Depression dai wani yanayi ne marar daɗi da mutum ke tsintar kanshi bayan wani abu marar kyau ya faru da shi, ko kuma haka kawai mutum ya tsinci kanshi cikin wani yanayi na rashin jin daɗin komai kuma ba ya sha’awar komai da kowa, wanda zai sa mutum ya riƙa tunanin ina ma ya mutu ya huta. Wani lokacin kuma mutum ya kasa bacci, aiki, cin abinci, kula da iyali, kula da jiki da sauran su.
Depression shi ne a kan gaba wajen saka mutane su hallaka kansu da kansu, ko ta hanyar rataya ko shan guba ko cakawa kai wuƙa ko faɗawa ruwa.
Wannan depression ɗin yana ɗaya daga cikin manyan matsalolin ƙwaƙwalwa ko in ce “PSYCHIATRIC EMERGENCY”.
A duniya baki ɗaya a ƙalla mutum (miliyan 264) ke fama da depression kuma daga cikin su kashi 87% cikin ɗari mata ne ‘yan shekara 15 zuwa shekara 40. Ya danganta daga tsawon lokacin da mutum ke yi yayin da yake cikin damuwar kamar SHORT TIME (kwana ɗaya zuwa kwana uku) ko kuma LONG TIME (kwana 3 zuwa sati biyu har abin da ya fi haka)
DEPRESSION YA KASU KASHI KASHI KANSHI, AKWAI:
1. Endogenous_depression: Wato mutum zai tsinci kanshi cikin yanayi marar daɗi ba tare da dalilin komai ba, wannan ya samo asali ne daga:
✍Gado daga uwa (mafiyawa)
✍Rashin lafiyar ƙwaƙwalwa ko taɓuwar ƙwaƙwalwa
✍Rashin isasshen bacci
✍Wata rashin lafiya da ke damun hormones da sauran jiki
2. Exogenous_depression ko kuma REACTIVE DEPRESSION: Wato idan wani abu ya faru da mutum na yau da kullum kamar:
✍Mutuwar miji ko mata/uba ko uwa
✍Sakin aure/ ƙara aure/kishiya
✍Rasa aiki/kora daga aiki
✍Wani bala’i na rayuwa
✍Faɗa ko rashin jituwa tsakanin ‘yan uwa, miji, mata, iyaye, dangin miji, dangin uwa ko uba da sauran su
✍Faɗuwa jarrabawa
✍Asarar dukiya ko faɗuwa takarar siyasa
✍Kamuwa da ciwo kamar HIV ko diabetes
✍Fyaɗe
✍Bayan haihuwa (peupherial blues)
Waɗannan su ne kashe-kashen depression da muke da su. Amma wani lokacin ba koyaushe depression ɗin ke kasancewa ga mutum ba, yakan iya zowa mutum kamar haka:
Biopolar: Da safe kana cikin damuwa amma da maraice ka kasance cikin farin ciki kamar ba kai ba.
Unipolar: Ko ka kasance cikin baƙin ciki koyaushe ko kuma ka kasance kana cikin baƙin ciki amma komai kana iya yi ba ka gajiya.
ALAMOMIN DEPRESSION
Alamomin shi suna zuwa ta fuska biyu Wato, yanda mai depression ɗin ke ji a jikin shi:
- Tsananin baƙin ciki da damuwa,
- Mummunan tunani,
- Tunanin mutuwa,
- Mutum ya ji ba shi da amfani
- Tunanin ba mai sonka
- Jin haushin kowa da komai
Don karanta Amfanin Aya Wajen Samar Lafiya A Jiki danna nan
Alamar da mutane za su gane cewa wannan mutum yana cikin depression
- Ramewa
- Gumi (zufa)
- Turowar idanuwa
- Rashin bacci
- Rashin cin abinci
- Bugawar zuciya da ƙarfi
- Hawan jini
- Kaɗaita cikin ɗaki ko gida
- Rashin son magana da kowa
- Fushi
- Rashin kula da kai kamar wanka
- Kuka dare da rana
MATAKIN DA YA KAMATA A ƊAUKA IDAN AN GA MUTUM CIKIN YANAYIN DEPRESSION /MATAKIN DA YAKAMATA KA ƊAUKAR WA KANKA
1- Psychological care: Babban abu na farko da mai depression ke buƙata shi ne shawarwari masu kyau a kan yanayin da ya tsinci kanshi.
- Kada ka danmu da kanka a kan abin da dole sai ya faru ga ɗan Adam kamar:
-Mutuwa, mutuwar ɗan uwa da sauran su
-Kishiya ko sakin aure
-Kora ko rasa aiki
-Asarar dukiya da sauran su
Mutane da dama kullum sai sun fuskanci wannan matsalar kuma ba za a daina ba har duniyar ta ƙare, to don haka kada ki damu kanki a kan abin da ba za ki iya canjawa ba idan ya faru. Idan ke kaɗai ce ga mijin ki yace zai ƙara aure kada ki damu, 4 Allah yace ya yi kin ga ko yanzu akwai 2 zuwa. To meye na damun kai?
Ya sani cewa rayuwar duniya ba komai kake so za ka samu ba, ko kuma ko me ka samu mai yiwuwa ne ya kuɓuce ma musamman idan ba rabon ki ba ne kuma idan mutuwa ce, to tabbas dole ce a kan kowa.
Ki nemi amintacciyar ƙawa ki gaya mata matsalolin ki kada ki bar damuwa a cikin zuciyar ki, idan ba ki da ita, ki nemi ‘yan uwa ko wani wanda kika fi jin sanyi a wurin shi koda addu’a aka yi miki za ki ji sanyi sosai. Idan kuma babu, ki nemi ƙwararru a wannan ɓangaren wato GUIDANCE AND COUNCELING SERVICES insha Allah za a dace.
- Yan uwa kuma ku saka mai damuwa a jiki kada ku bar shi ya kai ga hallaka kanshi ko ya kai shi ga wani ciwo daban
- Kada mutum ya zauna shi kaɗai, ya riƙa shiga mutane da abokai ana hira, idan ma babu hali, ki/ka nemi masu irin matsalar ka ku zauna tare ku riƙa samun nishaɗi.
2- Rehabilitation and care:
- Idan aiki ne mutum ya rasa ko wani abu, ya nemi wani abun wanda ko bai kai ga wancan ba ya yi haƙuri da shi, rayuwar duniya ta ɗan lokaci ce, ba dole ne sai an sami abin da ake so ba 100%
- ‘Yan uwa da abokai, ku kula da mai depression iya gwargwado kada ku watsar da mutum, sannna ku tabbata babu wuƙa ko kwalba ko wani mummunan abu kusa da shi ko ɗakin shi wanda aka san zai iya hallaka kanshi da shi. Ku sani, ba yin kanshi ba ne duk abin da ya yi.
3- Spiritual care: Dukkan mu musulmi mun yadda da Allah kuma mun yarda da ƙaddara, a nunawa mutum cewa komai ya gani daga Allah ne, kuma jarrabawa ce, mai yuwa ne ta yi masa sanadin shiga aljanna.
4- Diversion: Ka yi wa kanka maganin depression da abin da ka san ya fi faranta maka rayuwa kamar rawa da waƙa, sauraren music ko ƙuran, karatun littafan na nishaɗi ko soyayya, kallon films ko drama ko games da sauran su. Duniyar mai ƙarewa ce, don haka NO NEED TO WORRY ABOUT ANYTHING. An haife ka ba ka da komai, kuma ba za ka koma da komai ba, to meye don ka rasa wani abun?
5- Drugs: Idan abun ya gagara, ana bai wa mutum magungunan da ke sa bacci, tabbas suna rage depression kuma suna sa mutum bacci, amma kada mutum ya dogara da magani, ya yi ƙoƙari ya fahimci rayuwar duniya kuma ya yi ƙoƙarin ƙauracewa wannna abin da ke sa shi damuwa, saboda maganin zai iya zame ma mutum addiction ko maganin ya daina aiki.
Abu na ƙarshe: Ba kowacce damuwa ce depression ba, rayuwa dama an yi ta da farin ciki da baƙin ciki, don haka mu lura, damuwa idan an ɓata ma rai ko ka yi asarar abu ta ɗan lokaci ba matsala ba ce, matsala ita ce idan waɗancan alamomin da na lissafa sun faru da mutum.
Domin karanta Cutar Damuwa danna nan
Edita:@rumasau-kallamu