Yadda ake haɗa Mulukhayya

0
28

KAYAN HAƊI 

  • Nama 
  • Kori 
  • Tafarnuwa 
  • Sinadarin ɗanɗano 
  • Gishiri 
  • Albasa 
  • Ba’adonise 
  • Thyme 
  • Ganyan Ayayo

Yadda za a haɗ

Da farko a tafasa nama da albasa da thyme, idan ya tafasa kuma ya dahu sai a yanka ayayo ƙanana a daka shi a zuba sinadarin ɗandano da gishiri a kan romon da aka tafasa. 

Sai a ɓare tafarnuwa a daka da ba’adonise a soya, a zuba a cikin miyar ayayon ana zubawa sai a rufe a kashe wutar, kar a bar shi ya yi kauri, kar kuma ya yi ruwa. A ci da biredin Larabawa ko shinkafa ko abin da kike so.

Domin karanta cikekken littafin Girke Girke  Danna nan 
labarin da ya wuceYadda ake haɗa Miyar Kayan Ciki
Labarin na GabaYadda ake haɗa Kufta