Ƙaiƙayin Matsematsi (Jock itch)

0
25

A likitace ana kira wannan matsala da TINEA CRURIS, wanda kwayar cutar da ake fungi ke haddasa ta kuma kwayar cutar ita ke haddasa makero da cin ruwa na yatsun kafa. Babu alaka ta kusa tskanin wannan matsala da ciwon basir kamar yadda wasu ke tunani.

Wannan Cuta Ana Iya Dauka Daga Mai Ita Ta Hanyoyi Kamar Haka:
  •  Mu’amalar aure da mai dauke da ita
  •  Amfani da tawul daya da mai ita
  •  Sa kayan mai dauke da ita kamar underwears

Yanayin wannan matsala na zuwa da kaikayi da canjin fatar wurin, idan ya bushe aka sosa ya kanyi farin gari.

  Ga Masu Wannan Cuta:
  •  Akwai magani na shafawa wanda idan an tambatar shine a asibiti ake rubutawa mutum
  •  A daina barin matsematsi da danshi bayan wanka ko ziffa, domin kwayar wannan cuta na son danshi shi yasa mutane da yawa kan iya kara samun matsalar bayan sun warke.
  •  A kiyayi hadawa ko aron kaya daga mai dauke da wannan matsala.

Domin karanta Physiology da Hausa Kashi na Shida: Hematology (Jini da Abun da ya Ƙunsa) Danna nan

labarin da ya wuceƊabi’ar Gyaran Jiki A Yau, Shin Ina Hakan Zai Kai Mu
Labarin na GabaRashin Jini A Jiki (ANEMIA)