
Bandeji - Tana nufin farin ƙyalle da ake naɗe ciwo da shi. Misali; An naɗe ciwon da bandeji saboda kar ƙudaje su hau. ENG; Bandage (A turance tana nufin bandeji)
Bangaje - Tana nufin turewa da ƙarfi. Misali; Musa ya bangaje abokinsa. ENG; Push rudely (A turance tana nufin bangaje)
1 15 16 17 18 19 127