Ɗabi’ar Gyaran Jiki A Yau, Shin Ina Hakan Zai Kai Mu

0
137

Al’amarin sankarar nono “Breast cancer” nema yake ya zama tamkar wani zazzaɓin cizon sauro na Malaria, matsalar kullum ƙara ƙamari take,abin takaici gwamnati ba abinda take akai, munin matsalar ya wuce duk yada kuke tunani amma inda wacce tasan me matsalar ko wata wacce ta rasa nonuwanta dalilin matsalar za ta fahimta. 

A matsala irin wannan masu maganin gargajiya da Islamic chemist ɗinnan ba wani abu da za su iya yi akai, ba taimakawa suke ba, galibi damfara ce, tunda ba za ka taɓa ganin sun kawo mutum guda da za za su bugi kirji su ce su suka warkar da shi ba, babu kaf, na ga macen da ta kashe sama da Naira Milyan 5 dalilin matsalar nono hannunsu tare da ƙin zuwa asibiti, sai a ƙarshe da ta ga uwar bari. 

Wanda tun farko da za ka ce ki je asibiti a duba ki tunda wuri in ma ƙari ne a cire ko kuma in kansa ce a fara chemo za suce ma ba kuɗi. 

Domin karanta bayani akan Warin Baki (Mouth Odour) Danna nan

Su ko masu waɗancan magungunan kurum cewa za su yi ba da kaza mu ba ki magani ki sha za ki warke tas… suna iya dunƙule cutuka 10 su ba ki magani guda su ce duk zai warkar, toh banda kuma ƙananun ‘ƴan damfara da sun ma fi kowa illa mutum ya zo da magani yana Naira 50 guda uku N100, kullum a haka mutanen mu ke sake da ciwo har sai ya ci ƙarfinsu. Ko yadda ake tallan maganin sanyi, shawara, rana basir ya dace a ce zuwa yanzu wannan cuttukan sun zama tarihi a Nigeria amma ina sai dai kullum ai ta sha domin dama ƙarya ne.

Ku yi haƙuri masu magungunan nan amma dole na faɗi gaskiya, ba kwa fadawa mutane gaskiya, ita kuma gwamnati in dai za ta sami haraji ba ta da damuwa, mutum ya je yai ta tallansa cikin taron mutane.

Galibi sanda mata za su zo asibiti sai cancer ɗin ta tashi daga nono ta ƴaɗu zuwa sauran sassan jiki inda ba abinda za ka iya na hana su tunkarar mutuwa.

Domin sanin menene Cutar Dundumi Ko Ganin Hazo-Hazo Danna nan

Gwamnati ba abinda ya dame ta da wannan gagarumar matsala, illa iyaka surutunsu su kenan batun siyasa, fyaɗe, ƴancin mata, batun auren jinsi da sauran shirme, babu wata hukumar me zaman kanta dake ƙokarin zuba kuɗi ai binkice domin yaƙi da cutar cancer nono cikin mu, hankalinsu ma ba kan nonon yake ba ballantana a fara binkice.

Abu guda ne dai na sani duk waɗannan abubuwan da ake ta magana da ke haddasa kansar nono [risk factors] tabbas kwai wani ɓoyayyen hatsarin da binkice ne kaɗai zai sa a gano shi, domin a yadda larurar ke fantsama akwai wani muhimmin abin da binkice ne kurum zai tabbatar, sai dai ba a ma fara ba kuma babu tunanin yi, wanda yana iya ɗaukar shekaru 10 kafin ya kammala, don haka kowa yai ta kansa, musamman mata, ita ce lamba ɗaya cikin cancer ɗin da ke kashe mana mata a yanzu.

A da wannan larurar ba common ba ce tsakanin mata masu matsakaitan shekaru, wato yan shekaru kasa da 45, galibi sai manya wanda ma suka daina haila amma a yanzu galibin wanda muke samu ko kusa da shekara 50 ma ba su yi ba, Infact har Ƴar 20yrs, 27yrs, 32yrs 33yrs, duk mun same su ballantana kuma ,yan 35 zuwa 40yrs.

Ku san cewa Haihuwa A Gida Ba Jarumta Ba ne Kuskure Ne Danna nan domin sanin dalili

Wata baiwar Allah ‘yar shekaru 27 da ta zo asibiti kwanaki gaba ɗaya tana cuso kai cikin emergency ɗin nan.. ba wanda hankali da zuciyarsa ba su shiga damuwa tare da sanin wani mummunan abu yazo ba…. saboda wani irin mugun wari da gurin ya kaure da shi, tunda ta shigo ba a kara samun iska me daɗi ba.

Ba komai ba ne ke wari sai nononta! In ka kalla sau ɗaya In banda dole ba za kai marmarin ƙara bude ido ka gansa ba, irin yadda yai wani bulli ya yo cunkus, yai ɓamɓaronki, yai rami wani mugunyar ruwa me ɗoyi ke fitowa ta ciki, duk ya jiƙe gaban hijab ɗin, ko zama sak ba ta iyawa saboda azaba…  wayyo Allah kurum take faɗi, ni dai sai da nai kwana na yini ina jin wannan warin a hancina, wai ma sunan nasa face mask kenan.

Wata kwanaki da ta zo Allah likitan da ya kalla a nan ya zube ƙasa ya sami syncope sai daga baya akai Resuscitation ɗinsa, ka rasa irin jahilicin da muke ciki, ai ko ba ni da ko sisi gara ai wacce za ai da na zauna gida da wannan abin a jika. Sai dai ai kwaɓa abubuwa ana ƙara mulkawa jiki. 

To haka muke fama, baza a taho asibiti ba tun farko mutum in ya ji matsala sai yai ta bin gurin masu magungunan gargajiya suna nuna zasu warkar da shi amma a banza sai a ƙarshe matsala ta ci ƙarfin mutum sannan zai doso asibiti, kuma ko ya akai maganar kuɗi mutum ya shiga tashin hankali bayan da tun farko ya zo kafin matsalar ta girma da sai dai ai wani zancen amma ba yadda za ai gwaje-gwajen da kuɗin aikin suke tsadar haka,wata saita ɓata dubunnai gun masu magungunan gargajiya ko Islamic chemist a banza wanda da asibiti tazo ba haka ba.

Domin karanta Yadda Za ka Ba da Agajin Gaggawa Ga Wanda Ya Sha Kananzir (Kerosene) Danna nan 

Ita cancer ta wuce wasa, daga cancer ɗin nono tana iya yaɗuwa zuwa huhu, hanta, ƙwaƙwalwa da dukkan wani sassan jiki, kuma in tai wannan ba wani aiki da za kai wa mutum ta zamo advanced’ sai dai ai ta tafiya a hankali har ranar da ALLAH zai raba ka da mutum (mutuwa), wanda suke samu mu yi aiki a yanke nonuwan a ɗora su kan chemo wannan fa su ne wanda suka cika da imani kenan… don in tai ƙamari ba ma ɓata lokacin cire nonon haka za mu bar sa yai ta zugwanyewa a hankali don aikin cire shi ba zai taimaka da komi ba. 

Shi yasa kwai ban haushi mutum ya share duwawu ya zauna har sai an fara ƙyamatarsa cikin mutane, saboda yana wari sannan ya doshi asibiti yana zaton likita zai masa siddabaru ya warkar da shi lokaci guda.

Wannan shi ne video na links irin yadda cancer kan yi wa nono ku gani da idonku: yadda cancer kan yiwa nono

Don haka bayin Allah musamman kannen mu da yayyen mu mata ku yi karatun ta nutsu.

Wannan kansar ta nono jikinku babban abinda ke taka rawa shi ne sinadarin Iyistrojin (estrogen), shi kuma wannan estrogen dama a jikinku yake, shi ne sinadarin da ya bambanta jikin mace da na namiji, shi ke haɓɓaƙa sha’awar ku, girman nonuwa, haila, ɗaukar ciki zuwa haihuwa… Duk yana cikin aikinsa.

Toh ita wannan cancer muddin ya zamto jikin mace na cigaba da samun exposure da estrogen’ wato ya zamto ya cigaba da fita akai-akai ba tare da jikin mace na samun hutu ko tazara ba wannan shi ne babban hatsarin da ke kai mace ga kansar nono, duk ture wani batu na tarihin ciwon cikin ‘yan uwa, shan taba, da sauransu, wannan exposure ɗin da jikin ke samu da estrogen shi ne muhimmin kuma a kansa ne ya dace hukumomi a duƙufa binkice a nemo yadda za ai.

Jiki Na Samun Exposure Ne Kamar Haka:
  • Fara haila da wuri ga mata, wato duk wacce ta fara haila tana ‘yar tsakanin shekaru 10, 11, 12, 13 zuwa 14 wannan hatsari ne, domin hakan na nuna ta fara samun exposure da estrogen tun tana ƙanƙanuwa kuma haka abin zai zarce tunda duk wata sai tai haila, don haka dogon lokacin da za ta ɗauka tana haila kafin ta cimma shekarun dainawa na da yawa ba kamar na wacce ta fara a 15yrs ba, hakan ke nuna hatsarin kamuwarta da ciwon
  • Rashin haihuwa da jinkirin aure kafin a ɗauki ciki… wannan ma suna exposing jiki ga estrogen, domin kun san idan mace tai ciki to ba ta haila, har sai ta haihu, toh wannan watannin goyon cikin kariya ne ga jikinta, yana hana exposing jikinta ga estrogen, shi yasa yawan haihuwa kariya ne, haka wacce aure yai mata jinkiri jikin zai cigaba da samun exposure tunda duk wata cikin haila take don haka kwai hatsarin ciwon tattare da ita.
  •  Rashin shayarwa, sanda ake shayarwa hakan kan daƙile tasirin hauhawar estrogen a jika, ga matan da ba sa shayarwa ko kuwa ba sa yin cikakkiya yan watanni kaɗan sun yaye yaro saboda wani dalili nasu… To wannan gagarumin hatsari ne da ke kusanta ki ga cancer nono da a yau ta zamo ruwan dare.
  •  Magungunan tazarar haihuwa, wannan magunguna galibi cikinsu a karan kansu dama suna ƙunshe da estrogen don haka gwargwadon jimawa da mace tai a kansu gwargwadon hatsarin ta, duk da ko da na wata 1 ne wata ya isa ya haddasa komi a zubin jikinta, wannan kuwa walau na sha, allura ko implant… Muddin masu ƙunshe da estrogen ne to kwai hatsarin kamuwa da kansa, shi yasa sai an tantance mutum ma ake ɗora shi, yadda in aka ga matsala ana iya canza masa da magani mara estrogen a ba shi iya me progesterone in ma planning ya zama dole.
  • Shaye shayen magungunan mata da ya fantsama cikin al’umma. Wannan magungunan ba za su yi muku abinda suke muku ba inda babu estrogen a ciki, wanda ni a yau shi nafi ɗorawa laifin yawan adadin cancer da muke samu, domin wallahi inda kasan malaria yanzu haka samun mata da cancer nono yake. Wallahi duk masu wani gyaran nonon nan, hips da farji ku kuka da kanku, I’m serious…. Not joking. Kun ga hatta wannan hulba da kuke rainawa da kuke amfani da ita wajen gyaran nono tana da estrogen cikinta sosai, shi ne ma yasa nonuwan ke tashi, in babu estrogen nono bai taɓa girma, duk wannan shirin da ake ma yarinya kafin aure da wanda ke gidan miji estrogen ne ake exposing jikinsu gare shi. Don haka ai hattara
  • Jinkirin tsayawar haila, mace ta haura 50 ko 52 ba tare da ta daina haila ba hakan na nufin jikinta na cigaba da samun exposure da estrogen don haka kwai yiwuwar kamuwa da cutar breast cancer gareta.
Wannan su ne muhimman hanyoyin da matan mu ke samun exposure da estrogen

Musamman al’amarin kayan matan nan yadda da yawa suka rungume sa ba inda zai kawo su ƙarshe sai nan, cancer nono sai ma zuwa gaba. Kome matan mu dambarawa nono suke in dai za su yi girma ko su taso shikenan, amma tunanin ko me zai faru gaba sam ba ruwan su, shin kina jin mazan yanzu kaso 90% cikin 100% za su zauna da ke gaba in kin sami matsala a nono?

Mara lafiya na fama da kanta cancer nono ta ƴaɗu zuwa huhu cikin oxygen amma a haka mijinta ya sake ta saboda ya gaji. Yai cacar kuɗi, nasa sun ƙare ya shiga cin bashi har ya rasa me ba shi,… Babban abinda ya ja hankali na da na ga ‘yan uwanta ba su zarge shi ba, buɗar baki cewa su kai gajiya yai… Ba za mu ga laifinsa ba mun san me ya yi. Karshe dai mutuwa ta yi dama.

Kuma wasu za ka samu na da hawan jini ba su sani ba, wasu kuma sun san suna da shi, amma gani suke ba matsala a irin abubuwan da suke sha…. Toh ku sani shan wannan abubuwan ko shafa su gareki na kusantaki ga hatsarin samun shanyewar ɓarin jiki baya ga cancer, kwai hatsarin hemorrhagic strokes…  Wato fashewar jijiyar jini a cikin ƙwaƙwalwa musamman a basal ganglia ko nucleic.

Haka Ko da ba ki da hawan jini, domin binkice ya tabbatar da hakan. Matan turawa duk ba su san wannan haukan ba ballantana, kuma suna riƙe da mazan su, ballantana kuma ke da kina budurwa ba ki yi aure ba amma kina exposing kanki ga estrogen bayan ko da haila aka bar ki ta isheki hatsari amma sai shaye shayen abubuwa kike don ki ta-da nono.

Domin karanta bayani akan Warin Baki (Mouth Odour) Danna nan

Basal Nucleic wani network ne na jijiyoyin da ke da alhaki wajen sarrafa motsin jikin mu na tafiya, ɗaga hannuwa da duk wani motsi, hakan wajen koyon abubuwa, zartar da abubuwa ko umarnin a yi, sarrafa ɗabi’un mutum da jin tausayi ko damuwa da halin da wani ke ciki, ko jin babu daɗi ko farin ciki in wani abu ya afku.

Toh daga sanda wannan sashin a ƙwaƙwalwa ya sami matsala duk waɗannan ayyukan nasa cikas za su samu, kuna dai ganin yadda masu strokes ke kasancewa; jiki a jirkice, baki a kaikaice, magana ba ta fita, abinci ba ya ciyuwa a daɗin rai da dai sauran ɗawainiya da mai jinya har sai ya gajiya.

Toh ɗaya daga cikin illar shaye-shayen da shafe-shafen waɗannan supplements ɗin kenan da ke haɓɓaƙa shauƙin jima’i ga mata wanda aka fi fahimta da kayan mata, domin ƙarara an sami cases ɗin da hakan ta faru, Infact ita wannan sau ɗaya tak ta sha shikenan ya jawo mata strokes. Domin na faɗa, estrogen shi ne kacokan sinadarin da ke da alhakin haɓɓaƙa wannan abubuwan a mata, kuma shi ne ke cusasu a hatsarin cancer da shanyewar ɓarin jiki.

Batun maganin matsi, tsarki da wani ruwa ko wani turare kuwa…. dama wannan ku kuka da kanku kuna interfering da PH na vagina, kuma kansar bakin mahaifa da farji na nan na ƙwankwasa muku ƙofa a kwana a tashi. Maggots wato tsutsotsi haka za ka gani a farjin mace, amma ku ban hankalinku zuwa cikin wannan links din muga wani abu: Danna nan domin kallan video din 

Bari na taƙaita a nan ba don na kammala faɗin komi ba. Amma dai ya dace kowacce mace tai karatun ta nutsu. Bance kar mace ta lura da kanta ba, amma duk gyaran jiki ba sama da samun isashshen bacci, cin ingantaccen abinci, shan fruits, wanka, wanki, iya mu’amala, sanin buƙatun miji da haƙuri da rayuwa. Wannan za su kai ki dukkan matsayi gurin miji koda an cire miki nonuwa ba zai taɓa dena sonki ba, domin ke ɗin da halayenki yake so. In kunne yaji jiki ya tsira. Na yi nawa saura naku. 

labarin da ya wuceHaihuwa A Gida Ba Jarumta Ba Ne Kuskure Ne
Labarin na GabaƘaiƙayin Matsematsi (Jock itch)