Yadda ake haɗa Dambun Masara

0
31

KAYAN HAƊI 

  • Tsakin masara 
  • Mai 
  • Zogale 
  • Sinadarin ɗanɗano 
  • Albasa 
  • Attaruhu 
  • Gyaɗar miya 

Yadda za a haɗ

A samu madambaci a zuba ruwa a ƙasan, sai a ɗora ruwan a wuta, sai a wanke tsakin masarar sosai a tsane a mararaki , a sa buhu a saman madambacin, a juye tsakin masara a ciki, a bar shi ya turara kamar awa 1. 

A kwashe tsakin a faranti a kawo ruwa a yayyafa masa asa yankakkiyar albasa da attaruhu da sinadarin ɗanɗano da zogale da gyaɗa da mai ɗan daidai misali, a maida shi wuta a dinga yayyafa masa ruwa akai-akai har sai ya turara sosai ya yi laushi sannan a sauke.

Domin karanta cikekken littafin Girke Girke  Danna nan 
labarin da ya wuceYadda ake haɗa Gima Macaroni Jallof
Labarin na GabaMa`anar Siyasa A Musulunci