Kafin ki kai ga ɗaukar ciki (juna biyu) da wata guda ko bayan ta tabbata ciki ya shiga lallai a watanni ukun farkon nan na cikin ki tabbatar kin samo sinadarin (FOLIC ACID 5MG) kin riƙa sha tun wata ɗaya ma kafin ki ɗauki cikin, domin kaucewa zance da karkata-kai ko kuwa arba da abinda zai sanya damuwa tare fantsamar labarai tsakanin mutane na abin haihuwarki.
Domin yana daga cikin illolin ƙarancin folik asid haihuwar yara masu nakasa ko kuwa wasu irin munanan suffofin halitta da babu wanda zai so a sha wahalar goyon ciki karshe a haifo yaro ko yarinya wanda wani ma bazai iya ƙara kallonsa ba in ya kalle shi sau ɗaya.
- Akan haifo yara su zo da ƙaton ƙari ko tabo a gadon baya. ko yankakken leɓe ko datsatstsen dasashi (Encephalocele, spina bifida, cleft lips or cleft palates)
- Wani ka gan shi da ƙaramin ƙoƙon kai, ko mitsi-mitsin kunnuwa. (microcephalic with low set ears)
- Wani a haifo shi da ƙaton kai, wani da fuska kamar aljani (hydrocephalus abd dysmorphic facie)
- Ko jaririn da bai da dubura ko wajen fitsari. ko me yatsu shida zuwa bakwai da naniƙaƙƙen hanci.
- Wani a haifo shi da ƙatoton ƙari a ƙeyarsa, cikinsa, goshinsa, ƙirjinsa ko gadon bayansa. (teratoma, myelomeningocele)
- Wani ya zo kayan cikinsa a fili a bude, kamar yadda ‘yan kwanakin nan ga su nan muna ta gani, wanda galibi ko an zo asibiti ƙarshe macewa suke. (Gastroschisis, Omphalocele).
- Ko ‘ƴan gujil-gujil ɗin gaɓoɓi da dogon ƙoƙon kai.
- Ko yaran da kan zama wasu gaulaye, ko masu karkataccen wuya, rashin daukar karatu, kurumta, da sauransu.
Da dai sauran tarin matsaloli, wanda galibi ƙarancin ko rashin shan sinadarin folic acid ne ya zamo sila.
Domin karanta dalilin Rashin Jini A Jiki (ANEMIA) Danna nan
Wasu lokutan a asibiti akan ba mata su kyauta, amma rashin sanin amfaninsu yasa sai su je su yi watsi da su.
Shi wannan sinadarin yana da amfani ne a watanni uku na farkon ciki kacal domin a lokacin ake haɗa halittar jariri, sannan lokacin ne duk waɗancan illolin kan faru wanda da zarar ciki ya wuce watanni uku to shansu bai da wani amfani domin lokacin halitta ta kammala in yaro ya sami matsala ya riga ya samu kurum, in bai samu ba nan ma bai samu ba.
Sanin hakan yasa musamman masu shiga gidan aure a karon farko wato ‘yan matan da aka tsai da ranar biki, da ma bazawarar da za tai kome ko wani auren…in dai akwai haihuwa a plan ɗinsu toh tun wata ɗaya kafin ɗaurin auren ya dace mace ta fara shan; FOLIC ACID Me 5MG kullum ƙwaya ɗaya. Insha Allahu da wuya ka ga an kai ga haifo jariri me nakasa. Baki ɗaya ina jin banda abu da yai tsada na Naira ɗari biyu “N200” a da in mace ta sayo sai ta shekara tana sha bai ƙare ba, ko yanzu na tabbata Folic Acid na “Naira 300” ya ishi mace ta yi fiye da wata uku ma tana sha, ba wani magani bane me tsada.
Domin karanta bayani akan Warin Baki (Mouth Odour) Danna nan
Shan sa zai taimaka tare da kaucewa zuwa ai ta camfe-camfen banza, ana bin ‘yan tsubbu da bokaye neman lafiya, ko a riƙa mayu ne suka jefi cikinki, ko a haɗaki gaba da wata a ce ita ta yi miki asiri, ko a riƙa kin haifo ɗan ruwa saboda kin riƙa debo ruwa da daddare a borehole ko rijiya da dai sauransu…. Alhalin munanan suffofi ne da ko mayu ba su isa su iya ƙirƙirarsu a mutum ba.
Sannan haka yaro tun yana jariri iyaye su yi ta faman zaryar asibiti ana cacar kudi, kuma su kansu ƙunshe yaron za ka ga suna yi saboda damuwa…ba ma sa so a gan shi, ballantana kuma gaba in ya tasa, haka yara babu me son ya gan shi cikin abokan wasan sa, ko a mai da yaro matoni.
Shi yasa a ko da yaushe ilimi abu ne me daɗi musamman kuma a ce in ka yaɗa shi cikin al’ummar da kake da ƙwarin guiwar za su yi aiki da shi.
Kusan da cewa Haihuwa A Gida Ba Jarumta Bane Kuskure Ne Danna nan domin karanta dalilai
Ku nemi wannan magani ga masu shirin amarcewa kusa, ko wacce take da sabon cikin da bai wata uku ba, wacce ko ta san ta taɓa haifo yaro me nakasa toh shekara guda ma ya dace ta yi tana sha har zuwa ta sami wani cikin tai watanni ukun farko.
Idan ciki ya wuce wata 3 shansa bai da wani amfani, already halittar sassan jiki ta kammala ba abinda zai canza.