Yadda Ake Samosa A Sauƙaƙe

0
6693

Barkan mu da  kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, za mu koyi yadda ake ake samosa tare da ni Hafsat Shettima.

Abubuwan haɗawa:
  1. Flour kofi 3
  2. Gishiri pinch
  3. Corn flour chokali 3
  4. Ruwa
  5. Nama (niƙaƙƙen nama) ½ kg
  6. Attaruhu manya 5 (jajjagaggiya)
  7. Albasa matsaƙaita 2 (a yanka ƙanana)
  8. Carrot (Karas babba 1) a yanka kanana
  9. Tafarnuwa
  10. Curry da thyme
  11. Kayan ɗanɗano (dunƙule 3-4)
Yadda ake haɗawa
  1. Farko za ki samu bowl ki zuba fulawa da corn flour da ɗan gishiri, sai ki kwaɓa shi kamar yadda ake yin dough ɗin meat pie, za ki buga shi sosai har fulawar ta saki jikinta.
  2. Sai ki yi rolling ɗinta da faɗi kamar circle, ki shafa mai a kan ɗaya sai ki barbaɗa fulawa akai, sai ki sake ɗora wani dough ɗin, a haka za ki yiwa dukkansu, sannan sai ki sake rolling ɗin su ya yi faɗi.
  3. Ki ɗora wannan fulawar a kan non stick pan na tsawon mintina 2-5 sauke ki yanka shi gida huɗu. Kar a sa wuta sosai (medium heat).
  4. Don yin fillings, ki dafa nama tare da albasa, attarugu, karas, tafarnuwa, maggi, curry da thyme.
  5. Ki ɗauko kowane side na dough ɗaya, ki saka fillings sai ki kwaɓa flour da ruwa don manne bakin samosa ɗin.
  6. Sai ki soya samosa ɗinki a cikin deep frying pan har sai ya soyu.
Domin koyan Yadda ake  Fanke (puff-puff) a cikin sauƙi danna wannan koren rubutun.
labarin da ya wuceYadda Ake  Fanke (puff-puff) A Cikin Sauƙi
Labarin na GabaYadda Ake Miyar Alaiyahu Domin Ƙarin Lafiya