Ana yin amfani da coil na sauro a sassa daban-daban na duniya, musamman a yankunan da suke fama da yawan cututtukan da sauro yake yaɗawa kamar zazzaɓin cizon sauro da ciwon Dengue. A Najeriya, inda ake fama da tsananin zafi da kuma yawan sauro, musamman tare da tsadar kayan masarufi, coil na sauro yana daga cikin hanyoyin da aka fi amfani da shi wajen kare kai daga cizon sauro.
Sai dai, akwai abin damuwa game da illolin lafiya da ke tattare da hayaƙin da coil na sauro yake fitarwa. Hakan yasa mutane suke yin tambayoyi a kan ingancin coil ɗin gaba ɗaya. Wannan maƙalar za ta yi bayani ne a kan dalilan da suka sa coil ɗin sauro ya zama sananne, illolin lafiyarsa, ƙalubalen amfani da shi, da kuma hanyoyin magance matsalar a cikin yanayin ƙasashe irin Najeriya.
DALILIN SHAHARAR COIL NA SAURO
Babban dalilin da yasa coil na sauro ke ci gaba da shahara a Najeriya, kamar yadda yake a wasu ƙasashe masu tasowa, shi ne farashin sa da kuma yadda ake samun shi cikin sauƙi. Yawancin iyalai suna fama da ƙalubalen tattalin arziki kuma ba za su iya biyan ƙarin kudi don sayen wasu ingantattun kayan kare kansu daga sauro masu tsada ba, kamar yadda ake samu a wasu ƙasashe.
Haka kuma, yawan dauke wutar lantarki yana sanya yin amfani da kayan lantarki masu korar sauro ya zamo bazai yiwu ba, wanda hakan ke sanya iyalai da yawa su koma yin amfani da coil na sauro. Coil ɗin sauro yana da amfani saboda ba ya buƙatar wuta ko wata na’ura ta musamman kuma yana iya ƙonewa har tsawon sa’o’i, yana samar da kariya daga cizon sauro cikin ƙananan kuɗi.
Amma, ingancinsa yana da alaƙa da yadda ake barin shi yana ƙonewa da kuma yawan hayaƙin da yake fitarwa. A mafi yawan lokuta, dole ne a bar coil ɗin yana ƙonewa duka tsawon daren don tabbatar da kariya mai kyau daga sauro, saboda yawanci sauro sukan dawo da zaran hayaƙin ya gushe. Wannan yana haifar da matsala, kasancewar yana da alaƙa da illolin lafiyar da na ambata.
ILLOLIN LAFIYA DA KE TATTARE DA COIL NA SAURO
Kodayake coil na sauro yana da tasiri wajen korar sauro, hayaƙin da yake fitarwa yana ɗauke da wasu sinadarai waɗanda suke iya yin illa idan aka shaƙe su na tsawon lokaci. Yawanci coil ɗin na fitar da sinadarai irin su “pyrethroids”, wanda shi ne sinadarin kashe ƙwari, da wasu ɓurɓushi masu illa.
Bincike ya nuna cewa daɗewa ana yin amfani da hayaƙin coil na sauro yana iya haifar da matsalolin numfashi, musamman idan an yi amfani da shi a ɗaki maras isasshiyar iska. Wasu binciken kuma sun danganta hayaƙin coil ɗaya da na fiye da sigari 100, wanda ke nuna damuwa game da yiwuwar kamuwa da cututtukan huhu da sauran matsalolin numfashi.
Duk da waɗannan illolin, hukumomin da ke kula da lafiya da na kare haƙƙin masu amfani da kayan masarufi ba su hana yin amfani da coil ɗin sauro gaba ɗaya ba. Wannan yana da alaƙa da cewa, idan an yi amfani da coil ɗin cikin taka-tsan-tsan a wuraren da ake samun iska, to, fa’idarsa ta rage yaɗuwar cututtukan sauro ta fi haɗarin lafiyar da ake ganin zai iya haifarwa.
A yawancin gidaje, kaucewa kamuwa da zazzaɓin cizon sauro ko ciwon Dengue ya fi zama babban abin la’akari fiye da kamuwa da matsalolin numfashi a nan gaba sakamakon yin amfani da coil ɗin.
BUƘATAR SAMAR DA ISKA A CIKIN ƊAKI DA TASIRIN INGANCIN COIL ƊIN
Don rage haɗarin lafiyar da ke tattare da hayaƙin coil na sauro, ana bayar da shawarar a yi amfani da shi a wuraren da ke samun iska mai kyau tana kewayawa. Amma, wannan shawarar tana da ƙalubale, kamar haka: a wurin da iska take kewayawa, yawan hayaƙin coil ɗin zai zamo babu yawa sosai, wanda hakan zai sanya coil ɗin ya kasa korar sauro yadda ya kamata. Don haka iyali suka gwammace su bar hayaƙin coil ɗin ya taru sosai, saboda ya iya korar sauro sosai.
Wannan yana nufin cewa, domin coil ɗin sauro ya yi aiki yadda ya kamata, dole ne a bar shi ya ƙone gaba ɗaya a duk tsawon dare. Idan ba haka ba, to, sauro sukan dawo da zarar hayaƙin ya gushe. Amma kuma hakan zai iya sanya su shaƙi hayakin fiye da yadda ya kamata.
MATSALOLIN TATTALIN ARZIKI DA RASHIN WADATATTUN ZAƁIN HANYOYIN KARE KAI DAGA CIZON SAURO
A Najeriya, tsadar kayan masarufi, yawan ɗauke wutar lantarki, da kuma matsalolin tsadar rayuwa a yawancin gidaje suna haifar da wahalar iya sayen wasu wasu abubuwan korar sauro, waɗanda ba coil ba. Na’urorin lantarki masu korar sauro suna da tsada kuma suna buƙatar wutar lantarki, wanda ba a samu koyaushe. Haka kuma, ragar kwanciya da aka shafawa maganin kashe ƙwari (treated mosquito net) tana da tsada ga yawancin iyalai ko kuma ba a samunta a cikin sauƙi.
A ƙauyuka, wannan matsala ta fi tsanani, inda coil ɗin sauro yake zamowa kawai shi ne mafita mai sauƙi. Amma daɗewa ana yin amfani da coil ɗin a cikin gidaje marasa isasshiyar iska yana ƙara haɗarin samun matsalolin numfashi, musamman ga yara da tsofaffi. Wannan ya sanya ƙwararrun ma’aikatan lafiyar suke nuna damuwa kan illolin daɗewa ana yin amfani da hayaƙin coil ga lafiyar jama’a.
DAIDAITA YIN AMFANI DA COIL NA SAURO DA KUMA KIYAYE LAFIYA
La’akari da matsalolin tattalin arziki da ƙarancin hanyoyin magance matsalar sauro, coil ɗin sauro yana cigaba da zamowa mafi sauƙin mafita ga yawancin iyali a Najeriya. Amma, akwai hanyoyin da za a iya haɗa amfani dashi tare da kiyaye illolinsa. Misali, sanya coil ɗin sauro kusa da tagogi ko wuraren da sauro ke shiga zai iya sanya taruwar hayaƙin a wuraren sauron yake biyowa ya shigo ɗaki, yayin da kuma zai tabbatar da samun iska domin rage shaƙar ɓurɓushin da ke cutarwa.
Bugu da ƙari, iyalai suna iya haɗa yin amfani da coil ɗin tare da wasu hanyoyi masu arha. Misali, amfani da fanka wacce za ta bayar da iska a cikin ɗakin zai ƙara ingancinsa yayin da kuma zai rage yawan hayaƙin da ake shaƙa. Sa’annan sanya ragar sauro a rufe tagogi da ƙofofi zai iya taimakawa wajen rage dogaro akan yin amfani da coil ɗin.
Danna nan don karanta Ko Ka San Idanun Sauro Sun Fi 100?
Edita; Rumasa’u M. kallamu