Yaron Da Ke Ƙin Shan Nono

0
151

Ba ko yaushe ba ne don jariri ko yaro ɗan kasa da shekaru biyu ya ƙi shan nono, ko ya zamto mai saurin sakin nonon da zarar ya fara sha za a ce ba shi lafiya ba, a hau neme-nemen magani ana ɗura masa. 

Na sha faɗa magani guba ne kowanne iri muddin aka sha shi ba tare da tabbatuwar ciwon da ya dace da maganin ba! Har kuwa su Paracetamol, B-complex, ɗin nan da multivitamins da ake rainawa.

Don haka kamar yadda lafiya ƙalau amma saboda wani abu kuke kasa cin abinci shi ma jariri mutum ne haka yake! Kar ku ɗauka don kurum ɗan mitsitsi ne hakan na nuna bai san komai ba, sai kun ɗura masa abinci ko ba ya so. 

Wasu lokutan ku ke hana shi sha; musamman in yaro ba ya kuka, ba ya rikici, ba ya ƙwalla, ba kuma ya zazzaɓi hakan na nuna ƙalau yake wani dalili ne ya hana shi:

* Ƙarancin tsafta daga uwar! Kila hammatarta babu aski, ko kuwa kin yi aiki kin yi zufa kin zo kin ɗora shi a cinya alhalin iska na kaɗo masa tashin matse-matsin hammatarki, ko da ya kama nono tabbas zai saki, domin shi ma yana jin tsamin.

* Rashin tsaftar hannayenki, ƙila jikinki tsaf amma kin taɓo abu mai ƙarni, ko wari a hannunki kuma kin zo yayin sakar masa saleɓar brazier ɗinki kin dunguri kan nonon nan ma yana iya ƙin sha. In kika matsa kuma ya sa kuka.

* Rashin tsaftar rigar nono da kuma rashin wanke ko goge kan nonon sosai bayan yaro ya kammala sha, wasu rigar nonon ce sai ta shafe yini biyu jikinsu, zufa da kuma normal bacteria ɗin kan fatarki na da tasiri musamman in ya zamto dama da kin gama ba da nono kurum jan saleɓar rigar nonon kike yi mayar ba kya tsaftace kan nonon, haka anjima za ki ciro ki ƙara cusa masa a baki, hakan har gudawa yana iya jawoma jaririnki. Don haka sai an kiyaye.

* Canjin sabulun wanka me ƙarfin ƙamshi, wani yana kama fata har a baki a ji shi, don haka wannan ma na hana yaro kama nono, har sai kin koma irin wanda ya saba da shi mara ƙarfi da baya iya jin sa.

* Shafa turare me ƙarfi wanda shi ma bai saba da shi ba, kamar mu ne kai ma akwai turaren da in wani ya sa sai ka ji kamar za ka ce wayyo Allah in ya tsaya kusa da kai, to su ma haka ne, wannan na iya hana su shan nono.

* Juyowar kwanakin haila, shi ma na sa yaro ya ƙauracewa shan nono domin mizanin sinadarin gishiri-gishiri a cikin nono wato sodium & chloride na ƙaruwa, yayin da sinadarin kanwa-kanwa da zaƙi ke yin ƙasa wato potassium & lactose wanda kuma su yaro ya fi so. Kun ga ko a manya in gishiri yai yawa a abinci wani ba ya iya ci. 

* Haka nan yayin HAILA ko da canjin ɗanɗanon nono bai canza ba akan samu adadin ruwan nono ya ɗan yi ƙasa hakan ma iya sa jariri in ya ji ba ya isarsa yai zuciya ya dena wahalar da bakinsa saboda gajiyar tsotso alhalin babu wadataccen ruwa.

* Haka nan ma samuwar juna biyu alhalin ga wani ana shayarwa shi ma na iya sa irin wancan canjin da ake fuskanta yayin haila, wanda hakan na iya sa yaro ya yaye kansa.

* Haka nan wani magani da ke uwar ke sha walau na Hausa ko na asibiti, galibi na asibiti shi yasa likita ke tambaya ko kina da ciki ko shayarwa kafin a rubuta miki magani, idan kikai masa ƙarya alhalin kina shayarwa irin abunda zai iya faruwa kenan, yaronki ya ƙi nono kuma ki zo nonon yai ta ciwo. Haka cin irinsu tafarnuwa ko wani nau’in abinci da a da ba kya ci wanda suna iya ratsa ruwan nono.

* Ko yawan dauke hankalin yaro wato distracting, don wani yaron ko ya ya ji magana ko motsi sai ya waiga, shi yasa za ka ga suna shan nono suna saki. Irin wannan maganinsu kike shiga inda yake tsit babu hayaniya sai ku yi shayarwarku a nutse, ko a tsohe kunnuwan da wani abu kamar auduga kafin a gama in ba haka ba ko ya ya ji motsi ba fasa juya zai ba.

Waɗannan su ne wasu daga mahimman ababen da ke sa yaro ƙauracewa nono. Don haka kiyayewa kurum suke buƙata babu buƙatar zuwa ki yi ta cusawa yaro magani, ki lura da kyau, sai dai in akwai alamun rashin lafiya toh sai a taho ga likita.

* Sannan kar ki manta duk sanda kika gama bai wa yaro nono kike dora shi a kafaɗa kina shafa bayansa har sai kin ji ya yi gyatsa. Hakan alama ce ta ya ƙoshi, in bai gyatsa ba a kuma maida shi kan nono.

* Ganin jariri na yawan ƙwalla ko hawaye ko da ba ya kuka haka alama ce ta nono ba ya isarsa, ko da kuwa ana ba shi ƙila ruwan nono babu sinadaran da za su ƙosar da shi, sai a nemo madara wacce take ta yara irin NAN ɗinnan a ƙara masa da ita.

*Ganin jariri ko yaro na yawan tsilla fitsari hakan alama ce ta yana samun kyakkyawan shayarwa.

Fatan an ilmantu. Burina na ga al’umarmu mun yi lafiya, rayuwarmu ta canza, birni da ƙauye ana samun lafiyayyun yara masu tasowa.

Don karanta jerin abincin da ke ƙarawa mata masu shayarwa ruwan nono danna nan

Edita; Rumasa’u M. kallamu

      

labarin da ya wuceWaye Bahaushe?
Labarin na GabaFassarar Huɗuba Daga Masallaci Mai Alfarma 10 Rajab 1446 AH 10 January 2025