Sallar nafila ce raka’a huɗu, a kowacce raka’a ana yin tasbihi saba’in da biyar (75). Yadda ake yin ta shi ne:
“Bayan kabbarar harama sai a karanta Fatiha da sura, kafin ruku’u sai a faɗi “Subhanallahi walhamuduillahi, wala’ilaha illallahu wallahu Akbar” sau goma sha biyar(15) . Sai a yi ruku’u a cikin ruku’un a yi wannan tasbihi sau goma. In aka ɗago kafin a yi sujjada sai a sake yin ƙafa goma, a yi sujjada ƙafa goma, in an ɗago daga sujjada ƙafa goma, a ɗaya sujjadar ƙafa goma. in ka ɗago kafin a miƙe sai a yi ƙafa goma raka’a ɗaya ke nan, haka za a yi a sauran raka’o’in.
Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Sallar Tasbihi danna nan.
Wannan bayani anciro shine daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.