Kamar yadda in aka dafa dankali yake laushi tuɓus ta yadda ko yatsa kasa ka dirza ɓawonsa za ka ga ya saluɓe nan da nan, ko kuma saboda ma tsabar shan wuta za ka ga ya sassaluɓe ya fashe.
Toh ƙwatan-ƙwacin abinda ke faruwa kenan a cikin mahaifar ‘ƴa’ƴa mata wato (uterus) a yayin haila, haka mayanin bangon mahaifarsu ke ɓamɓarowa tare da saluɓowa ya zubo kamar yadda maciji ke saɓa, wanda hakan ke haifar da fitar wannan jinin wanda ake kira jinin haila bayan saluɓowarsa.
Sannan hakan zai sa ku fahimci yadda period ke da tsananin zafi, zugi da ciwo, domin in dankali ya sha wuta ka dauke shi a hannu kai ma ka san me ka taɓa wajen azabar zafi, toh amma haka su mata jikinsu ke karɓar wannan zugin, shi yasa ba banza ba wasu ke murƙususu, wasu ma ba sa iya miƙewa sosai sak su yi tafiya saboda azaba yadda kowa a gidan sai ya san lokacin hailar wance ya yi, domin kowa da yanayin irin yadda jikinsa ke isar masa da saƙon zugi ko zafi.
Zan yi ƙarin haske ne akan zubar jini sosai fiye da kima da kan faru da wasu matan yayin haila.
A ƙa’idance bai kamata a ce yayin haila mace ta fitar da jinin da ya fi cikin sirinjin allura me lambar biyar (5ml syringe) ƙwaya 3 zuwa 4 ba a kullum. Wato 15mls zuwa 20mls. Wannan normal ne.
Toh amma daga lokacin da jini ya zamto yana ƙwaranyowa wato rushing, wani lokacin har da dunƙulallan jini wato clots toh da akwai damuwa.
Domin karanta bayani akan Vaginal Infection shiga nan
Alamomin Heavy Bleeding Yayin Haila
Ga alamomin da ke nuna mace na zubar da jini fiye da kima kuma akwai buƙatar ɗaukar mataki domin babu lafiya:
- In ya zamto duk bayan awa guda sai mace ta canza pad saboda jiƙewa da jini tsawon awoyin yini a jere.
- Ko Pad ɗaya kurum bai wa mace har sai ta haɗe pads biyu gu ɗaya sannan za ta saka saboda yadda jinin ke kwaranyowa.
- Ya zamto har da daddare sai kin tashi kin canza pads saboda jiƙa.
- Jinin ya cigaba da zuba har fiye da sati guda.
- Fitar da jini a duddunƙule manyan gudaji me yawa.
- Jinin yasa ba kya iya sakewa ki ayyukan yau da kullum saboda yadda yake fita.
- Ko yawan kasala, nauyin numfashi ki ji kamar iskar shaƙa na miki kaɗan saboda zubar jini.
Duk macen da ke fuskantar alamomi bakwai ɗin can yayin haila to alama ce da ke nuna tana da HEAVY MENSTRUAL FLOW wanda ke buƙatar a duba a yi wani abu.
Wasu Daga Cikin Dalilan Da Ke Jawo Zubar Jinin Fiye Da Kima Su Ne:
Akwai lokacin da yakan zamto abu me wahala a iya gano dalilin da yasa mace ke zubar da jini sosai, toh amma akwai tarin ababen da binkice ya tabbatar suna jawo hakan.
(1) Rashin daidaiton sinadaran jima’i, girman nono, sha’awa, haila da goyon ciki wato ‘Istirojin da furojestaron”. Wanda a lafiyayyar haila ya dace a ce waɗannan sinadaran sun yi daidai da daidai wato 50/50 wanda hakan ne ke sa a sami lafiyayyen mayanin mahaifa wato lining na uterus da kan kwaɓo yayin haila. Amma in ya zamto babu daidai to musamman a ce “Furojestaron” ya ɗara “Istirojin” wato an sami 70/30 ko 60/40 maimakon 50/50 toh hakan zai sa mayanin shimfidar cikin mahaifar a wannan wata ta yi kauri sosai, wanda kaurin nata shi ke sa sai ta dahu sosai kafin ta kwaɓo ta bi jini ta fito, wanda hakan ke jawo a ga jinin na fita fiye da kima domin da kyar jikin ya ɓamɓaro ta. Hakan kan faru
Daga Cikin Abinda Ke Haddasa Rashin Wancan Daidaiton Shi Ne:
- Mace in ta kasance me jiki ko ƙiba
- Mace me ganin nononta na samar da ruwa duk da ba ta shayarwa koma ƙila budurwa ce
- Mace me ‘PCOS’ wato yawan marurai jikin ƙwayayen haihuwa
- Ciwon maƙoƙo, ciwon sugar, ko kuma idan ya zamto tana haila amma ba ta ovulation musamman ga matan dakan yi haila ba tare da wani ciwon mara ko wata damuwa sosai ba
- Wanda rashin ovulation kansa wani lokacin kwatsam mace sai ta ga jini a tsakiyar wata alhalin ta san ba lokacin haila ba ne.
- Magance yawan zubar jinin a wannan macen ya rataya ga magance matsalar macen bayan an gano, walau ƙiba, pcos
Domin karanta bayani akan Pelvic Inflammatory Disease (PID) Danna nan
(2) Tsiron cikin Mahaifa na fayiburod (Fibroid); wanda kan fito jikin mahaifar mace wanda suke a tsakanin shekarun haihuwa wato shekaru 15 zuwa 50, musamman a matan da suka sami jinkirin haihuwa ko na aure, ko rashin ɗaukar ciki a kai-a kai. Fibroid kansa zubar jini sosai ko jini yake zuwa a tsakiyar wata ya zamto lokacin da mace ba ta tsammanin haila kwatsam sai ta ga jini, ko ya riƙa ɗaukewa yana dawowa, ko haila ta wuce kwanakinta.
Yin scanning a gano matsalar tare da magance shi ko aiki a cire shi na jawo zubar jinin ya daidaita ya daina.
(3) Tsiron cikin mahaifa na Folif (polyp) shi ma tsiro ne dakan yi kamar fibroid sai dai shi bai cika ƙara girma ba, kuma ya fi a matan da suka manyanta suke gab da daina haila, wannan kansa ko bayan daina haila mata suke ganin jini na ɗiga musu lokaci lokaci wato spotting. shi ma magance shi ta hanyar cire shi kansa a rabu da matsalar.
(4) Sai tsiron ƙurarraji a wajen mahaifa wato”Adenomayosis”sakamakon glands ɗin tsokokin mahaifar dakan kumbura su zamo sun yi kurji, wannan na haddasa zubar jini sosai ka ga mace na zubar da jinin haila kamar an yanka wata dabbar, sosai tare da matsanancin ciwon mara, tare da birgima. Zuwa ga likitocin mata (Gynecologist) bayan gano matsalar tare da ɗora ta akan magani shi ne mafita.
Karanta cikakken bayani a kan Malaria In Pregnancy Danna nan
(5) Macen da aka saka mata IUD cikin mahaifa na tazarar iyali, wasu daga side effect ɗin da sukan fuskanta shi ne zubar jini sosai yayin haila koma jinin ya riƙa musu wasa musamman matan da aka sanyawa copper IUD me ƙunshe da estrogen da progesterone.
Don haka magance wannan matsalar shi ne a canzawa mace IUD zuwa ga me progesterone kaɗai zalla banda estrogen, ko kuma a canza mata wata hanyar planning ɗin zuwa implanon, allura, maganin sha ta baki ko wata hanyar daban, ana haka jinin zai daidaita.
(6) Samun juna biyu a ɓangaren mahaifar da bai saba aje ɗa ba, wato maimakon can cikin uterus inda yake da zurfi da faɗi, amma sai ya zamto cikin gashi a cikin mahaifa amma daga farko-farkon bakin mahaifar ana wuce cervix “fulasanta firebiya” wannan kan jawo mace ta ga jini na zuba, shi ne ma wasu kanyi zargin ga mace na da ciki amma tana haila, abinda ba haka ya kamata ya faru ba.
Wannan sai dai a zuba idanu a yi hattara, a hana mace aikin ƙarfi sosai domin cikin na iya samun matsala a ko da yaushe ko ya jawo aikin gaggawa na CS domin a cire cikin.
Karanta Abubuwan Daya Dace A Sani Akan Allurar Artemether
(7) Cutar kansar bakin mahaifa ko cikin mahaifa (cervical cancer) zubar jini sosai musamman bayan duk an yi magunguna amma abu ya cigaba hakan ka iya zama alamun da ke nuna tsokokin bakin mahaifar mace sun fara rikiɗa zuwa kammanin ƙwayoyin kansa, musamman ganin jini ba tsammani ko yake fita sosai. Shi yasa gashinan ake gwajin kyauta don haka zuwa ai wa mace gwajin musamman me auren da ta haura shekara 30, ko wacce ke gab ko ta dena haila, wacce dai aka riga aka saba saduwa da ita, ko wacce take da zargi me ƙarfi akan mijinta manemin mata ne, banda ‘ƴan mata matuƙar mace ba ta taɓa sanin namiji ba, domin kwai masu amsa sunan ‘yan mata amma ko mai aure ba lallai ta kai su sanin daɗin namiji ba irin wannan su ne kan gaba cikin wanda ya dace su je a yi musu cervical cancer screening da za a buɗe a sa spatula a dangwalo majinar bakin mahaifar su a tantance.
(8) Hakazalika matsalar ka iya zamowa a dalilin larurar zubar jini ta gado sakamakon sun gaji ƙarancin sinadaran da ke sanya jini tikkewa da sauran tsai da zubarsa, kamar su hemofiliya ko bonwilbiran, irin wannan larura ce ta gado ba ka iya raba su da ita complete sai dai ana iya ba su magani da zai taƙaita fitarsa don ganin ba a shiga wahala ba.
(9) Hakazalika yana iya kasancewa a dalilin wani magani da mace kan amfani da shi wanda shi ne ke sanya period na mata rushing, kamar maganin tazarar haihuwa na sha wato OCP, ko maganin katsa jini ga masu larurar kumburi ko ciwon zuciya da akan ba su, ko shan magani irin su aspirin, irin waɗannan dakatar da su ko canza musu kalar magani shi ne mafita.
(10) Matan da ke da ciwon ƙoda, ko ciwon hanta ko maƙoƙo wato “thyroid disease” su ma sukan fuskanci wannan matsalar, don haka mai da hankali wajen maganin matsalar shi zai taimaka su rabu da heavy bleeding ɗin.
Don haka kowacce matsala kun ji abin da na faɗa matsayin hanyar magance ta, don haka zuwa ga ƙwararun likitoci medical doctors da kuma gynecologist likitocin mata shi ne zai taimaka a gano tushen matsalar da kuma hanyar da za a bi a magance, kar ki ce ai na je asibiti amma har yau, a a ta yiwu ba babban asibiti kika je kika ga Gyne doctor ba. In ma shi kika gani in babu canji ba laifi bane kije wani asibitin ki ƙara ganin wani gyne ko medical doctor ɗin, ta yiwu a sami bambancin ƙwarewar aiki.
Edita@rumasau-kallamu
Domin karanta bayani akan Noristerat (Norist) Danna nan